Harin Ta’addanci A Wani Coci Ya Lashe Rayukan Mutane Fiye Da 21 A Gabashin Kongo
Published: 28th, July 2025 GMT
Fiye da mutane 21 ne suka mutu a wani harin ta’addanci da aka kai kan wani coci a gabashin Kongo
Rahotonni sun tabbatar da cewa; Sama da mutane 21 ne aka kashe a wani hari da mayakan ‘yan tawayen kungiyar Allied Democratic Forces (ADF) suka kai kan wani cocin Katolika da ke gabashin Kongo, wanda ya hada da kona gidaje da shaguna a yankin.
A ranar Lahadin da ta gabata ne mayakan da suke da alaka da kungiyar Allied Democratic Forces (ADF) da ke samun goyon bayan kungiyar ‘yan ta’adda ta ISIS suka kaddamar da harin ta’addanci kan wata majami’ar Katolika a gabashin Kongo.
“Sama da mutane 21 ne aka kashe a ciki da wajen cocin,” Dieudonné Duranthabo, wani jami’in kungiyoyin farar hula a Komanda, ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na Associated Press cewa: “Sun gano akalla gawarwakin mutane uku da suka kone, sannan an kona gidaje da dama.”
Harin ya faru ne da misalin karfe 1:00 na safiyar Lahadi a cikin wani cocin Katolika da ke yankin Komanda a gabashin Kongo. An kuma kona gidaje da shaguna da dama.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Gano Wani Dutse Mai Sassaka Na Daular Qin A Kan Tsaunin Qinghai-Tibet
Hukumar kula da al’adun gargajiya ta kasar Sin ta sanar a yau cewa, an gano wani dutsen da aka yi sassaka kan sa a kan tsaunin Qinghai-Tibet, wanda ya kasance irinsa daya tilo na daular Qin da har yanzu ke mazauninsa na asalin, kuma a wuri mafi tsawo.
Dutsen wanda ke arewacin bakin tabkin Gyaring na gundumar Maduo, dake arewa maso yammacin lardin Qinghai, na wuri mai tsawon mita 4,300.
Gano dutsen na tattare da wata muhimmiyar daraja ga tarihi da fasaha da kimiyya. Sarki Qinshihuang na daular Qin ne ya fara hada kan kasar Sin. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp