NAJERIYA A YAU: Matakan Da Muke Dauka Don Karfafawa ’Yan Najeriya Kwarin Gwiwar Kada Kuri’a —INEC
Published: 28th, July 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
’Yan Najeriya da dama ne dai aka bayyana ba sa fitowa kaɗa kuri’a a duk lokacin da zaɓe ya zagayo.
Wasu daga cikin ’yan ƙasar sun bayyana rashin jin daɗin abun da hukumar zaɓe ke yi, rashin yarda da sakamakon zaɓuɓɓukan da suka gabata da dai sauransu a matsayin dalilansu na rashin kaɗa ƙuri’a.
Ko waɗanne matakai Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) take ɗauka don ƙarfafawa ’yan Najeriya gwiwan fitowa su kada ƙuri’a a zaɓen 2027?
NAJERIYA A YAU: Yadda masu yi wa kasa hidima za su ci arzikin yankunan da suke aiki DAGA LARABA: Abubuwan da ya kamata yara su yi yayin hutun makarantaWannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Hauhawar farashi ya ragu a watan Agusta — NBS
Hukumar ƙididdigar a Najeriya NBS ta bayyana cewa an samu raguwar hauhawar farashin kaya a watan Agusta idan aka kwatanta da watan Yulin da ya gabace shi.
Cikin sabbin alƙaluman da NBS ta fitar a ranar Litinin sun nuna cewa an samu raguwar kashi 1.76 a watan Agustan saɓanin watan Yulin, wanda ya nuna karo na hudu ke nan a jere hauhawar farashin yana sauka.
NDLEA ta kama ɗan Indiya da ƙwaya ta Naira biliyan 3 a Legas Kundin Bajinta na Guinness ya taya Hilda Baci murnaRahoton na hukumar NBS na zuwa ne kwanaki bayan da Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin karya farashin kayan abinci ƙasar.
A watanin baya-bayan an riƙa samun raguwar hauhawar farashin kayyaki a ƙasar.
Ko alƙaluman da NBS ta fitar a watan Yuni, ta bayyana cewa hauhawar farashi a Najeriya ya sauka zuwa kashi 22.22 daga 22.97 da aka samu a watan Mayu.
A baya dai dai an yi ta kiraye-kirayen gwamnatin ƙasar ta ɗauki matakan rage hauhawarar farashi domin magance tsadar rayuwa da ake fuskanta a ƙasar.