Aminiya:
2025-10-14@21:52:49 GMT

’Yan bindiga sun kai hari a Kankia

Published: 14th, October 2025 GMT

Dandazon ’yan bindiga sun kai hari a yankin Kankia da ke Jihar Katsina inda suka halaka mutum daya tare da jikkata wasu da dama.

Shaidu sun ce ’yan bindiga kimanin 100 a kan babura ne suka kai harin a yankin Kwadawa da ke Gundumar Gashi da ke Karamar Hukumar Kankia, inda ake Ana zargin maharan sun kai harin daukar fansa ne,

Maharan da suka kai farmaki a yankin da ke Gabahsin karamar hukumar, sun sace dabbobi da ba a san adadinsu ba, suna masu barazanar halaka duk mutanen yankin.

Wakilinmu ya ruwaito cewa a halin yanzu mazauna yankunan Bogga, Taiba Badole, Arahiya, Kwandawa, Rumawa, Gangara da Rugar Bindo da ke gundumar Gachi da kuma Fakuwa/Kafindangi suna yin kaura domin tsira da rayuwarsu.

Ya kamata ‘yan fim su rika taimaka wa kananan cikinsu-Rukayya Abdullahi Juyin mulki: Shugaba Rajeolina ya tsere daga ya rushe majalisa

Wani ganau ya ce’yan bindigar suna kutsawa zuwa yankunan da a baya suke zauna cikin aminci, kmar Kankia , Charanchi, Kusada da a baya ba sa fama da matsalar tsaro.

Kazalika mazauna kauyukan Tama da Dokaji da ke Karamar Hukumar Bindawa sun bayyana fargabarsu da bayan samun labarin harin na Kankia,  mai makwabtaka da su.

Haladu Badole ya ce, “Kimanin kwanaki uku ke nan da muka lura da wasy bakin fuska a yankunanmu, kuma a daren jiya sun kai hari suka sace dabbobin mutane.”

Mazauna yankin sun yi kira ga hukumomi da su gaggauta tura jami’an tsaro zuwa yankin domin samar da tsaro.

A baya yankin Gabashin Karamar Hukumar Kankia ya kasance cikin amici duk da ’yan hare-haren da aka samu a yankunan Rimaye, Magam, Sukuntuni, Gyaza daKunduru da ke karamar hukumar.

Wakilinmu ya tuntubi kakakin ’yan sandan jihar, amma ya bayyana masa cewa suna gudanar da bincike domin gano hakikanin halin da ake ciki.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Bindiga hari Tsaro

এছাড়াও পড়ুন:

Mutumin da ya sayar da ɗansa kan N1.5m ya shiga hannu a Ebonyi

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ebonyi, ta kama wani mutum mai suna Chukwuma Onwe, ɗan Ƙaramar Hukumar Izzi, bisa zargin sayar da ɗan da aka haifa masa kwanaki biyar kan Naira miliyan 1.5.

An gano cewa Onwe ya sayar wa wata mata mai suna Chinyere Ugochukwu jaririn, wacce ake zargin tana cikin ƙungiyar safarar yara zuwa ƙasashen waje.

ASUU za ta fara yajin aikin mako 2 daga ranar Litinin Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja

Dukkaninsu suna hannun ’yan sanda.

Wata majiyar ’yan sanda ta bayyana cewa matar Onwe, mai suna Philomena Iroko, ce ta fallasa shi bayan ta samu labari daga maƙwabta cewa mijinta ya sayar da jaririn da suka haifa.

Da ta tabbatar da hakan, sai ta garzaya ta kai rahoto ofishin ’yan sanda, inda aka kama Onwe ba tare da ɓata lokaci ba.

Kakakin rundunar jihar Ebonyi, SP Joshua Ukandu, ya tabbatar da cewa an ceto jaririn daga hannun wacce ta saya shi.

Ya ce an kama Onwe da Chinyere Ugochukwu a ranar Juma’a a unguwar Azugwu, Ƙaramar Hukumar Abakaliki, kuma suna tsare a hannun ’yan sanda domin ci gaba da bincike.

Matar Onwe, Philomena, ta ce ta yi mamaki matuƙa cewa mijinta ya sayar da jaririn nasu.

Ta bayyana cewa tun bayan haihuwarta, Onwe, ya ce zai kai jaririn wajen ’yar uwarsa domin ta sa masa albarka, sai dai daga baya aka gano cewa ya sayar da shi.

Ta ce, “Yaronmu bai wuce kwanaki biyar da haihuwa ba, amma mijina ya sayar da shi.

“Ban taɓa tunanin zai yi haka ba. Ina roƙon jama’a da masu hannu da shuni su taimaka min a wannan hali da na tsinci kaina.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gidauniyar Sheikh Dahiru Bauchi Ta Tura Ɗalibai 117 Karatu Ƙasar Algeria 
  • An kama mata da miji suna safarar makamai a Kaduna
  • Majalisar Wakilai Ta Buƙaci Hukumomin Tsaro Su Kai Agajin Gaggawa A Sakkwato
  • Rasha ta kai wa tawagar kayan agajin MDD hari a Ukraine
  • Hukumar Kwastam Ta Tara Naira Biliyan ₦658.6 A Watan Satumba — DG Na NOA
  • Zaben Kamaru: Issa Tchiroma Bakary ya lashe yankunan da Biya ke da rinjaye
  • Hukumar Hisbah Ta Kama Wasu Matasa Da Suka Yi Aure Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Kano
  • Ƴan Bindiga Sun Amince Da Dakatar Da Hare-Hare A Ƙananan Hukumomi 5 A Katsina
  • Mutumin da ya sayar da ɗansa kan N1.5m ya shiga hannu a Ebonyi