Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya (ASUU) ta mayar da martani kan barazanar gwamnatin tarayya ta “ba aiki, ba a biya”, tana mai cewa ba za ta bari a tsoratar da ita da irin wannan gargaɗi ba. Shugaban ASUU, Chris Piwuna, ya bayyana haka a wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels a shirin Politics Today a ranar Litinin.

Piwuna ya ce ASUU ta tsaya tsayin daka tare da sauran ƙungiyoyin Malamai kamar CONUA, da NAMDA, da SSANU, da NASU, wajen goyon bayan yajin aikin da ke gudana. Ya zargi Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, da ƙoƙarin rarraba malamai ta hanyar yin alƙawarin biyan wasu ma’aikata albashi. “Ya na ƙoƙarin rarraba kan mu, amma kan mu a haɗe yake. Babu wanda zai iya tsoratar da mu,” in ji shi.

Ba Bu Dalilin Da ASUU Za Ta Fara Yajin Aiki, An Biya Duk Buƙatunsu – Ministan Ilimi  ASUU Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Kwanaki 14 Don Biyan Buƙatunta

Shugaban ASUU ya kuma shawarci Ministan Ilimi da ya maida hankali wajen warware rikicin maimakon yin barazana. “Ya kamata ya karkata kan magance wannan matsalar. Idan kuma ya ci gaba da bin wannan hanyar ta barazana, zai gaza,” Piwuna ya ƙara da cewa.

Duk da matsayinta mai tsauri, ASUU ta bayyana cewa tana shirye don tattaunawa da gwamnati. Piwuna ya ce sun samu kiran Ministar Ƙwadago, wadda ta bayyana cewa an umurce ta da shiga tsakani don warware rikicin. “ASUU a shirye take, muna son tattaunawa don kawo ƙarshen wannan ƙwan gaba ƙwan baya,” in ji shi.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Rundunar Ƴansanda Ta Kama Gaggan Ƴan Fashi 9 A Kano October 13, 2025 Manyan Labarai Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 236 A Jihohi 27 Da Birnin Tarayya October 13, 2025 Manyan Labarai Ta’addanci: Ana Fuskantar Ƙarancin Man Fetur A Mali Sakamakon Datse Hanyoyin Shiga Bamako October 13, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Ƙasar Japan ta fara sayar da injin da ke yi wa mutane wanka

An fara sayar da wani inji da ke yi wa mutum wanka bayan ya burge baƙi a lokacin bajekolin duniya a Japan, in ji wata mai magana da yawun kamfanin da ya ƙera injin, a ranar Juma’a.

Masu amfani za su kwanta su rufe kansu a cikin injin da wani murfi, sannan ya wanke su kamar yadda ake wanke kaya a injin wanki, amma ba tare da ya jujjuya su ba, yayin da kiɗa ke tashi a ciki.

An gabatar da samfurin na’urar, mai suna “injin wankin ɗan adam”, kuma an sami dogayen layuka a baje kolin watanni shida da aka kammala a Osaka a watan Oktoba bayan ya sami halartar fiye da mutum miliyan 27.

Kamfanin Japan mai suna Science ne ya ƙera shi, kuma wannan na’urar sabuwa ce a kan irin ta da aka nuna a Osaka, a shekarar 1970.

“Injiniyanmu shugaban kamfani ya samu wahayi daga wannan tun yana ƙaramin yaro mai shekaru 10 a lokacin,” in ji mai magana da yawun Science, Sachiko Maekura, ga AFP.

Na’urar “ba wai tana wanke jiki kaɗai ba, har ma da ruhinka,” in ji ta, tare da lura da bugun zuciya da sauran muhimman alamomin lafiyar masu anfani da shi.

Bayan wani kamfanin shakatawa daga Amurka ya tuntubi Science don ganin ko za a shigar da samfurin fasahar kasuwa, sai kamfanin ya yanke shawarar samar da shi a zahiri.

Wani otal a Osaka ya sayi na’urar ta farko kuma yana shirin fara amfani da ita ga baƙin otal ɗin, in ji mai magana da yawun kamfanin.

Sauran abokan cinikin na’urar sun haɗa da Yamada Denki, babban kamfanin dillancin kayan lantarki a Japan, wanda ke fatan na’urar za ta jawo mutane zuwa shagunan su, in ji ta.

“Saboda wani bangare na jan hankalin wannan na’ura shi ne ƙarancinta, muna shirin samar da kusan guda 50 ne kawai,” in ji Maekura.

Jaridun ƙasar ta Japan sun rawaito cewa farashin siyarwa zai kasance yen miliyan 60, kwatankwacin sama da Naira miliyan 500.

AFP

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ƙasar Japan ta fara sayar da injin da ke yi wa mutane wanka
  • Jagoran : Amurka Tasha Kashi A Yakin Kwanaki 12 Duk Da Manyan Makamai Na Zaman Da Take Da Su.
  • Ya kamata ’yan majalisar Najeriya su koma zaman wucin gadi – Ndume
  • An janye ’yan sanda 11,566 daga yi wa manyan mutane rakiya – Egbetokun
  • Isra’ila Na Barazanar Sake Shiga Wani Sabon Yaki Da Kasar Lebanon
  • An janye ’yan sanda 11,566 daga gadin manyan mutane a faɗin Nijeriya
  • Gwamnati Za Ta Biya Wasu Kudaden Ariyas Ga Masu Fensho Wannan Wata
  • Super Falcons za su ƙaurace wa wasannin Nijeriya saboda riƙe musu alawus
  • Shugaba Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta-baci Kan Harkar Tsaro Tare da Bada Umurnin Daukar Sabbin Jami’ai
  • An ceto ’yan mata 24 d aka yi garkuwa da su a makaranta a Kebbi