Bakai’i: Iran Tana Son Ganin An Yi Taron Gaggawa Na Kungiyar Kasashen Musulmi
Published: 28th, July 2025 GMT
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa;Yunwar da mutanen Gaza suke fama da ita na tsawon watanni biyar, laifi ne maras tamka da HKI take tafkawa, da ya zama wajibi kungiyar kasashen musulmi ta yi taron gaggawa akansa.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran Dr. Isma’ila Baka’i wanda ya gabatar da taron manema labaru a yau Litinin ya kuma yi Magana akan tattaunawar da Iran ta yi da kasashen turai akan shirinta na makamin Nukiliya, ya ce: Tattaunawar da aka yi ta da kasashen turai manufarta ita ce dauke wa Iran takunkuman da aka kakaba mata akan shirinta na Nukiliya.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya kuma ce; Kasashen na turai ba su da hakkin su kakabawa Iran takunkumi, idan kuwa har su ka ci gaba to za su fuskanci mayar da martanin Iran.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Uba Sani Ya Bayyana Tsare-tsaren Ci Gaban Kaduna a Taron Duniya a Dubai.
Daga Abdullahi Shettima
Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya wakilci Nijeriya a taron ƙoli na biranen Asiya da ya gudana a ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), inda ya gabatar da kudirorin sauyin ci gaban Kaduna.
Taron ya samu halartar manyan baki daga ƙasashe sama da 150, ciki har da gwamnoni, shugabannin birane da jagororin kasuwanci daga Asiya, Fasifik, Turai da Afirka. Taken taron shi ne “Haɗin Gwiwa. Ƙarfafawa. Sauyi.”
A jawabinsa mai taken “Gina Haɗin Gwiwa Domin Ci Gaban Kowa,” Gwamna Uba Sani ya bayyana yadda Kaduna ke samun nasara a fannoni da dama kamar gyaran birane, bunƙasa noma da tallafawa jama’a. Ya ce tsarin ci gaban jihar yana dogara ne kan faɗaɗa damar tattalin arziki, kare marasa ƙarfi, da ƙarfafa jama’a su cim ma nasara a rayuwarsu.
Haka kuma, ya halarci baje kolin birnin Dubai mai taken “Sauya Arewa a Nijeriya: Jagoranci, Ƙirƙira da Tasirin Zamantakewa,” inda ya jaddada muhimmancin jagoranci mai nagarta da amfani da fasaha wajen buɗe damarmaki ga al’umma.
A yayin taron, Gwamnan ya gudanar da ganawa ta musamman da Marwan Bin Galita, Darakta-Janar na birnin Dubai, inda suka tattauna batutuwan kirkirar makamashin sharar gida, kula da sharar zamani, da tsare-tsaren gine-ginen birane na zamani.
Duk ɓangarorin biyu sun amince da zurfafa haɗin kai a fannin fasaha da musayar ƙwarewa domin tallafawa sauyin tattalin arzikin Kaduna zuwa mai ɗorewa.
Gwamna Sani ya bayyana cewa halartar Kaduna a taron (APCS 2025) na nuna shirin jihar na shiga sahun gaba wajen yin haɗin kai, ƙirƙira da zama abin koyi a fannin ci gaba mai ɗorewa — a Najeriya da duniya baki ɗaya.
Karshe.