Trump Ya Fadawa Hamas Su Mika Makamansu Ko Kuma A Kwace Su Da Karfi
Published: 15th, October 2025 GMT
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya fadawa kungiyar Hamas su mika makamansu da radin kansu ko kuma zai kwance damararsu da karfi.
Jaridar Daily Mails ta kasar Burtaniya ta nakalto shugaban yana fadarwa kafafen yada labarai a washinton a jiya Talata.
Amma kungiyar Jihadul Islami daya daga cikin kungiyoyin da ke dauke da makamai a zirin gaza ta bakin mataimakin babban sakataren kungiyar Mohammad Al-Hindi a hirar da yayi da tashar talabijan ta Aljazeerah cewa kungiyoyi masu gwagwarmaya a gaza basu amince su mika makamansu a yarjeniyar sulhu na Trump ba kuma basu damu da barazanar shugaba Trump na kwance damarasu da karfi ba.
Alhindi ya kara da cewa banda haka babu wata kalma ko guda a cikin yarjeniyar da muka cimma da Trump dangane da kwance damarar masu gwagwarmaya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta Samarda Sabban Hanyoyi Na Fuskantar Barazanar Makiya October 15, 2025 Hamas Ta Ce HKI Tana Jinkirta Neman Gawakin Yahudawa A Gaza October 15, 2025 Yansandan Italiya Sun Kara Da Masu Goyon Bayan Falasdinawa A Garin Udine October 15, 2025 Iran Ta Yi Allah Wadai Da Kalaman Kin Jinin Iran Da Trump Ya Yi A Majalisar Dokokin Isra’ila October 15, 2025 A Lokacin Yaki, Iran Ta Tarwatsa Wata Cibiyar Leken Asirin Yahudawan Sahayoniyya Da Ke Yankin Farar Hula October 15, 2025 Shugaban Kasar Columbia Ya Yi Dirar Mikiya Kan Donald Trump Kan Bai Wa Isra’ila Makamai October 15, 2025 Kungiyar Jihadul-Islami Ta Falasdinu Ta Ce; ‘Yantar Da Fursunonin Falasdinawa Abu Ne Mai Muhaimmanci October 15, 2025 Majalisar Dinkin Duniya Ta Bayyana Cewa: Sake Gina Gaza Zai Ci Dala Biliyan 70 October 15, 2025 Araghchi : Trump bai cancanci mai samar da zaman lafiya ba October 14, 2025 UNDP : An ruguza fiye da kashi 80 cikin 100 na gine-ginen Gaza October 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Trump, da Al’Sisi za su jagoranci taron zaman lafiya kan Gaza a Masar ranar Litinin
Masar za ta shirya wani taron kasa da kasa kan zaman lafiya a birnin Sharm el-Sheikh da ke bakin Tekun Maliya a ranar Litinin, wanda Shugaba Abdel Fattah el-Sisi da takwaransa na Amurka, Donald Trump, za su jagoranta.
Wata sanarwa daga fadar shugaban kasar ta bayyana cewa taron zai tattaro shugabanni daga kasashe fiye da 20.
Manufar taron ita ce “kawo karshen yakin Gaza, da karfafa zaman lafiya da kwanciyar hankali a Gabas ta Tsakiya, da kuma fara wani sabon mataki na tsaro da kwanciyar hankali a yankin,” in ji sanarwar.
A ranar Laraba Trump ya sanar da cewa Isra’ila da Hamas sun amince da mataki na farko na wani shiri mai matakai 20 da ya gabatar a ranar 29 ga Satumba don cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da sakin dukkan fursunonin Isra’ila da ke hannun Hamas a musayar fursunoni Falasdinawa kusan 2,000, da kuma janye sojojin Isra’ila daga dukkan yankin Gaza.
Mataki na biyu na shirin ya tanadi kafa sabon tsarin mulki a Gaza, samar da wata rundunar tsaro da za ta kunshi Falasdinawa da sojoji daga kasashen Larabawa da Musulmi, da kuma kwace makamai daga hannun Hamas.
Tun daga watan Oktoba na 2023, hare-haren Isra’ila sun kashe Falasdinawa fiye da 67,600 a Gaza, yawancinsu mata da yara, tare da mayar da yankin kufai.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka ‘Yan Kamaru na kada kuri’a a zaben shugaban kasar October 12, 2025 Wata Kotu a Faransa ta yi watsi da rufe wata makarantar musulmi a birnin Nice October 12, 2025 Gwamnatin Cuba ta yi watsi da zargin da Amurka ke yi na hannu a yakin Ukraine October 12, 2025 Arachi: HKI Ba Abar Amincewa Ba Ce, Falasdinawa Su Yi Hattara October 12, 2025 Iran Ta Yi Allawadai Da HKI Kan Hare-Haren Da Take Kaiwa Kudancin Lebanon October 12, 2025 An Gudanar Da Taron ‘Farkawar Musulmi’ A Nan Tahren Inda Aka Tattauna Batun Falasdinu October 12, 2025 Amurka Da Masar Ne Zasu Jagoranci Taron Rattaba Hannu Tsakanin HKI Da Falasdin A Sharm Sheikh October 12, 2025 China Ta Sha Alwashin Maida Martani Kan Harajin Trump A Kanta Na 100% October 12, 2025 An Yi Girgizar Kasa Mai Daraja 5 A Ma’aunin Richter A Kasar Habasha October 12, 2025 Shugaban Kasar Najeriya Ya Yi Afuwa Ga Wasu Mutanen Da Kotuna Su Ka Hukunta October 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci