‘Yan Kamaru na kada kuri’a a zaben shugaban kasar
Published: 12th, October 2025 GMT
Yau Lahadi al’ummar Kamaru na kada kuri’a a zaben shugaban kasar.
Masu kada kuri’a miliyan takwas ne aka tantance domin kada kuri’a a zaben zagaye na farko da Shugaban kasar mai ci Paul Biya mai shekara 92 dake neman wa’adi na takwas.
A cikin makonni biyu na yakin neman zaben, Shugaba Biya wanda aka dade ba a gan shi a bayyanar jama’a ba ya gudanar da gangami guda daya kacal, a garin Maroua dake yankin Arewa mai Nisa, daya daga cikin yankuna uku na arewa, inda ya sha alwashin magance matsalar tsaro da rashin aikin yi.
A hukumance dai ‘yan takara goma sha biyu ne ke fafatawa a wannan zaben, amma biyu sun janye.
Manyan masu kalubalantar Paul Biya guda biyu a wannan zaben su ne, Issa Tchiroma Bakary, na jam’iyyar CNSF, da Bello Bouba Maïgari, wanda zai iya dogaro da jam’iyyarsa ta (UNDP).
Batun tattalin arziki da rashin aikin yi da matsalar tsaro su ne suka fi mamaye yakin neman zaben.
Mista Biya na Jam’iyyar (RDPC), ya fara mulkin kasar ne tun shekarar 1982.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Wata Kotu a Faransa ta yi watsi da rufe wata makarantar musulmi a birnin Nice October 12, 2025 Gwamnatin Cuba ta yi watsi da zargin da Amurka ke yi na hannu a yakin Ukraine October 12, 2025 Arachi: HKI Ba Abar Amincewa Ba Ce, Falasdinawa Su Yi Hattara October 12, 2025 Iran Ta Yi Allawadai Da HKI Kan Hare-Haren Da Take Kaiwa Kudancin Lebanon October 12, 2025 An Gudanar Da Taron ‘Farkawar Musulmi’ A Nan Tahren Inda Aka Tattauna Batun Falasdinu October 12, 2025 Amurka Da Masar Ne Zasu Jagoranci Taron Rattaba Hannu Tsakanin HKI Da Falasdin A Sharm Sheikh October 12, 2025 China Ta Sha Alwashin Maida Martani Kan Harajin Trump A Kanta Na 100% October 12, 2025 An Yi Girgizar Kasa Mai Daraja 5 A Ma’aunin Richter A Kasar Habasha October 12, 2025 Shugaban Kasar Najeriya Ya Yi Afuwa Ga Wasu Mutanen Da Kotuna Su Ka Hukunta October 12, 2025 An Yi Musayar Wuta A Tsakanin Masu Tsaron Iyakokin Kasashen Afghanistan Da Pakistan October 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Uganda: An Kama Fiye Da ‘Yan Hamayyar Siyasa 300 A Lokacin Yakin Neman Zabe
Majiyar ‘yan hamayyar siyasar kasar Uganda sun sanar da cewa, jami’an tsaron kasar sun kama magoya bayan Bobi Wine dake takarar shugabancin kasar 300 a tsawon yakin neman zabe.
Mai magana da yawun Bobi Wine dan takarar shugabancin kasar ya fada a jiya Talata cewa; jami’an tsaron kasar sun kama fiye da mutane 300 da suke goyon bayansa tun da aka fara yakin neman zabe daga watan Janairu zuwa yanzu.
Bob Wine wanda shahararren mawaki ne ya juye zuwa dan siyasa, yana yin takara a karo na biyu da shugaban kasar mai ci, Uweri Musaveni. A zaben 2021 Bob Wine wanda sunansa na yanke shi ne Robert Kyagulanyi,, ya zo na biyu.
Kakakin jam’iyyarsa ta NUP,ya ce, a cikin wannan makon ma an kama mutane da dama, kuma ana tsare da su ne a cikin babban birnin kasar Kamfala.
Majiyar jam’iyyar hamayyar ta kuma ce, a ranar Litinin da aka bude yakin neman zabe kadai na kame mutane sun kai 100, sai kuma wani adadi mai yawa a jiya Talata.
Jami’an tsaron kasar sun sanar da kame mutane 7 bayan da su ka yi jefe-jefe da duwatsu a lokacin yakin neman zabe.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Reuters: Kungiyar Likitoci Ba Da Iyaka Ba Ta Fice Daga Asibitin Darfur Bayan Bude Wa Ma’aikatanta Wuta November 26, 2025 Shugaban Iran: Kasuwar jarin cikin gida sirrin nasarorin gwamnati na tattalin arziki November 26, 2025 Larijani: Hadin gwiwar Iran da Pakistan na taimaka wa zaman lafiya a yankin November 26, 2025 Al-Houthi ya yi ta’aziyyar shahadar babban kwamanda na Hizbullah November 26, 2025 UNIFIL: Isra’ila tana sabawa wa kudurorin MDD a cikin Lebanon November 26, 2025 Matsalolin Tsaro A Yankunan Bakin Ruwa A Kasar Siriya Ya Kai Ga Zanga-Zangar Lumana November 26, 2025 Aljeriya Ta Bukaci Kasashen Duniya Su Dauki Mataki Don Kawo Karshen Ta’asan HKI A Yankin Asiya Ta Kudu November 26, 2025 Shugaban Majalisar Koli Ta Taron Kasa Iran Ya Yabawa Pakistan Saboda Goyon Bayanta November 26, 2025 EU da AU na taro kan diyya ga laifukan mulkin mallaka da cinikin bayi November 25, 2025 Hizbullah: Isra’ila na kure idan ta na tunanin kashe-kashe zai kawo karshen kungiyarmu November 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci