Yajin Aikin ASUU: Ba za mu biya duk wanda bai yi aiki ba — Gwamnatin Tarayya
Published: 12th, October 2025 GMT
Gwamnatin Tarayya, ta gargaɗi Ƙungiyar Malaman Kami’o’i ta Ƙasa (ASUU), cewa za ta aiwatar da dokar “babu aiki, babu albashi” idan malaman suka ci gaba da yajin aikin da ka iya zai kawo cikas ga harkokin karatu.
A wata sanarwa da ma’aikatar ilimi ta fitar da yammacin ranar Lahadi, Ministan Ilimi, Maruf Tunji Alausa, da Ƙaramar Ministan Ilimi, Suwaiba Sa’id Ahmed, sun ce gwamnati tana da niyyar magance ƙorafe-ƙorafen ASUU ta hanyar tattaunawa cikin lumana.
“Gwamnati ta nuna gaskiya, haƙuri da kyakkyawar niyya a tattaunawarta da ƙungiyar,” in ji sanarwar.
Ministocin sun bayyana cewa yawancin buƙatun ASUU, kamar ƙarin kuɗin koyarwa da inganta yanayin aiki an riga an biya musu.
Sauran matsalolin kuma suna ƙarƙashin kulawar kwamitocin gudanarwar jami’o’i, waɗanda gwamnati ta sake kafawa don su kula da batutuwan da suka rage.
Sai dai duk da waɗannan matakan, ASUU ta zaɓi shiga yajin aiki.
Ministocin sun ce wannan mataki bai nuna haɗin kai ko adalci ga ɗalibai da jama’a ba.
Sun ƙara da cewa: “Gwamnati ta yi tsayin daka wajen tabbatar da zaman lafiya da daidaita karatu a jami’o’i.
“Amma sun yi gargaɗi cewa, dokar “babu aiki, babu albashi” tana nan daram a tsarin dokokin ƙwadago na Najeriya, kuma gwamnati za ta yi amfani da ita idan aka katse harkokin karatu.
Gwamnati ta roƙi ASUU da ta sake tunani tare da dawowa teburin sulhu, inda ta ce ƙofarta a buɗe ta ke don tattaunawa da yin sulhu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: gargadi Gwamnatin tarayya Yajin aiki
এছাড়াও পড়ুন:
An buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarawaba a Katsina
Hukumar kula da makarantun firamare da sakandare ta Jihar Katsina ta sanar da sake buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarabawar zangon farko na shekarar karatu.
A wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Sani Danjuma Suleman, ya fitar a madadin Shugaban hukumar, ta ce makarantun firamare, sakandiren je-ka-ka-dawo da kuma makarantu masu zaman kansu za su buɗe daga yau Talata domin ci gaba da jarabawar zangon farko.
Sanarwar ta ƙara da cewa, sauran makarantun kwana za su ci gaba da kasancewa a rufe har sai lokacin da hali ya ba da dama.
Aminiya ta ruwaito cewa, a bayan nan ne Gwamnatin Katsina ta rufe makarantun bayan ƙaruwar hare-haren sace ɗalibai da masu garkuwa da mutane suka sake farfaɗowa da su a wasu yankuna.
Gwamnatin ta ce ta ɗauki matakin ne da nufin daƙile matsalar tsaro da kuma sa ido a kan al’amura.
A ƙarshe, hukumar ta roƙi haɗin kan iyaye da masu kula da ɗalibai domin su ci gaba da ba wa shirin goyon baya tare da ƙarfafa ɗaliban su dage da karatu wajen rubuta jarabawar da suke yi.