Aminiya:
2025-07-28@15:15:11 GMT

Matsalar Lantarki: Ga tsada ga rashin wuta

Published: 28th, July 2025 GMT

Duk da ƙarin kuɗin wutar lantarki da sabbin dokokin da aka yi don inganta ɓangaren, yawancin ’yan Najeriya na ci gaba da fama da karancin wutar da kuma tsadarta.

Wannan matsalar babu wanda ta bari, daga manyan masana’antu zuwa ƙananan gidaje a sassa daban-daban a Najeriya.

Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya sanar cewa gwamnati tana aiki don magance matsalolin, amma duk da haka ’yan Najeriya na ci gaba da kokawa kan matsalar, wadda ta ƙi ci ta ƙi cinyewa.

A watan Fabrairun 2024, Gwamnatin Tarayya ta sanya hannu kan sabuwar Dokar Wutar Lantarki. Ta bayyana cewa munafar dokar ta haɗa da taimakawa da kuma bai wa jihohi damar samarwa, turawa, da kuma rarraba wutar lantarki na ƙashin kansu ta hanyoyi daban-daban na cikin gida kamar hasken rana da sauransu.

An gano gawar mutum 15 bayan hatsarin kwalekwale a Neja Gwamnatin APC ta jefa ’yan Najeriya cikin ƙangin talauci — Shugabar LP

Kodayake jihohi 11 sun karɓi wannan doka, amma yawancin al’umma da ’yan kasuwa ba su ga wani sauyi  na a-zo-a-gani ba. Hasali ma, kokawa suke yi bisa yawan katsewar wutar lantarki da kuma rashin ƙarfinta.

Ninka kuɗin wutar lantarki sau uku da aka yi wa kwastomomi da ke kan layin Band A, waɗanda aka yi musu alƙawarin samun wutar aƙalla sa’o’i 20 a kullum, shi ma ya bar baya da ƙura.

Gwamnati Tarayya ta bayyana cewa ta janye tallafin wutar lantarki ne domin inganta ɓangaren ta yadda jihohi za su iya samarwa. Haka kuma jama’a za su riƙa samun wuta mai inganci gwargwadon yadda suke biya.

A kan haka ne aka ƙirkiro da tsarin Band A wanda aka ninka kudinsa sau, tare da alƙawarin bayar da wutar aƙalla awa 20 a kullum ga masu amfani da layin.

Amma yawancin mutanen da ke kan Band A sun ce duk da tsadar kuɗin da suke biya, ba su samun wutar yadda aka yi musu alƙawari. Wasunsu ma na zargin cewa ko babu wutar mitocinsu suna ci gaba da lissafa amfani da ita, wanda ke tilasta musu amfani da injinan janareto.

Wata babbar matsala ita ce sama da rabin masu amfani da wutar lantarki a Najeriya ba su da mita, wanda ke nufin kamfanonin rarraba wutar lantarki na canjin si kudin wuta ne bisa ƙiyasi, wanda galibi ke da tsada kuma babu adalci.

Masana’antu suna wahala

Tsawon shekaru, musamman a tun bayan cefanar da ɓangaren wutar lantarki da gwamnatin Najeriya ta yi, har yanzu matsalar ta ƙi ci, ta ki cinyewa.

Masu masana’antu a Kano, misali, suna kashe miliyoyin naira duk wata a kan kuɗin wutar lantarki amma har duk da haka suna dogara ne a kan injinan janareto saboda rashin tabbacin samun wuta.

Wani mai ƙaramar masana’anta a Kano, Yusuf Bello Yakasai, ya ce sama da kashi 60 bisa 100 na ribarsa tana tafiya ne a biyan kuɗin wutar lantarki.

Wani kuma, Habibu Sulaiman, ya ce miliyan biyu yakw biyan kuɗin wuta a duk wata, wanda ke cinye kaso mai tsoka na ribarsa.

Don haka suka yi kira ga gwamnati da ta dawo da tallafin wutar lantarki ga masana’antu.

A Maiduguri, yawancin kasuwanci da sana’o’i, ciki har da masu injinan niƙa da bankuna, suna aiki ne kusan gaba ɗaya da injinan janareto, masu amfani da man dizel, saboda wutar lantarki ta kasa da sa’o’i uku suke samu a kullum. Wasu ma sun sauka daga kan babban layin wutar na ƙasa saboda yawan lalacewar injinansu, sakamakon tsada yawan rashin daidaiton ƙarfin wutae da ke lalata musu kayan aiki.

Masu ƙananan sana’o’i a Kaduna sun bayyana cewa yanzu kuɗin wutar ke cinye sama da kashi 60% na abin da suke samu.

Abraham Benson, wani mai kamfanin buga takardu, ya ce tsadar kuɗin wutar lantarki, tare da tsadar man fetur da sauran kayan aiki, suna sa kasuwanci ya yi wuya.

Ya kuma yi imanin cewa tsarin rarraba Band A zuwa Band D ba adalci ba ne, hasali ma haifar da tsadar kayan aiki yake yi, wanda kuma ke shafar farashin kayan da aka sana’anta.

Kira don ɗaukar mataki

Mazauna jihohin Binuwai da Filato suna da ƙwarin gwiwa cewa samar da wutar lantarki na gida a jihohi zai inganta abubuwa kuma zai rage tsadarta.

A Jihar Legas, wasu kwastomomi da ke kan layin Band A suna ƙorafin tsadar kudin wuta. Kodayake sun ce suna samun wutar akai-akai, amma duk da haka suna neman a sauya su zuwa ƙananan Band, sa’annan a ba kowa mita.

Masana suna kira ga jihohi da su yi amfani da sabuwar dokar kuma su mayar da hankali kan samar da wutar lantarki na ƙashin kansu ta hanyar amfani da albarkatun gida kamar kwal ko hasken rana da sauransu. Sun yi imanin cewa wannan zai sa wutar lantarki ta zama mai araha.

Duk da yawan ƙorafe-ƙorafen,  kakakin Ministan Wutar Lantarki, Bolaji Tunji, ya nace cewa an samu ci-gaba a ɓangaren, yana mai cewa matsalolin da suka yi shekara da shekaru ana fama da su, ba zai yiwu a iya magance su “farat ɗaya ba.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: kuɗin wutar lantarki da wutar lantarki wutar lantarki na a ɓangaren

এছাড়াও পড়ুন:

Rashin abinci mai gina jiki ya kashe yara 650 a Katsina — MSF

Wani rahoto daga ƙungiyar likitocin ƙasa da ƙasa wato Medecins Sans Frontiere na nuni da cewa sama da yara 650 ne suka mutu bayan fuskantar ƙarancin abinci mai gina jiki a Jihar Katsina.

Medicins Sans Frontiere wadda ta fara aiki a Katsina tun shekarar 2021, ta ce ta samu ƙaruwar yara masu fama da yunwa sanadiyyar rashin abinci mai gina jiki da aka isar da su zuwa cibiyoyin kula da marasa lafiya da ƙungiyar ke da su a yankin.

Za mu ba da damar shigar da kayan agaji a Gaza — Isra’ila Super Falcons ta lashe gasar WAFCON karo na 10 bayan doke Maroko

A cewarta, a tsakanin Janairu da Yuni 2025 ta yi jinyar kusan yara 70,000 da ke fama da tamowa a Jihar Katsina, ciki har da kusan 10,000 da ke bukatar kulawa da ta dace daga likitoci .

“A wannan shekarar ta 2025 a cewar ƙungiyar, yara 652 suka mutu saboda rashin samun kulawa akan lokaci,” in ji Ahmed Aldikhari, mai magana da suna ƙungiyar ta MSF a Nijeriya, kamar yada sanarwa ta tabbatar a ranar Juma’a.

MSF ta ce yaran da iyaye sun fuskanci tarin matsaloli ne sakamakon raguwar tallafin da ake samu daga ƙasashen duniya, inda manyan ƙasashe masu bayar da tallafi da suka hada da Amurka da Birtania da kuma Tarayyar Turai suka rage kudaden da suke bayarwa.

Ana iya tuna cewa a wannan makon nan da muke bankwana da shi ne Hukumar Samar da Abinci ta Duniya (WFP) ta sanar da dakatar da tallafin abinci na gaggawa ga mutane milyan 1.3 a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya daga karshen watan Yuli, sakamakon karancin kudade.

Ƙungiyar ta ce adadin yaran da ke fama da matsalar rashin abinci mai gina jiki wanda ya fi kamari kuma mai barazana ga rayuwa a Jihar Katsina ya karu da fiye da kashi 200 cikin 100 idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Rashin abinci mai gina jiki ya kashe yara 650 a Katsina — MSF
  • NSCDC Ta Gurfanar Da Wanda Ake Zargi Da Badakalar Naira Miliyan 159
  • Matashi ya tono gawar kakarsa don yin tsafin kuɗi da ƙoƙon kanta
  •  Gaza: Ana Ci Gaba Da Samun Shahidai Da Yunwa Take Kashewa A Gaza
  • Matashi ya tono gawar kakarsa don yin tsafin kuɗi ya sare kan gawar kakarsa don yin tsafi
  • Araqchi Ya Jaddada Cewa; Karfin Kariya Da Makamai Masu Linzamin Iran Ne Suka Tilastawa Makiya Neman Tsagaita Wuta
  • ADC Ga Tinubu: Ina Wutar Lantarki Ta Awa 24 Da Ka Yi Wa ‘Yan Nijeriya Alkawari?
  • Jihohin Da Ke Shirin Rage Kudin Wutar Lantarki Su Shirya Biyan Tallafi – Ministan Wuta
  • An yanke wa mutum 3 hukuncin kisa kan kisan kai a Gombe