A ranar Talata ne, Allah ya yi wa Alhaji Abbas Sanusi, Galadiman Kano kuma babban mai nada sarki a masarautar Kano rasuwa. A safiyar Laraba, 2 ga watan Afrilun 2025 aka yi jana’izar sarkin wanda ya shafe fiye da shekaru 60 yana hidimtawa masarauta, ya rasu yana da shekara 92 bayan doguwar jinya. Ya bar ‘ya’ya da jikoki da dama.
Mu Leka Shirin “Bunkasa Tagomashin Kirkirarriyar Basira Ta AI” Na Kasar Sin Tinubu Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Galadiman Kano, Abbas
Sanusi Daga cikin ‘ya’yansa akwai Alhaji Abdullahi Abbas, shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano. Kano, jiha ce da hamayyar siyasa da rikicin masarauta ya dabaibaye ta. Akwai hamayyar siyasa tsakanin shugabannin jam’iyyun NNPP mai mulki a jihar da takwararta ta APC wacce Abdullahi Abbas kuma ɗa ga Galadima ke shugabanta a jihar.

A ɓangaren Masarauta, Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya tumɓuke Sarki Aminu Ado Bayero inda ya maye gurbinsa da Sarki Sanusi II, wanda yanzu haka suke gaban kotu. Jana’izar Galadima da aka yi a fadar Kano, kofar kudu, ta hada kawunan duka bangarorin da ke hamayya da juna a jihar. Jiga-jigan Jam’iyyar NNPP a jihar da suka hada da shugabanta na Kasa, Engr. Rabiu Musa Kwankwaso, gwamna Abba Kabir Yusuf da sauransu duk sun halarci jana’izar yayin da a ɓangaren APC, Akwai shugaban jam’iyyar, Abdullahi Abbas, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin da sauransu. Sai dai, Sarki Aminu Ado Bayero bai samu halartar jana’izar ba duba da yanayin tsaro.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp
উৎস: Leadership News Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna
Wannan mataki ne awanni kaɗan bayan ɓangaren Damagum ya dakatar da Anyanwu da wasu mutane uku, lamarin da ya ƙara ta’azzaea rikicin shugabanci a cikin jam’iyyar PDP.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA
Manyan Labarai Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami
November 1,
2025 
Manyan Labarai Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 20, Sun Ceto Mutane 17 Da Aka Yi Garkuwa Da Su November 1, 2025

Manyan Labarai Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Martani Kan Iƙirarin Trump Na Kisan Ƙare Dangi Ga Kiristoci November 1, 2025