Hukumar Tsarin Fansho na Hadin Gwiwa tsakanin Jiha da Kananan Hukumomi a Jihar Jigawa ta bayyana cewa ta raba sama da Naira Biliyan 1 da dubu 500 ga tsofaffin ma’aikata 569.

Yayin da yake jawabi ga wadanda suka ci gajiyar shirin a gaban Gidan Fansho kafin fara rabon kudin, Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, Alhaji Muhammad K.

Dagaceri, ya bayyana tsarin fansho na jihar a matsayin daya daga cikin mafi nagarta a kasar nan.

A cewarsa, fiye da jihohi ashirin sun kai ziyara jihar Jigawa domin koyon yadda take tafiyar da shirin fansho.

Ya jinjina wa Gwamna Umar Namadi saboda dagewarsa da kuma jajircewarsa wajen dorewa da inganta tsarin fansho a jihar.

Alhaji Dagaceri ya yabawa Gwamna Namadi kan goyon bayansa da matakan da ya dauka tun bayan hawansa mulki domin inganta tsarin, yana mai jaddada irin tasirin alherin da shirin ke yi ga tsofaffin ma’aikata da daukacin ma’aikatan gwamnati.

Ya bukaci tsofaffin ma’aikata da wadanda ke aiki yanzu da su ci gaba da yi wa gwamnati addu’a, tare da nuna godiya ga Gwamna Namadi bisa irin ayyukan alherinsa.

A nasa jawabin, Shugaban hukumar ta Fansho, Dr. Binyaminu Shitu Aminu, ya bayyana cewa fiye da naira biliyan 1 da rabi ne za a raba tsakanin tsofaffin ma’aikata 569.

“Wannan adadi ya kunshi nau’o’in biyan kudi daban-daban, ciki har da hakkokin ritaya, hakkokin mutuwa da sauran ragowar hakkokin fansho na mamatan ma’aikata,” In ji Dr. Aminu.

Dr. Aminu ya kara da cewa, cikin wadanda za su amfana, 287 sun fito ne daga ma’aikatan jiha, 158 daga kananan hukumomi, yayin da 124 suka fito daga Hukumar Ilimin Kananan Hukumomi (LEA).

Ya kara da cewa, za a biya sama da Naira Miliyan 875 ga ma’aikatan da suka yi aiki a karkashin gwamnatin jiha, sannan sama da Naira Miliyan 355 kuma ga wadanda suka fito daga kananan hukumomi, da kuma sama da naira miliyan 274 ga wadanda suka fito daga LEA.

Shugaban hukumar ya tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da biyan hakkokin fansho a kan kari, ciki har da biyan fansho na wata wata a cikin mako na farko na kowane wata.

 

Ya jaddada kudurin gwamnatin jihar na inganta walwalar ma’aikata, domin samun rayuwa mai kyau da kwanciyar hankali bayan kammala aikin.

Usman Muhammad Zaria

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: sama da Naira

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Neja Ta Musanta Rahoton Hana Da’awa A Jihar

Rahoton rashin fahimtar da aka fara yadawar, ya biyo bayan taron kwamitin zaman lafiya da kwantar da tarzoma na jihar, wanda Darakta Janar ya jagoranta a ranar 4 ga watan Satumba.

 

Rashin fahimtar sahihin sakamakon taron ya sa wasu suka rahoto cewa, kwamitin ya dakatar da Malamai daga yin wa’azi.

 

Sanarwar ta kara da cewa, “Hukumar ba ta da hurumin haramtawa Malaman Addinin Musulunci yin wa’azi sai dai in ya bayyana a fili an taka ƙa’idojin hukumar da ta shimfiɗa”.

 

A cewar Hukumar, an kira taron ne domin gabatar da fom din rijistar yin wa’azi ko Da’awah da kuma bin tsarin tantancewa.

 

Ta bayyana shirin a matsayin wani yunkuri na wayar da kan jama’a don “hana rashin fahimtar juna da kuma daƙile yaɗuwar wa’azin yaudara” a faɗin jihar Neja.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Manyan Ma’aikatan FIRS 4 Sun Rasu Sakamakon Gobarar Da Ta Tashi A Ginin Afriland A Legas 
  • Tinubu Ya Janye Dokar Ta-baci A Jihar Rivers
  • Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
  • Jihar Jigawa Ta Amince Da Karin Kasafin Kuɗi Na Naira Biliyan 75 Na Shekarar 2025
  • ALGON ta karrama Gwamna Buni da lambar yabo kan kawo ci gaba a Yobe
  • Najeriya Na Asarar Dala Biliyan 10 Bayan Girbi Duk Shekara- Gwamnatin Tarayya
  • Kungiyar Kare Hakkokin Bil’Adama Ta Siriya Ta Bankado Karin Fararen Hula Da Aka Kashe A Rikicin Suweida
  • Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar 
  • NDLEA ta kama ɗan Indiya da ƙwaya ta Naira biliyan 3 a Legas
  • Gwamnatin Neja Ta Musanta Rahoton Hana Da’awa A Jihar