Dakarun Yemen Zasu Kara Daukan Matakai Kan Jiragen Ruwan Da Ke Hulda Da Isra’ila
Published: 28th, July 2025 GMT
Dakarun kasar Yemen sun sanar da sabbin zabukan kara rurutan bude wuta kan makiya a matsayin martani ga abubuwan da suka faru a Gaza
Dakarun sojin kasar Yemen sun bayyana a cikin wata sanarwa da suka fitar a yammacin jiya Lahadi cewa: Suna tunanin zafafa yakin da suke yi da ‘yan mamaya dangane da abin da ke faruwa a Zirin Gaza na kisan kare dangi da kakaba masifar yunwa kan al’ummar yankin.
Rundunar sojin kasar ta Yemen ta tabbatar da fara aikin killace teku kashi na hudu a kan makiya, inda zasu kai hari kan dukkanin jiragen ruwan kamfanonin da ke aiki a tashar jiragen ruwa na Isra’ila, ba tare da la’akari da kasarsu ba, da kuma duk inda sojojin suka isa.
Sanarwar da Rundunar Sojin ta fitar ta ce, bisa la’akari da ci gaban da ake samu a Falastinu da aka mamaye, musamman a zirin Gaza, ci gaba da yakin kisan kiyashi, da kuma shahadar dubun dubatar al’ummar Falastinu sakamakon wuce gona da iri da aka shafe tsawon watanni ana yi, da ke lashe rayukan al’ummar Falasdinu cikin abin kunya na Larabawa, Musulmi da kuma duniya kan irin wannan mummunan shiru, lallai kasar Yemen, zata kalubalanci irin wadannan munanan hare-hare da ake kai wa na kisan kiyashi, wanda ba a taba ganin irinsa ba a tarihin wannan zamani, kasar Yemen ta samu kanta a matsayin wajibin fuskantar wani nauyi na addini da ɗabi’a, da kuma jin kai ga waɗanda ake zalunta a kullum rana.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Yemen
এছাড়াও পড়ুন:
HKI Na Ci Gaba Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza Inda Take Kashe Falasdinawa
Rahotanni sun bayyana cewa Isra’ila ta kashe wasu falasdinawa guda 5 yankin gaza a ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da suka cimma tsakaninta da kungiyar Hamas a farkon watan oktoba,
A yau juma’a kafar yada labarai ta falasdinu ta bayyana cewa sojojin Isra’ila sun harbe wani bafalasdine a yankin jabaliya dake arewacin yankin Gaza, haka zalika wani bafalasdine mai suna Mahmud suleman al- wadiya sojojin isaraila sun kashe shi a gabashin shuja’iyya dake makwabtaka da gabashin gaza, gari mafi girma a gaza kuma an jikkata wani dan uwansa,
Har ila yau hamdi al-barim da mohamma salem qadi sun ji mummunan rauni sakamakon harin da sojojin Isra’ila suka kai musu a khan yunus dake yammacin gaza a yan kwanakin nan,
Tun daga lokacin da Isra’ila ta kaddamar da hare-hare a yankin Gaza zuwa yanzu a shekara ta 2023 sojojin Isra’ila na ci gaba da kai hare – hare a yankuna daban – daban inda akalla sun kashe mutane 1062 tare da jikkata wasu dubbai fiye da 20,000 kuma da suka hada da yara kana 1600 an cafkesu ana tsare da su .
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka An Tube Yarima Mai Jiran Gado Na Birtaniya Bayan Da Aka Tabbatar Da Laifinsa October 31, 2025 Kasashen Pakistan Da Afghanistan Sun Tsawaita Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta October 31, 2025 M D Duniya Tayi Gargadi Game Da Gwajin Nukiliya Da Amurka Ta Sanar Za ta yi October 31, 2025 Sudan Ta Yi Kira Ga Kwamitin Tsaro Da Ya Ayyana RSF A Matsayin Kungiyar ‘Yan Ta’adda October 31, 2025 Araqchi: Gwajin Makaman Nukiliya Na Amurka Babbar Barazana Ce Ga Duniya October 31, 2025 Masar da Eritrea Sun Tattauna Bukatar Tallafawa Kasar Sudan October 31, 2025 Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Kutsen Na Isra’ila A Kudancin Kasar October 31, 2025 Madagascar Ta Sanar da Kafa Sabuwar Gwamnati Tare da Manyan ‘Yan Adawa October 31, 2025 Iran ta yi fatali da kalamman IAEA Kan Shirin Nukiliyarta October 30, 2025 Trump Ya Umarci Ma’aikatar Yakin Amurka Ta koma gwajin makaman nukiliya October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci