HausaTv:
2025-07-28@19:53:32 GMT

Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan Almutaba (a) 120

Published: 28th, July 2025 GMT

120-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da haka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin da suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtadha Muttahhari, ko kuma cikin littafin mathnawa na maulana Jalaluddeen Rum ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.

////… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata a kuma cikin sarir Imam Al-Hassan Almujtaba (a) diyar Fatima (s) kuma jikan manzon All..(s) na farko , mon tsaya inda muka bayyana yadda Talha da Zubair suka bukaci Amirulmuminina (a) ya yi masu izini su je umra amma sai ya dubesu da idon shakka, sai yace masu ba umra kukeson zuwa ba. Kuna son yaudara ne. kuna son kwance bai’ar da kuka yi mani. Sai suka sake rantsewa kan cewa umra suke son zuwa. Sai ya sake karbar bai;a daga wajensu. Don ya tabbatar masu shifan da manzon All..(s) ya fada masa, dangane da su. Inda yake fadawa Imam Aliyu dan abitalib (a) kan cewa: Zaka yaki, a bayana,  masu kwace alkawali, da azzalumai da kuma wadanda suke saurin ficewa daga addini” Kamar yadda ibn Abil hadida ya kawo a cikin littafinsa sharhin Nahjul Balagha, JZ 1,  shafi na 201.

Sai kamar yadda zamu gani a nan gaba, da Talha da Zubai, da A’isha matar manzon All…(s) sun daga cikin wadanda suka kasance masu karya alkawali, wadanda manzon All.. (s) yace Aliyu zai yake su.

Daga nan sai ya barsu suka fita zuwa Makka. Inda suka je suka sami cewa Aisha tana cikin bakin ciki a lokacinda ta ji labarin cewa Aliyu dan abitalib (a) ya zama khalifa a bayan kissan Khalifa Uthman.

Malaman tarihi sun bayyana cewa bayan an kammala aikin Hajji na wancan shekarar,  sai ta kama hanyar Madina daga Makka, tana sauri don ta je da ga abinda Zai faru da Khalifa Uthman.

Malaman tarihin sun bayyana cewa, Aisha tana daga cikin wadanda suke ingiza mutane, kan khalifa Uthman. Wasu sunce ta fara sabani da shi ne tun lokacinda, ya haw kan kujerar Khalifanci, sai ya daidaita ta da sauran matan manzon All..(s) a rabonsu na dukiya da khalifa Umar yake basu.

Khalifa Umar yana fifitata a kan sauran matan manzon All..(s) amma Khalifa Uthman ya dai-daitasu da ita.

Wannan daya Kenan, sannan wata rana ta je wajensa tace ya bata gadonta, daga manzon All..(s). Sai yace mata, wani gado kuma, kina daga cikin wadanda suka shaida kan cewa: manzon All..(s) yace: Mu annabawa ba’a gadommu, abinda muka bari sadaka ne) a lokacinda Zahra (s) ta nemi gadonta daga babanta, kun hanata gadon babanta, sannan ki zo kice a baki gadonki daga manzon All..(s). sai ya hanata ta kara fushe da shi. Tun lokacin sunansa a wajenta ya zama Nathal, wato mai yawan gashi a jiki. Don haka basa shiri da ita.

Sannan ta bar Madina ta kama hanya zuwa Hajji a dai dai lokacinda yan tawaye suka yiwa gidan Khalifa kawanya.

Don haka da ta kammala aikin hajji sai tana sauri zuwa Madina don ta ga abinda zai faru da shi.

Amma a lokacinda ta isa wani wuri da ake kira ‘Sarf’ da sini ko sharaf da shini, sunan wani wuri kimani mel 6 daga Makka, sai ta hadu da wani mutum, daga cikin dangin mahaifiyarta, wanda ake kiransa Ubaidullahi dan Salamah, wanda ya fito daga Madina, sai ta yi sauri ta tambaye shi, wani labari kake da shi daga Madina, sai ya ce mata: An kashe Uthman :

Sai tace, sannan sun yi me? Sai ya ce, sun gamu a kan bai’a ga Aliyu, sai al-amura suka zama alkhairi a garesu.

Sai jikinta ya mutu, yanayinta ya canzu tana daga kanta sama ta sake dawo da shi kasa, tana cewa: Wallahi, ina da ace wannan(sama) ta fadi ta hadu da wannan(kasa), idan har wannan al-amarin ya tabba ga dan abitalib, to an kashe Uthman a matsayin wanda aka zalunta, kuma zan nemi fansar jininsa.

Sai Ubaidullah, yace me ya sa? Na rantse da All.. mutum na farko wanda ya fara mummunan kalma a kansa ke ce! Kin kasance kina cewa: ku kashe Naathal ya kafirta.

Amma me ya sa Aisha take wannan bakin ciki mai tsananin, kan dawowar khalifanci ga Amirulmuminina (a)? ba kome ba musulunci ya dawo da karfinsa na farko da ya rasa tare da hukumar Aliyu dan abitalib (a). Musulmi sun sami abinda suka dade suna nema.

Amma sai Aisha ta amsa wa dan kawunta kan cewa, sun nemi uthman ya tuba, bayan ya tuba suka kashe shi.

A bin tambaya ita ce, shin tana nan a lokacinda haka ya faru? Tana nan a lokacinda suka bukaci khalifa Uthman tuba, kuma tana nan sannan ya tuba? Kuma tanan nan sanda aka kashe shi? Da wa da wa suka kasashe shi? Shin Amirul muminina (a) yana daga cikin wadanda suka bada umurni a kasashe? Idan ba haka ba, me ya sa za’a dora masa laifin kissan Uthman a lokacinda mutane suka zabe shi.

Duk wadan nan tambayoyi sai ta amsa su kafin ta ce, ya zama wajibi a gareta neman fansar jinin Khalifa Uthman da yakar gwamnatin Imam Ali (a).

Ga wanda yake son sanin menene tsakanin Amirulmuminina (a) da kuma Aisha matar manzon All..(s) da kuma abinda ya sa bata son ganinsa a matsayin khalifan musulmi ta ya koma yadda tayi da manzon All..(s) da kuma iyalan gidansa tsarkaka.

Na’am, wanda ya koma baya zai ga cewa ta yi amfani da neman fansar jinin Uthman don yakar Amirulmuminina (a) ne don tsohuwar gaba da kiyayyar da takewa wannan gidan mai tsarki tun manzon All..(s) yana da ransa.

Aisha matan manzon All..(s) bata son wani alkhairi gad an uwan manzon All…(s) kuma ma’ajiyar ilminsa da matarsa diyar manzon All..(a) da kuma yayansu Alhassan da Alhussain (a) tun manzon All..(s) yana da ransa. Ta ga yadda manzon All..(s) yake girmamasu, yake, ya kebesu da kebebbiyar sonsa a garesu, ba don su danginsa ne ko kuma dan amminsa da diyarsa da jikokinsa bane, ee shi haka ne a garesu, amma don matsayin da suke da shi a wajen All..mai girma da daukka, Aliyu wasiyyinsa ne, tare da zaben All..T, ba babanta ba, Fatimah (s) diyarsa ne, amma kuma All…ya sanyata shugaban matan Aljanna, na duniya da lahira. Sannan Alhassan da Al-husain jikokinsa ne, amma kuma All…ya sanyasu cikin wasiyyan manzon All…(s) kuma daga tsotson Hussainine sauran wasiyansa 9 zasu fito. Na karshensu shi ne Mahdi na wannan al-ummar.

Don wadannan matsayi da daukakan da All..yayi masu ne suka gamu da hasadan masu hasada.

Wata rana manzon All.. (s) yana khudaba a cikin masallaci, sai yayi ishara da hannunsa ga dakinta, yana cewa,: Nanne fitina, nan ne fitina, nan ne fitina daga inda kahon shaitan zai fito.

Wannan kamar yadda ya zo a cikin Shahihul Buhari JZ daya, shafi na 125 a babin wajibcin Khumusi,

Hadisi mai kama da wannan ya zo a cikin Sahih Muslimu JZ na biyu  shafi na 503

Malaman tarihi sun bayyana cewa manzon All..9s) ya yi mata barazana da sakinta sau da dama, saboda yadda take cutar da shi da wadannan iyalan gidansa tsarkaka.

Ta ga yadda manzon All..(s) ya himmato da sin Aliyu da Matarsa Fatimah (s), himmatuwar da dukkan matansa basu samu irinsa ba.   

Wata rana babanta ya nemi izinin shiga wajen manzon All..(s), a lokacinda ya shiga, sai ya ji muryanta sama da muryar manzon All..(s). tana cewa: Wallah na san cewa, Aliyu ya fi soyuwa a wajenda da ni da babana, ..ta nanata wannan har sau biyu ko uku.

Kamar yadda Ahmad bin Hambal ya kawo a cikin Musnadinsa JZ 4 shafi na 275.

Banda haka, wani abinda yake mata zafi shi, bata haihuba, kamar yadda sauran matansa basu haihu ba, amma sai tana ganin yadda ya maida soyayyansa da jikokinsa Imam Hassan da Imam Alhussain. Yana sonsu matukar so, baya son duk abinda zai taba su.

Don haka ta tsaya tsayin daka, tun bayan manzon All..(s) don tabbatar da cewa Alioyu bai sami matsayin khalifanci ba. Amma gashi al-amarin ya kubuce mata. Ali ya zama Khalifa. Shi ne take neman duk wata hanya ta fidda khalifanci daga hannunsa.

Wannan duk tare da cewa ta ji manzon All..(s) yana fada dangane da Aliyu (a) falaloli, masu yawa. Cewa shi danuwansa ne, matsayinsa da shi, kamar matsayin haruna da Musa ne, har ya kara da cewa a hadisin Ghadir: Ya ubangiji ka jibanci wanda ya jibanceshi ka yi adawa da wanda yayi adawa da shi ka tabard wannan ya tabar da shi, ka risker da gaskiya tare da shi.) har zuwa karshen hadisin.

Amma hasada da rufe zuciyarta, tana neman duk wata hanya ta yakarsa da kuma dauke khalifanci daga hannunsa idan zata iya.

Sannan wani abnda ya sa bata son khalifanci ga Aliyu dan Abitalib sun hada da cewa tana son khalifanci ta koma cikin danginta, Banu taim. Tana son dan amminta Talha dan Ubaidullah ya zama Khalifa. Kamar yadda wasu malaman tarihi, musamman Akkad ya kawo a cikin littafinsa mai suna Abkariyyatul Imam Ali (a).

Hakama Ibnu Abil hadid ya kawo shi cikin sharhinsa na Nahjul Balagha JZ 6 shafi na 215.

Sannan na uku, wasu malaman tarihi suna ganin, ta fake ne da neman jinin Uthman, amma a shari’a, mai neman jinin wanda aka kashe shi danginsa na kusa, musamman dansa na cikinsa, idan babu shi to shugaban musulmi shi ne da hakkin ya nemi jinin wanda bai da waliyi. Khalifa Uthman yana da yaya maza wadanda zasu nemi hakkin zubar da jinin mahaifinsu, Aisha da Talha da Zubair da Mu’awiya da sauransu basu da hakkin neman jinin Uthman a lokacinda yayansa suna da rai. Sannan khalifan musulmi yana nan.

Wannan babban malami Allamah Ala’ili dan kasar Lebanon amma yayi karatu a jami’an alazhar a cikin littafinsa.

Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu nay au sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu assalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: daga cikin wadanda masu sauraro wadanda suka kamar yadda

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamna Namadi Ya Biya Sama Da Naira Biliyan Daya Ga Tsofaffin Ma’aikata

Hukumar Tsarin Fansho na Hadin Gwiwa tsakanin Jiha da Kananan Hukumomi a Jihar Jigawa ta bayyana cewa ta raba sama da Naira Biliyan 1 da dubu 500 ga tsofaffin ma’aikata 569.

Yayin da yake jawabi ga wadanda suka ci gajiyar shirin a gaban Gidan Fansho kafin fara rabon kudin, Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, Alhaji Muhammad K. Dagaceri, ya bayyana tsarin fansho na jihar a matsayin daya daga cikin mafi nagarta a kasar nan.

A cewarsa, fiye da jihohi ashirin sun kai ziyara jihar Jigawa domin koyon yadda take tafiyar da shirin fansho.

Ya jinjina wa Gwamna Umar Namadi saboda dagewarsa da kuma jajircewarsa wajen dorewa da inganta tsarin fansho a jihar.

Alhaji Dagaceri ya yabawa Gwamna Namadi kan goyon bayansa da matakan da ya dauka tun bayan hawansa mulki domin inganta tsarin, yana mai jaddada irin tasirin alherin da shirin ke yi ga tsofaffin ma’aikata da daukacin ma’aikatan gwamnati.

Ya bukaci tsofaffin ma’aikata da wadanda ke aiki yanzu da su ci gaba da yi wa gwamnati addu’a, tare da nuna godiya ga Gwamna Namadi bisa irin ayyukan alherinsa.

A nasa jawabin, Shugaban hukumar ta Fansho, Dr. Binyaminu Shitu Aminu, ya bayyana cewa fiye da naira biliyan 1 da rabi ne za a raba tsakanin tsofaffin ma’aikata 569.

“Wannan adadi ya kunshi nau’o’in biyan kudi daban-daban, ciki har da hakkokin ritaya, hakkokin mutuwa da sauran ragowar hakkokin fansho na mamatan ma’aikata,” In ji Dr. Aminu.

Dr. Aminu ya kara da cewa, cikin wadanda za su amfana, 287 sun fito ne daga ma’aikatan jiha, 158 daga kananan hukumomi, yayin da 124 suka fito daga Hukumar Ilimin Kananan Hukumomi (LEA).

Ya kara da cewa, za a biya sama da Naira Miliyan 875 ga ma’aikatan da suka yi aiki a karkashin gwamnatin jiha, sannan sama da Naira Miliyan 355 kuma ga wadanda suka fito daga kananan hukumomi, da kuma sama da naira miliyan 274 ga wadanda suka fito daga LEA.

Shugaban hukumar ya tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da biyan hakkokin fansho a kan kari, ciki har da biyan fansho na wata wata a cikin mako na farko na kowane wata.

 

Ya jaddada kudurin gwamnatin jihar na inganta walwalar ma’aikata, domin samun rayuwa mai kyau da kwanciyar hankali bayan kammala aikin.

Usman Muhammad Zaria

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamna Namadi Ya Biya Sama Da Naira Biliyan Daya Ga Tsofaffin Ma’aikata
  • Kissoshin Kayuwa: Sirar Imam Hassan(a) 122
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan Almujtaba 121
  •  Rasha Ta Kai Munanan Hare-hare Akan Birnin Kiev Na Ukiraniya
  • Gwamnatin APC ta jefa ’yan Najeriya cikin ƙangin talauci — Shugabar LP
  • LP za ta ceto Nijeriya daga halin da APC ta jefa ta — Nenadi Usman
  • Musuluntar Wata Ce Ya Ja Hankalina Shiga Fim – Sailuba Dadin Kowa
  • Ta’addanci: Alƙawuran sojoji 8 na kamo Bello Turji
  • Duk da kashe jagororin ’yan bindiga, Turji na ci gaba da kai hare-hare