Ana Ci Gaba Da Habaka Karfin Kudin Kasar Sin Tun Daga Shekarar 2021
Published: 28th, July 2025 GMT
Da safiyar yau Litinin ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar da taron manema labarai, bisa taken “Cimma burikan da aka tsara domin neman bunkasa tattalin arziki da zaman takewar al’umma a tsakanin shekarar 2021 zuwa shekarar 2025”.
A yayin taron, jami’in babbar hukumar buga haraji ta kasar Sin ya bayyana cewa, tun daga shekarar 2021 ya zuwa yanzu, tattalin arzikin kasar Sin ya bunkasa bisa shirin da aka tsara, kana, bisa hasashen da aka yi.
A sa’i daya kuma, jami’in ya ce, tun daga shekarar 2021, ya zuwa yanzu, jerin manufofin da aka samar a fannin rage haraji, da kudaden da hukumomin buga haraji suka karba, ya nuna goyon baya ga aikin raya tattalin arziki da kyautata zaman takewar al’umma. Hasashen da aka yi ya kuma nuna cewa, tsakanin shekarar 2021 da ta 2025, yawan haraji da kudaden da hukumomin buga haraji suka rage, ya kai kudin Sin Yuan tiriliyan 10.5, kana, yawan harajin da aka mayar kan kayayyakin fitarwa ya kai Yuan tiriliyan 9. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Yuan tiriliyan shekarar 2021 buga haraji
এছাড়াও পড়ুন:
Shawarwarin Sin: Ingantattun Hanyoyi Masu Sauki Na Warware Sabani
A bayan bayan nan, an aiwatar da jerin tattaunawa tsakanin Sin da Amurka karkashin jagorancin shugabanninsu, inda aka samu kyawawan sakamakon da ya kyautata alakarsu ta tattalin arziki da cinikayya. Wannan ya nuna shawarar da a kullum Sin ke bayarwa cewa, tattaunawa ita ce mafita ga dukkan rikice-rikice, maimakon amfani da karfi.
Kasar Sin ta sha nanata cewa, babu mai samun nasara a yakin cinikayya ko haraji. Mun ga yadda aka samu hauhawar farashin kayayyaki da karuwar rashin aikin yi da faduwar darajar hannayen jari a Amurka, a lokacin da ta kaddamar da yakin haraji, wanda ya nuna cewa, maimakon cimma abun da take fata na samun fifiko, asara aka samu da lalacewar muradun kamfanoni da ’yan kasuwar kasar.
Kowace kasa tana da cikakken iko da ’yancin zabar manufofi da matakan da ya dace da ita. Da Sin ta tsaya kai da fata cewa ba za ta ba da kai a yakin haraji da Amurka ta tayar ba, hakan ya sa Amurka yin karatun ta nutsu, kuma ta tuntubi bangaren Sin domin tattaunawa.
Wadannan misalai sun nuna mana cewa, akwai hanyoyi masu sauki da inganci na samun maslaha, kuma shawarwarin da Sin take gabatarwa, su ne suka dace da yanayin duniya a yanzu. Ba dole sai kowa ya samu abun da yake so ba, amma hawa teburin sulhu da tuntubar juna tana taka muhimmiyar rawa wajen warware sabani, da lalubo inda kowane bangare zai iya saki, domin a samu mafitar da za ta karbu ga kowa. Kuma irin wannan din, shi ne burin sabuwar Shawarar Tsarin Shugabancin Duniya da shugaban kasar Sin ya gabatar a baya bayan nan. Duniya ba ta bukatar mayar da hannu agogo baya ta hanyar tayar da rikice-rikice da danniya da nuna fin karfi, zamani ya sauya kuma dole salon tafiyar da harkoki ya sauya, domin dacewa da yanayin da ake ciki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp