Shugaban Kasar Masar Ya Roki Trump Ya Kawo Karshen Yaki A Gaza
Published: 28th, July 2025 GMT
Shugaban kasar Masar Abdulfattah Assisi ya bukaci shuggaban kasar Amurka Donal Trump ya taiama ya kawo karshen yaki a Gaza, ya kuma kawo karshen walar da Falasdinawa suke ciki.
Jaridar The Nation ta kasar Amurka ta nakalto shugaba Sisi yana fadar haka a wani jawabinda ya gabatar a yau Litinin, inda yayi alkawaliwa mutanen kasar masar kan cewa masar bazata taba kyale mutanen Gaza a halin da suke ciki ba har abada.
Ya ce: Gwamnatin kasar Masar tana daga cikin kasashen da suka tsaya don ganin an kawo karshen wannan yakin, tare da Amurkan da kuma kasar Qatar don tabbatar da cewa an kawo karshen yakin . Shugaban daga karshe ya gabatar da shawarar samar da kasashe biyu a matsayin hanya tilo ta samar da zaman lafiya a kasar Falasdinu. Ya kuma bayyana rashin amincewar shirin tilastawa Falasdinwa barin kasarsu.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kawo karshen
এছাড়াও পড়ুন:
IRGC Ta Ja Kunnen Kasashen Turai Dangane Da Taimakon Da Suke Bawa HKI
Janar majid Khatami Shugaban Bangaren Leken Asiri Na dakarun IRGC masu kare juyin juya halin musulunci ya bayyana cewa, rundunarsa tana sa ido akan take –taken kasashen Turai dangane da ayyukan sharrin da HKI take gudanarwa a yankin. Ya kuma kara da cewa rundunarsa tana da hanyoyin wadanda zata yi amfani da su , wanda daga karshe turawan ne zasu cutu a goyon bayan da suke bawa HKI.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim ya nakalto Janar Majid Khatami yana fadar haka a lokacinda yake jawabi a taron addu’a da girmama Ghulam Hussan Ghaiba a nan Tehran. Dangane da marigayin ya bayyana cewa ya kasance cikin wadanda suka je yakin kare kasa na shekaru 8, kuma a cutu da makaman guban da sadam ya jefa a yakin don haka tun lokacin yake fama da matsalolin rashin lafiya har zuwa lokacin da bar duniya a cikin yan kwanakin da suka gabata.