Araqchi: Tattaunawar Nukiliya Wani Zabi Ne Mai Muhaimmanci Wanda Ya Karfafa Matsayin Iran A Duniya
Published: 28th, July 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Tattaunawar makamashin nukiliya wani zaɓi ne mai mahimmanci wanda ya ƙarfafa matsayin Iran a duniya
Ministan harkokin wajen kasar Iran Seyyed Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa; Kasarsa ta shiga shawarwarin makamashin nukiliya ba na kai tsaye ba da Amurka bisa wata cikakkiyar shawarar kasa.
Hakan dai ya zo ne a yayin wata ganawa da aka yi da Araghchi, inda ya yi nazari kan batutuwan da suka shafi makamashin nukiliyar Iran da ma matakan da aka dauka na yin shawarwari da kasashen yammacin duniya. Ya yi bayanin cewa, manufar yarjejeniyar makamashin nukiliyar ta ginu ce bisa ka’ida mai ma’ana, ta yadda Iran za ta dauki matakai na karfafa kwarin gwiwa domin dage takunkumin kanta.
Jami’in na Iran ya yi nuni da cewa, a lokacin da gwamnatin Trump ta Amurka ta bayyana burinta na yin shawarwari kan batun makamashin nukiliyar, Iran ta bayyana shirinta na shiga tattaunawa bisa wannan manufa, tare da jaddada cewa, ba za ta amince da duk wani sharadi da zai kawo cikas ga shirinta na nukiliya ko kuma dakatar da ayyukan inganta sinadarin Uranium ba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Da EU Suna Kokarin Samun Moriyar Juna A Shekaru 50 Masu Zuwa
Duk da cewa yanayin duniya ya yi babban sauyi, kamata ya yi a mayar da hankali ga hadin gwiwa, yayin da ake raya dangantaka tsakanin Sin da EU, kana bangarorin biyu su bi hanya mafi dacewa, da samun kyakkyawar makoma a shekaru 50 masu zuwa, da kuma kara samar da gudummawa ga dukkanin sassan duniya. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp