Wulayati: Hanyar Zangezur Wata Shirin Amurka Ne Don Matsa lamba Kan Kasashen Iran Da Rasha
Published: 28th, July 2025 GMT
Mai ba da shawara ga Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya bayyana cewa: Hanyar Zangezur wata shiri ne na Amurka don matsawa kasashen Rasha da Iran.
Ali Akbar Velayati mai ba wa Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran shawara kan harkokin kasa da kasa, ya dauki aikin Zangezur (arewa maso yammacin Iran) a matsayin wani aikin Amurka na matsawa kasashen Rasha da Iran lamba.
A cikin wani sako na tunawa da Sheikh Safi al-Din Ardebili, Velayati ya yi tsokaci kan batutuwan da suka shafi Azarbaijan da mashigar Zangezur, yana mai cewa, “Makiya Iran karkashin jagorancin ‘yan sahayoniyyan duniya da Amurka, suna neman ta hanyar tsare-tsare irin su mashigar Zangezur, don ciyar da manyan ayyukan siyasa a karkashin fakewa da wadannan tsare-tsare.”
Ya kara da cewa, manufar farko ita ce raunana gwagwarmaya da yanke alakar Iran da yankin Caucasus da kuma killace Iran da Rasha ta kasa a kudancin yankin.
Ya bayyana cewa: “Wannan aikin ba wai kawai wani bangare ne na shirin Amurka na maye gurbin Ukraine da yankin Caucasus a matsayin wani sabon fage na matsin lamba kan Rasha da Iran ba, amma ana aiwatar da shi ne tare da goyon bayan kungiyar tsaro ta NATO da kuma wasu kungiyoyin ‘yan kishin kasa na Turkiyya (Pan-Turkist).
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kasar Ukraine Ya Nuna Sha’awar Ganawa Da Shugaban Kasar Rasha
Shugaban kasar Ukraine ya nuna sha’awar ganawa da shugaban Rasha kan neman hanyar warware rikicin da kasashen biyu ke fama da shi
Ana ci gaba da yakin Ukraine musamman ta hanyar kai hare-hare da jiragen sama marasa matuka coiki. Ma’aikatar tsaron Rasha ta sanar da kakkabo jiragen sama marasa matuka ciki guda 105 na Ukraine da aka harba zuwa yankuna tara, a tekun Azov, da kuma cikin kasar Rasha a daren jiya.
Shugaban kasar Ukraine Zelenskyy ya ce: Kasarsa tana da kudade don sarrafa tsarin makamai masu linzami na Patriot guda uku kuma yana neman samar da karin kudade don sarrafa wasu bakwai na daban, gami da taimakon abokan huldarsa na kasashen Turai.
A cikin wata sanarwa da ofishinsa ya fitar, Zelenskyy ya tabbatar da cewa: Ukraine na fuskantar gibin kudade da aka kiyasta kimanin dala biliyan 40 a shekara mai zuwa, yana mai kira ga kasashen duniya da su ci gaba da ba da tallafin kudi da na soji “domin kare ‘yancin kai na Ukraine da dawo da kwanciyar hankalin tsaron kasarta.”