HausaTv:
2025-11-02@17:09:51 GMT

Kissoshin Kayuwa: Sirar Imam Hassan(a) 122

Published: 28th, July 2025 GMT

122- Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da haka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin da suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtadha Muttahhari, ko kuma cikin littafin mathnawa na maulana Jalaluddeen Rum ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.

////… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata a kuma cikin sarir Imam Al-Hassan Almujtaba (a) diyar Fatima (s) kuma jikan manzon All..(s) na farko, idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata mun bayyana yadda.

Ummul muminina Aisha matar manzon All..(s) ta gabatar da khuba mai tsawo a Makka tana kirin mutanen Birnin su fito tare da ita cewa, Basra na kasar Iraki don neman jinin Khalifa Uthman, sannan daga cikin wadanda suka kira har da sauran ummahatul muminin, daga cikin har da umma salama. Inda ta shiga tana yabunta, daga karshe Ummu Salma (r ) ta yi mata nasiha, ta kuma tunanatar da ita girman Aliyu dan Abitalib (a) a wajen manzon All..(a), amma bata dauka ba. Sannan ta kama hanyarta zuwa Madina, ta kuma rubutawa Amirul muminina (a) wasika inda ta fada mata Shirin Aisha. Sannan ta aiki danta da wasikar ta bukaci danta Umar dan Abisalma ya taimaka masa a kan makiyansa.

Har’ila yau malaman tarihi sun bayyana cewa Yaala dan Umayya dan Ubaidata Attamini. Wanda ya kasance walin Khalifa Umar a wasu wurare a kasar Yemen, sannan Khalifa Uthman ya sanyashi wali a birnin Sanaa abban birnin kasar Yemen. Sannan daga karshe ya ji labarin kissan Khalifa Uthman yana babban kwamandan sojojin a kasar Yemen.

Don haka ya yi sauri don ya taimaka masa, amma kafin ya iso madina ya ji an kasashe. A lokacinda ya zo Makka ya ji abinda Aisha da Talha da Zubair suke kokarin yi, sai ya taimaka masu. Ya bawa Zubair dinari dubu 400. Sannan ya bawa sojojin Aisha 70 guzurin hanya don zuwa tare da ita. Banda haka ance shi ya bawa Aisha rakumin da ta hau wacce ake kiranta Askar.

Don haka a lokacinda Aisha ta fita daga makka, ta yi tafiya da rundunarta har tayi zango a wani wuri da ake kira Zeekar kusa da kufa. Sai ta hadu da Sa’eed dan Ass daya daga cikin gwamnonin Usman a Kufa, bayan walid.

Sai saeed Al-umawi ya tambayeta: Ina zaki je ya Ummul muminin? Sai tace: Basra,

-Me zaki yi a can.

-Ina neman fansar jinin Uthman.

Sai yayi Dariya, snnan yace: Ga wadannan tare da ke su suka kashe Uthman, sai ta juya fuskanta daga gare shi. Daga nan sai ya wuceta, ya ji wajen Marwan ya ce masa: Kaima kana zuwa basra ne ? sai yace : ee.

-Me kake so?

– Ina neman fansar jinin Khalifa Uthman.

-To ai ga wadanda suka kashe Uthman tare da kai. Wannan mutane biyu sune suka kashe Uthman, suna sun khalifanci wa kansu, A lokacinda ta fice daga hannunsu. Sai suka ce: Zamu wanke jinni da jinni. Laifi da tuba. Bai saurare shi ba. Sun ci gaba a kan hanyarsu ta zaluntar Amirul muminina da kuma raba kan al-ummar manzon All..(s) kan karya.

A cikin tafiyarsu zuwa Basra sai dare ta riskesu a wani wuri da ake kira Haw’abu, akwai ruwa a wurin,  sai taji karnuka suna haushin ayarinta, sai ta tsorata. Sai ta kira Muhammad dan Talha dai Ubaidullahi, ta tambaye shi. Wani ruwa ne wannan sai yace: Haw’abu.

Sai kara tsorata, sannan da yi nadamar abinda ya fito da ita. Sai ce: Ai ni zan koma!

-me yasa?

-Naji manzon All…(s) yana fadawa matansa: Kamar ina ganin daya daga cikinku hakika karnukan Haw’aba sun yi mata haushiu, kuma ina maki gargadi kada ki kasance ita, ya ke humaira.

Sai Muhammad dan Talha yace mata: Ki bar wannan maganar, mu wuce. Amma ba ta gamsu da maganarsa ba. Ta dage kan cewa zata juya ta koma. Ana cikin wannan halin sai labari ya kaiwa Talha da Zubair wanda suke cikin ayarinta. Sai suka taho wakinta, sun yi mata Magana, amma bata gamsu ba.

Sun kuma tabbatar da cewa idan ta fice daga cikinsu to abinda suke fatan samu ya tafi a banza.

Don haka sai suka kawo mata mutane, wadanda suke saye su, wasu suka ce yawansu ya kai 50, suka rantse da All..kan cewa wannan wurin ko wannan Ruwan ba Ruwan Haw’aba bane. Ance wannan shi ne shaidar Zur na farko a musulunci.

Da abinda ya dace mata, shi ne ta koma gidanta, bayan ta tuna da hadisin mikinta manzon All…(s). Amma sai ta gamsu da karyan da wasu suka yi mata, sai ta ce gaba ta je ta jawo raba kan al-ummar musulmi tare da yakar dan uwan manzon All..(s).

A lokacinda suka isa kusa da garin Basra. Suka yi sansani a wajen garin. Sai gwamnan garin Basra a lokacin shi ne, Uthman bin Hunaifa mutumin Madina ne daga kabilar Aws.

Kafin Imam Ali (a) ya nada shi walin Basra, ya taba zama gwamnan garin a lokacin Khalifa Umar, ya kuma yi aiki mai kyau na kyautata ayyukan numa. Sannan a lokacinda Imam Ali ya nemi shawarar mashawartansa suka nuna masa shi sai ya sake tura shi gwamnan Basra.

Don haka sai Uthman bin Hunaifa, ya aiki Abu aswad Addu’ali zuwa wajenta, don sanin abinda ya zo da ita.

A lokacinda Abul Aswad Addua’ly ya isa wajenta sai yace mata: Me yazo da key a ummul muminina ko?

Sai tace: Neman jikin Uthmanu.

-babu mutun ko daya, a Basra daga cikin wadanda suka kashe uthman.

-Ka yi gaskiya, amma kuna tare da Aliyu dan Abitalib (a) dake Madina. Na zo don kiran mutanen Basra saboda yakarsa.  Ba za muyi fushi da ku kan faduwar Uthman ba, amma ba zamu yi fushi wa Uthman daga takubbanku ba.?

Sai Abu Aswad Addu’ali ya mayar mata da kalmomi masu hikima. Yana cewa: Me ya hadaki da bulala da kuma takobi? Ai abinda muka sani ke masoyiyar manzon All..(s). ya umurceki ki zauna a gidanki, ki karanta littafin Ubangijinki, yaki bai wajaba a kan mata ba. Kuma ba ruwansu da neman jinin wanda aka kashe.

Kuma lalle Aliyu ya fi cancanta da ke, kuma ya fi ki kusa da shi a kan wannan al-amarin.  Don dukkanku yan abdul manaf ne.

Sai tace: Ba zan je ko ina ba, sai na yi abinda ya kawo ni. Shin Abu aswad kana tsammanin wani ya isa ya yake ni?  Sai yace mata: Na rantse da All..Za’a yake ki, yaki mai tsanani.

Sannan ya barta, yaje wajen Zubaira, sai ya tunatar da shi, abinda ua shude na biyayyarsa ga Aliyu dan Abitalib (a). Yana cewa: Ya Baban Abdullahi, mutane sun sanka da cewa, a ranar da aka yi bai’a wa Abubakar, kana rike da takobinka kana cewa: ba wanda ya cancanci wannan al-amarin in banda dan Abitalib(a), ina wannad matsayin da wannan.

Sai Zubair yace: Muna neman Jinin Uthman.

-Kai da abokinka, kun yi masa bai’a kamar yadda na sami labari. Sai Zubair ya karaya, da nasihan Abu Aswad Addu’ali ya yi masa, ya tabbatar da cewa shi ne gaskiya da shiriya. Sai yacewa Abu Aswad ya je yayi magana da abokinsa Talha dan Ubaidullah ikan al-amarin.

Sai Abuaswad Addu’ali ya je yayiwa Talha dan ubaidullahi Magana, amma ya dage kan cewa, sai sun yaki Amirulmuminina (a).

Sai Abu Aswad ya koma wajen Uthman dan Hunaif ya fada masa abinda ya ji ya gana daga wadannan mutane, da kuma dagewarsu sai sun yaki Ali (a) da kuma magoya bayansa.

Daga nan sai dan Hunaif ya tare mutanen Basra yayi masu khuduba yana cewa: Ya ku mutane! Abin sani kawai shi ne kun yi mubaya’a ga All..

{Hannun All..yana kan hannayensu, wanda ya kunce , to lalle hakiki ya kwancewa kansa, wanda kuma ya cika abinda yayiwa All..alkawali, to da sannu zai bashi lada babba}

Na rantse da All…da Aliyu ya san cewa akwai wanda ya cancanci wannan al-amarin da bai karbe shi ba. Da kuma mutane sun yi bai’a ga wani da yayi masa mabaya’a kuma ya yi biyayya a gareshi. Baya bukatar wani daga sahabban manzon All..(s). amma ba wani daga cikinsu wanda baya bukatar taimakonsa.

Kuma hakika ya yi tarayya da su a kyawawansu, ba wanda yayi tarayyar da shi a kyawansa.

Wadan nan mutane biyu -wato Talha da Zubair-sun yi masa mubaya, ba All.. suke nufi ba da wannan fitarsu ba. Sai dai sun gaggauta yaye ne kafin lokacinsa shayarwa ya kare, sanna sun gaggauta shayarwa kafin haihuwa. Haka ma haihuwa kafin daukar ciki.

Sun nemi ladar All..daga bayinsa. Sun riya cewa sun yi bai’a a dole, — har zuwa inda yake cewa. Ku saurara, gaskiya tana tare da mutane gama gari, kuma mutane suna kan bai’ar Aliyu. Me kuke gani yak u mutane?

Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu nay au sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu. Wassalamu alaikum wa rhamatullahi wa barakatuhu.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: Aswad Addu ali masu sauraro wadanda suka

এছাড়াও পড়ুন:

 Gaza: Daga Tsagaita Wuta Zuwa Yanzu Fiye Da Mutane 200 Ne Su Ka Yi Shahada

Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta sanar da cewa daga lokacin da aka tsayar da wuta zuwa yanzu adadin Falasdinawan da HKI ta kashe sun kai 200, yayin da wasu  kusan 600 sun jikkata.

Sanarwar ta ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta kuma ci gaba da cewa; A cikin sa’o’i 48 da su ka gabata,an sami shahidai 22, biyar daga cikinsu basu dade da yin shahada ba, sai kuma 17 da aka tono su daga karkashin baraguzai. Haka nan kuma na kai wasu 9 zuwa asibitocin da suke a yankin.

Wani sashe na sanarwar ma’aikatar kiwon lafiyar ta Gaza ya ce, har yanzu da akwai shahdai masu yawa da suke a karkashin baraguzai, wasu kuma a kan hanyoyi, saboda rashin kayan aiki da kungiyoyin agaji za su yi amfani da su.

Tun daga ranar 7 ga watan Oktoba na 2023 zuwa yanzu, adadin shahidai ya kai 68,858, sai kuma wani adadin da ya kai 170,664 da su ka jikkata.

Amma daga tsayar da wuta a ranar 11 ga watan Oktoba zuwa yanzu, an sami shahidai da sun kai 226, sai kuma wasu 594 da su ka jikkata. Haka nan kuma an iya tsamo gawawwakin shahidai daga cikin baraguzai har su 499.

Haka nan kuma ma’aikatar kiwon lafiyar tra sanar da karbar gawawwaki 30 da HKI ta mika wa bangaren Falasdinawa ta hannun hukumar agaji ta “Red-Corss.

Tun bayan tsagaita wutar yaki, har ya zuwa yanzu dai HKI tana ci gaba da kai hare-hare a sassa daban-daban na Gaza.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Shugaban Kasar Najeriya Ya Mayar Da Martani Ga Takwaransa Na Amurka Akan Rikicin Addini November 1, 2025 Iran ta damu da halin da ake ciki a yankin El Fasher na Sudan November 1, 2025 Kwamitin Tsaron MDD ya goyi bayan shirin Morocco game da yankin Yammacin Sahara November 1, 2025 Samia Suluhu Hassan ta lashe zaben shugaban kasa a Tanzaniya November 1, 2025 Najeriya ta musanta ikirarin Trump, na cewa Kristoci na fuskantar babbar barazana a kasar November 1, 2025 Majalisar Dinkin Duniya ta damu da hare-haren Amurka a Caribbean da Pacific November 1, 2025 Israila Ta Kai Hari  Kan Ofishin kungiyar UNICEF Dake Gaza A November 1, 2025 Amurka Na Shirin Kai Hari Kan Kasar Venzuwela A Kowanne Lokaci November 1, 2025 Iran Ta Sanya  Da Ranar 30 Ga Watan Nuwamba A Matsayin Ranar Kasa Ta Tsibirai 3 October 31, 2025 Isra’ila Na Ci Gaba Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza October 31, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • 2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su
  • Tsokaci Dangane Da Juyin Mulki A Nahiyar Afirka
  •  Gaza: Daga Tsagaita Wuta Zuwa Yanzu Fiye Da Mutane 200 Ne Su Ka Yi Shahada
  • Samia Suluhu Hassan ta lashe zaben shugaban kasa a Tanzaniya
  • Zaɓen Tanzania: Shugaba Samia Suluhu Hassan ta yi tazarce
  • An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3
  • Gwamnatin Jihar Kwara Ta Kafa Kwamitoci 2 Don Tantance Wadanda Suka Yi Ritaya
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar
  • Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP
  • Sin Ta Fitar Da Jerin Sakamakon Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Tawagar Kasar Da Ta Amurka Suka Cimma