Amurka Ta Dakatar Da Bai Wa ‘Yan Kasar Nijar Bisa Shiga Cikin Kasarta
Published: 28th, July 2025 GMT
Kasar Amurka ta sanar da dakatar da bai wa mutanen Nijar bisa ta shiga cikin kasarta har illa masha Allahu.
Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka ne ya tabbatar da cewa an dakatar da bayar da bisa din ga ‘yan kasar Nijar da suke son shiga cikin kasar, saboda abinda ya kira matsala da ake da ita da gwamnatin Nijar, ba tare da yin Karin bayani ba.
Sai dai kuma sanarwar ta yi togiya akan jami’an diflomasiyya da sauran jami’an gwamanti,kamar yadda wani sako na diplomasiyya ya nuna a ranar 25 ga watan Yuli.
Wannan matakin na Amurka ya biyo byan rashin jituwar da ake da shi a tsakanin gwamatin Amurka da gwamnatin Jamhuriyar Nijar. A watan Satumba da ya shude ne dai Amurka ta kammala dauke sojojinta daga kasar Nijar bayan da gwamnatin sojan kasar ta umarce su, su fice daga kasar.
Da akwai sojojin Amurka da sun kai 1000 a cikin jamhuriyar Nijar, da janye su yake a matsayin kwankwasar kan Amurka da rage tasirinta a yammacin Afirka.
Gabanin juyin mulkin da aka yi a kasar dai Amurka tana amfani da wannan cibiyar a abinda take kira fada da ta’addaci a yammacin Afirka. Sai dai kuma hakan bai hana ci gaba da yaduwar ayyukan ta’addanci a cikin kasashen na yammacin Afirka ba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jigawa Za Ta Kashe Naira Biliyan 3.5 Wajen Gina Shaguna A Farm Centre
Gwamnatin Jihar Jigawa ta fara aikin gina shaguna guda dubu daya a cibiyar kasuwanci ta Farm Centre da ke Kano, wanda zai lakume kudi Naira Biliyan Uku da rabi (N3.5bn), domin bunkasa kudaden shiga na cikin gida na jihar.
Shugaban Kungiyar Hadaka kan Tsaro, Zaman Lafiya da Warware Rikice-rikice a Jihar Jigawa, Muhammad Musbahu Basirka, ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a sakatariyar NUJ da ke Dutse, babban birnin jihar.
Ya bayyana cewa, hukumar EFCC ce ta mika filin hannun gwamnatin jihar Jigawa a matsayin wani bangare na dawo da kadarorin da jihar ta gada daga tsohuwar jihar Kano.
Ya ce: “Wannan fili da ke a tsakiyar birnin Kano, na daga cikin kadarorin da jihar Jigawa ta gada bisa tsarin raba kadarori da filaye da aka yi bayan kirkar jihar Jigawa daga tsohuwar jihar Kano a watan Agustan 1991.”
“Bayan tattaunawa da masana, shugabannin al’umma da kuma masu ruwa da tsaki, muna sanar da jama’ar jihar Jigawa cewa gwamnatinmu ta yanke shawarar amfani da wannan fili mai muhimmanci domin amfanar kowa da kowa.”
“Manufar ita ce kara habaka kudaden shiga na cikin gida na jihar, kasancewar filin na dag cikin muhimman wuraren kasuwanci na Kano. Gwamnatinmu na fuskantar bukatar fadada hanyoyin samun kudaden shiga ba tare da dogaro kacokan ga kasafin kudi na kasa”.
Yayin da ya ke kira ga ‘yan asalin jihar da sauran mazauna da su rungumi wannan cigaba da fahimta da hadin kai, Musbahu Basirka ya ja hankalin jama’a da a guji siyasantar da wannan lamarin.
“Duk da haka muna maraba da shawarwari masu amfani kan hanyoyin da za a fi amfana da wannan aiki mai matukar muhimmanci domin dorewar ci gaba ga al’umma.” In ji shi.
“Mu a matsayinmu na wakilan kungiyoyin fararen hula, za mu kasance cikin tsaka-tsaki wajen sa ido da tabbatar da cewa an yi aiki mai inganci, tare da yin nazari lokaci-lokaci domin tabbatar da gaskiya da adalci ” in ji Basirka.
Usman Muhammad Zaria