Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-07-29@02:41:50 GMT

Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadiyar Mutuwar Mutane Da Dama A Yola

Published: 28th, July 2025 GMT

Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadiyar Mutuwar Mutane Da Dama A Yola

Ruwan sama mai ƙarfn gaske ya haddasa mummunar ambaliya a Yola ta Kudu, Jihar Adamawa, inda mutane da dama suka mutu, yayin da wasu da dama suka rasa matsugunnansu.

Yankunan da ambaliyar ta fi shafa sun hada da Shagari, Sabon Pegi da Anguwan Tabo.

Ayyukan ceto suna ci gaba da gudana, inda Sojoji da hukumomin agaji ke kwashe mazauna yankunan da abin ya shafa.

Hukumomi sun shawarci mazauna yankunan da ke fuskantar barazanar ambaliya da su gaggauta barin wuraren, kasancewar ana hasashen karin ruwan sama.

 

RN

 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Adamawa Ambaliya

এছাড়াও পড়ুন:

Mutane 6 Ne Suka Yi Shahada Sanadiyyar Hare-haren Yan Ta’adda A Zahidan

Wasu yan bindiga wadanda ake dangantasu da kungiyar Jaishul-Zulum sun dauki alhakin kai hare-hare a cikin wata kotu a  birnin Zahidan babban birnin lardin Sistab Baluchistan a yau Asabar.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa yan ta’addan sun shigo da motarsu har zuwa a wata kotu a garin da Zahidan, sannan suka sauka suna son shiga kotun amma jami’an tsaro a kotun suka hanasu shiga. Daga nan kawai suka fara jefa nakiya irin da yaki a kansu.

An yi ta musayar wuta tsakaninsu da jami’an tsaro zuwa wani lokacin suka sami nasarar halakasu. Amma kuma sun kai mutane 6 ga shahada uku daga cikinsu jami’an tsaron kotun da kuma wani yaru da kuma wata mata yar kabilar Baluch wacce har yanzun ba’a ganeta ba.

Kungiyar yan ta’adda ta jaishul Zulum wacce take da cibiya a cikin yankin Baluchistan na kasar Pakisatan dai ta sha daukan alhakin kai hare-hare a yankin Sistan Baluchistan na kasar Iran. Tare da kashe Jami’an tsaro da kuma fararen hula, da kuma kawo hargitsi tsakanin mabiya mazhabobin musulunci daban –daban da kuma kabilu.

Mutane da dama sun ji rauni bayan wadanda suka yi shahada. Sannan mafi yawa an yi masu magani a asbitoci kuma an sallamesu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ambaliyar Ruwa: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Ya Ƙaru Zuwa 23 A Jihar Adamawa
  • Mutanen Sweida Na Kasar Siriya Suna Fama da Rashin Abinci da Ruwa
  • Kungiyar Gwamnonin Jihohi Ta Jajintawa Jihar Adamawa Bisa Ambaliyar Ruwa A Yola
  • Harin Ta’addanci A Wani Coci Ya Lashe Rayukan Mutane Fiye Da 21 A Gabashin Kongo
  • Ambaliya ta yi ajalin mutane, ta lalata gidaje a Adamawa
  • Yadda Ake Faten Acca
  • Mutane 6 Ne Suka Yi Shahada Sanadiyyar Hare-haren Yan Ta’adda A Zahidan
  • HOTUNA: Shugaban Gambiya ya kai wa iyalan Buhari ziyarar ta’aziyya a Daura
  • ‘Yan Jarida Da Suka yi Shahada A Gaza Sun Kai 232, Yayin Da Wadanda Suka Rasa Rayukansu Sakamakon Yunwa Suka Kai 122