Jami’an Hukumar Tsaron Farin Kaya DSS da takwarorinsu na rundunar sojin ƙasa sun kashe aƙalla ’yan ta’adda 45 da ke addabar wasu sassan Jihar Neja.
Bayanai sun ce an kashe ’yan ta’addan ne a ƙauyen Iburu da ke Ƙaramar Hukumar Shiroro a ranar Juma’ar da ta gabata bayan jami’an DSS sun tattaro bayanan sirri kan harƙallar miyagun a yankin.
Majiyoyin tsaro sun ce DSS ta samu bayanan sirri kan wani hari da ’yan ta’addan ke shirin kaiwa ƙauyen Iburu a kan babura, lamarin da sojojin da ke shirin ko-ta-kwana suka tari hanzarinsa.
Ɗaya daga cikin majiyoyin ya shaida cewa an yi musayar wuta tsakanin ɓangarorin biyu, inda aka harbe ’yan ta’adda 45 yayin da jami’an tsaro biyu suka kwanta dama sai kuma huɗu da suka jikkata.
“Mazauna ƙauyukan da lamarin ya shafa sun ce sun ƙidaya aƙalla gawawwakin ’yan ta’adda 40 da kuma gomman babura da aka lalata a yayin musayar wutar.”
Aminiya ta ruwaito cewa wannan tumke ɗamara da ƙara ƙaimi da jami’an tsaron suka yi na zuwa ne a daidai lokacin da Hukumar Kwastam ke bayyana damuwar cewa jami’anta na faɗawa tarkon ’yan ta’adda a yankin.
Ana iya tuna cewa, a watan Afrilun da ya gabata ne Kwanturola Janar na Kwastam, Bashir Adeniyi, ya yi ƙorafin cewa ’yan ta’adda na sheƙe ayarsu a Iyakar Babanna da ke Jihar Neja a ɓangaren da ta yi makwabtaka da Jamhuriyyar Benin.
A wancan lokacin, Adeniyi ya ce jami’ansa sun tsallake rijiya da baya bayan wani kwanton ɓauna da ’yan ta’addan suka yi musu a matsayin ramuwar gayya a sakamakon kame wasu jarkokin man fetur 500 da ake shirin kai musu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan ta adda Jihar Neja yan ta adda
এছাড়াও পড়ুন:
HOTUNA: Yadda Aisha ta koma gidan Buhari na Kaduna
Aisha ta koma gidan mijinta, marigayi Muhammadu Buhari da ke Jihar Kaduna, bayan shafe kwanaki a Daura tana karɓar gaisuwa.
Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe, ce ta jagoranci tawagar gwamnatin jihar wajen tarbar Aisha a Filin Jirgin Sama na Kaduna a ranar Lahadi.
Tsohon shugaban jami’ar Kashere ya rasu a Abuja Gwamnatin APC ta jefa ’yan Najeriya cikin ƙangin talauci — Shugabar LPDaga cikin waɗanda suka tarbe ta akwai Shugabar Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Munira Suleiman Tanimu, da wasu manyan jami’an gwamnati.
Tarbar da aka yi mata ta nuna yadda jihar ke ci gaba da girmama tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da iyalinsa bisa gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban ƙasar nan.
Bayan tarbar ta, Dakta Hadiza ta raka Aisha Buhari da iyalanta zuwa gidan marigayin.
Wannan ya nunacewar iyalan marigayin za su ci gaba da rayuwa a jihar, tare da ƙarfafa zumunci tsakanin gwamnatin jihar.
Dubban mutane na ci gaba da miƙa ta’aziyyarsu kan rasuwar tsohon shugaban wanda ya mulki Najeriya sau biyu.
Ga hotunan a ƙasa: