HausaTv:
2025-04-30@19:35:51 GMT

ICC ta yi kakkausar suka ga Hungary saboda yin watsi da sammacin kama Netanyahu

Published: 2nd, April 2025 GMT

Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) mai hedkwata a birnin Hague ta yi Allah-wadai da matakin da kasar Hungary ta dauka na kin mutunta sammacin kame firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da zai ziyarci kasar da ke tsakiyar Turai a ranar Alhamis.

Mai magana da yawun kotun, Fadi El Abdallah, ya fada yayin wani taron manema labarai cewa, bai kamata mambobin kotun ICC su yi watsi da hukuncin kotun ba.

Kakakin ya ci gaba da cewa dole ne mambobin kotun su aiwatar da hukuncin da kotun ta yanke.

Ana sa ran Netanyahu zai isa Budapest a yammacin yau Laraba don ziyarar kwanaki hudu, bisa gayyatar Firaministan Hungary Viktor Orbán.

Shugaban na Hangari mai tsatsauran ra’ayi ya gayyaci takwaransa na Isra’ila duk da tuhumar da ake yi wa Netanyahu a hukumance da laifin amfani da yunwa a matsayin hanyar yaki da kuma aikata laifukan cin zarafin bil’adama a Gaza.

Kotun hukunta manyan laifuka ta ICC ta bayar da sammacin kama Netanyahu da tsohon ministansa na yaki, Yoav Gallant, bisa zargin laifukan yaki da cin zarafin bil adama a ranar 21 ga Nuwamba, 2024.

An bayar da sammacin ne bayan tantance akwai “kwararen dalilai ” dake cewa Netanyahu da Gallant “da gangan sun hana farar hula a Gaza abuban more rayuwa, ciki har da abinci, ruwa, da magunguna da kuma man fetur da wutar lantarki.” A Gaza.

A matsayinta na mamba a kotun hukunta manyan laifuka ta ICC, dole ne Hungary ta kama Netanyahu da zarar ya isa a tsakiyar nahiyar Turai tare da mika shi ga kotu, saidai duk da haka Hungary, ta fito karara cewa ba za ta mutunta hukunci da bukatun kotun ta ICC ba.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: Netanyahu da

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnan Sokoto Ya Amince Da Sauya Wa Manyan Sakatarori 25 Ma’aikatu A Jihar 

Gwamnatin jihar ta ce, matakin na daya daga cikin kokarin gwamnati mai ci na inganta ayyukanta domin samar da romon dimokuraɗiyya ga al’ummar jihar Sokoto.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An kashe Falasdinawa kusan 30 a wani sabon kisan kiyashin Isra’ila a Gaza
  • Gwamnan Sokoto Ya Amince Da Sauya Wa Manyan Sakatarori 25 Ma’aikatu A Jihar 
  • Saudiya Ta Yi Allawadai Da Kissan Kiyashin Da HKI Take Yi A Gaza A Gaban Kutun ICJ
  • ‘Yansanda Sun Kama Masu Garkuwa da Mutane 12 Da Masu Sayar da Makamai 3 A Taraba Da Kaduna
  • An ɗaure ’yar shekara 80 a kurkuku saboda dukan jikarta da silifas
  • Dalilin da manyan ’yan siyasa ke barin NNPP — APC
  •  Manyan Malaman Roman Katolika Sun Fara Taron Zabar Paparoma
  • Za a rataye wani soja saboda laifin kashe budurwarsa
  • Ƴansanda Sun Kama Ƴan Daba 33 A Kano
  • Dukan farar hula saboda sanya kayan sojoji kuskure ne — Janar Chibuisi