Isra’ila na karbe yankuna a zirin Gaza
Published: 2nd, April 2025 GMT
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa sojojin kasar na karbe iko da wasu yankunan zirin Gaza, a wani mataki na kara matsin lamba kan kungiyar Hamas domin tilasta ta sakin mutanen da ta ke garkuwa da su.
“Muna karbe zirin Gaza tare da kara matsin lamba mataki-mataki domin tilasta su mayar da mutanen da aka yi garkuwa da su,”inji Netanyahu a wani faifan bidiyo da ofishinsa ya fitar.
Ya kara da cewa, Sojoji na karbe yankuna, suna kai farmaki kan ‘yan wadanda ya danganta da ‘yan ta’adda in ji shi, yana mai sanar da samar da wata sabuwar hanya karkashin ikon Isra’ila don raba garuruwan Khan Younis da Rafah (kudu).
Tunda farko dama ministan tsaron Isra’ila Israel Katz ya sanar a Larabar nan cewa, kasarsa ta fadada kaddamar da hare-haren soji a sassan zirin Gaza, yana mai barazanar dakarun Isra’ila za su kwace karin yankuna a zirin da nufin samar da yankuna masu tsaro da za su raba Isra’ila da wurare masu fama da tashin hankali.
Cikin wata sanarwa, mista Katz ya ce matakin fadada ayyukan sojin zai kunshi fadada kwashe mutane daga yankunan da ake dauki ba dadi a Gaza.
Isra’ila dai ta kawo karshen wa’adin tsagaita wuta na watanni 2 tun a ranar 18 ga watan Maris da ya shude, inda ta koma kaddamar da munanan hare-hare ta sama da kasa kan wuraren da Falasdinawa ke fakewa.
A jiya Talata, hukumomin lafiya a Gaza sun ce kawo yanzu sabbin hare-haren sun sabbaba rasuwar Falasdinawa 1,042 tare da jikkata wasu 2,542, yayin da rikicin da ya barke tun daga watan Oktoban shekarar 2023 zuwa yanzu, ya haddasa jimillar asarar rayukan Falasdinawa 50,399, tare da jikkata wasu 114,583.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Ci Gaba Da Killace Gaza Da Kashe Mutane, Laifi Ne Da Ba A Taba Yin Irinsa Ba
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Ci gaba da killace Gaza da kuma kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, laifi ne da ba a taba yin irinsa ba a tarihin dan Adam
A wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Masar Badar Abdel Ati a yammacin jiya Lahadin da ta gabata, Araqchi ya bayyana ci gaba da killace yankin Gaza da rashin abinci da magunguna, tare da kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, a matsayin wani laifi da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin dan Adam. Ya dauki Amurka da sauran masu goyon bayan ‘yan sahayoniyya a matsayin masu hannu a kisan kiyashi da laifukan yaki da ake aikatawa a Gaza.
Ministan harkokin wajen na Iran ya jaddada wajibcin tunkarar muggan manufofin yahudawan sahayoniyya na tilastawa al’ummar Gaza da yammacin kogin Jordan yin hijira daga muhallinsu, yana mai bayyana halin ko in kula da kasashen duniya suke nun awa kan wadannan laifuka a matsayin abin mamaki da damuwa.
Araghchi ya kuma yi wa takwaransa na Masar bayani kan ci gaban tattaunawar Iran da Amurka kan Shirin makamashin nukiliya na zaman lafiya da ake takaddama a kai tsawon shekaru.