Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan Almujtaba 121
Published: 28th, July 2025 GMT
121- Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da haka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin da suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtadha Muttahhari, ko kuma cikin littafin mathnawa na maulana Jalaluddeen Rum ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.
////… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata a kuma cikin sarir Imam Al-Hassan Almujtaba (a) diyar Fatima (s) kuma jikan manzon All..(s) na farko , mun tsaya inda muka bayyana yadda Talha da Zubair suka nemi izinin Amirulmuminina (a) na zuwa umra, amma ya basu izini duk da cewa ya san ba umra zasu je ba, sai dai ya bukacesu sun yi ranstuwa su kuma sake yi masa bai’a kafin su fita. Sun yi hakan amma kuma, kamar yadda ake zata suna neman hanyar yi masa tawaye ne, don abinda suka yi Kenan bayan da suka fita madina.
Sannan mun yi maganar ummilmuminina Aisha matar manzon All..(s), wacce ta je aikin hajji a shekarar, ta bar madina a lokacinda yan tawaye suka yiwa gidan Khalifa kawanya. Don haka da ta kare aikin hajji ta kama hanyar zuwa madina, amma da ta isa wani wuri a wajen Makka ta ji labarin cewa Aliyu dan Abitalib (a) shi ne aka yiwa Bai’a. Sai ta yi bakin ciki, sannan a lokaci guda tace sai ta nemi jinin Khalifa Uthman daga Imam Ali (a). mun yadda ta kawo hujjojinta na yin haka, amma gaba daya sun sabawa hankali sun sabawa shari’a, wanda zai sa ta yake shi.
Mun yi magana kan yadda take rayuwa da manzon All..(s) tana ginin yadda yake gairma iyalan gidansa gudu hudu Aliyu da Fatimah da kuma yayansu alhassan da Al-hussain(a).
Tana son manzun All..(s) ya sota kamar yadda yake son wadannan mutane 4 amma bata samu ba, sai ta fara hasada da su. Duk tare da matsayinsu a wajen All.. da ta sha ji a wajen manzon All..(s).
Don haka kiyayyar ne ya sa ta ce dage sai ta yake shi duk da cewa mata da hujjar yan hakan. Munji yadda malamai da dama suka kawo hujjojin da suka sa ta yake shi.
Daga karshe mung a cewa a sharia ma, idan an kashe wani mutum, danginsa ne , musamman yayansa ne suke da hakkin neman jininsa daga wadanda suka kashe shi. Idan har babu su, to shugaban muminai wanda shi ne Aliyu, dan Abitali (a).
Sannan mun fara bayyana cewa matan manzon All..(s) dangane da yakar da Aisha ta yiwa Aliyu dan Abitalib (a) sun rarraba, wasunsu suna tare da Aliyu dan Abitalib (a), kuma Ummu salma ce take jagorantarsu, wasu kuma karkashin Aisha suna goyon bayan yakarsa.
Mun bayyana cewa Aisha bata fito yaki da Aliyu dan Abutalib don neman jinin Khalifa Uthman ba, sai dai ta fake da neman jinin Uthman en don yakarsa da kuma fidda khalifanci daga hannunsa.
Ummil muminina Aish ce ta fara shelanta yaki a kan gwamnatin Amirul muminina (a) a makka, a lokacinda tayi doguwar akhuduba, tana bayyana abinda ya faru da kuma yadda aka kashe Khalifa Uthman. A cikin khudubarta ta tabbatar da cewa Khalifa Uthman yayi kura kurai, sannan manya manyan sahabban manzon All..sun aibata shi.
Kafin mu je, gama, yakamata mu sani daga cikin wadanta suka aibata shi har da ita Aisha ummil muminina, har an jita da dama tana fada, ku kashe Nathaly a kafirta, tana nufin Uthma, sannan ta yi maganar cewa an bukace shi ya tuba. Wannan gaskiya ce, amma malaman tarihi sun bayyana cewa, bayan ya tuba, yan tawaye daga kasar masar sun kama hanya, sai ya zo cikin masala ci ya ce bai tuba ba zai ci gaba da abinda yake kai. Sai labara ya kaiwa yan tawaye, suka sake dawowa sannan suka ce ya sauka kawai daga kan kujerar khalifanci, ya ce ba zai sauka ba, ba abinda ya rage masu sai yakarsa da kuma kashe shi.
Amma batun cewa, ya tuba sannan suka kashe shi ba haka bane. Ya tuba ne sannan ya kwance tubarsa. A nan ne suka bashi zabi ko ya sauka ko su kashe shi. Sai ya zabi na biyun. Sannan kisansu bai da alaka da Amirulmuminina, (a), gaskiya ne ya yi masa nisaha ya kuma aibata shi kamar yadda sauran sahabban suka yi, amma ba wana ya taba jinshi yana cewa ku kashe uthman.
Wannan duk yana faruwa ne a makka, bayan aikin hajji, inda matan manzon All..(s) da dama suka fito zuwa aikin hajji na wancan shekara , shekara ta 35 bayan hijiran manzon All..(s).
Don haka bayan khudubarta a cikin jama’a , Aisha ta kira sauran matan manzon All..(s) zuwa yakar wasiyyin manzon All..(s) wato Aliyu dan Abitalib (a), kofar ilminsa, baban jikokin manzon All..(s) Al-Hassan da Alhussain.
Don haka ta hadu da ummu salma ® tana kiranta zuwa yakar Aliyu (a) tana cewa: ya ke yar abu Umayya, ke ce farkon wadanda suka yi hijira daga cikin matan manzon All..(s) kuma, kece babban a cikin iyayen muminai, manzon All..(s) yana raba mana a dakinki, sannan mala’ika jibrilu ya fi sauka a dakin ki. …
Sai umma salma ta cewa, mata, na rantse da All..menene kike bukata da dukkan wadannan maganganun? Sai Aisha ta fito fila ta fada mata abinda take so, sai tace: Mutanen nan sun bukaci Uthman ya tuba, a lokacinda ya tuba sai suka kasheshi yana azumi, a cikin wata mai alfarma (zulhajji). Na yi niyya zan fita zuwa Basra, sannan Talha da zubair suna tare da ni, ki fita tare da mu, mai yuwa All..ya kyautata wannan al-amarin a hannummu.
Daga nan sai Ummu Salma ta fara karyatata, da kuma yi mata nasiha da kuma shiryatar da ita, inda take cewa: Kin kasance a jiya din na kina zuga mutane a kan Uthman, kina fadar mafi munin kalmomi a kansa, sunansa a wajenki shi Nathal, Sannan kin san matsayin Aliyu dan Abitalib (a) a wajen manzon All..(a), ba zan yi maki nasiha ba?
Sai Aisha ta ce, ee.
Shin zaki tuna wata rana, ya zo (Aliyu) muna tare da shi (s), — har zuwa inda take cewa—sai ya kebe da Aliyu yana tattaunawa da shi, sun dade, sai kina son ki fada masu, sai nah ana ki, sai kin saba mani, kika fada masu, ba’a dade ba sai kika dawo kina kukax, sai na ce maki, me ya same ki? Sai kika ce na zo masu suna tattaunawa, sai na fadawa Aliyu(a), kwana guda ne kawai nake da shi a wajen manzon All..(a) a cikin ko wani kwanaki 9, shin ba zaka barni da kwanana ba ya dan Abiyalib ?.
Sai manzon All..(s) ya juya gareni fuskansa ta yi ja yana fushi, ki koma baya, na rantse da All..ba wanda za iyi da Aliyu sai wanda sai wanda bai da Imani. Sai na dawo ina nadawa.
Sai Aisha ta ce, ee na tuna!
Sai tace: in kara tunatar da ke?
Sai tace : ee!
Sai tace: wata rana ina zaune ni da ke tare da manzon All…(a) sai yace mana: Wacece daga cikinku, wacce zata hau wata rakuma mai yawan gashi, kuma karnukan Haw’aba zasu yi mata haushi, sai ta kasance ta karkata daga barin hanyar gaskiya?
Sai muka ce gaba daya: muna neman tsarin All..da manzonsa da kasancewa haka. Sai ya taba bayanki sannan yake: ina gargadinki kada ki kasance, kice ya ke Humaira.
Sai Aisha tace na tuna.
Sai Ummu Salam ta kara cewa: in kara tunatar da ke? Sai tace: ee.
Sai tace: wata rana ni da ke muna zaune tare da manzon All..(s) a wata tafiyarsa. Aliyu (a) ya kasance shi ne yake kula da takalman manzon All..(s) da kuma wanke kayansa, sai ya zo ya dauki takalman manzon All..(s) ya na gyaransa a karkashin inuwar itaciyar Samara.
Daga nan sai babanki ya zo tare da Umar sai suka nemi shiga wajensa, sai muka tashi muka je wajen Hijabi. Suka shiga suna yi Magana da shi kan abinda suka ga dama, sannan suka cewa masa: Ya manzon All..bamu san zuwa yauce ne zaka kasance tare da mu ba, da ka fada mana waye zaka Sanya khalifanka a bayanka don mu sanda zamu fake da shi a bayanka.
?
Sai yace masau: Amma ni ina ganinsa, da kuma na nuna maku shi da kun waste kun bar shi, kamar yadda banu Isra’ila suka watse suka bar Haruna dan Imrana., sai suka yi shiru. Sannan suka fita.
A lokacinda suka fita, sai muka fito zuwa wajen manzon All..(s). sai ke kika fara masa Magana, kika ce: Ya manzon All..(s) wa zaka Sanya khalifa a kansu bayanka. Sai yace: wanda yake gyaran takalma. Sai duk muka fita waje sai muka ga Aliyu yana gyran takalma.
Sai kika ce ya manzon All..bamu ga wani ba sai Aliyu.? Sai ya ce: shi ne.
Sai tace na tuna.
Sai ummu salma tace: bayan wannan wani fitowa kuma zaki yi bayan wannan?
Sai Aisha tace: Ni ina fita ne don gyara a cikin mutane. Kuma ina fatan samun lada daga All.. Sai Ummu salma tace, ki tafi da ra’ayinki.
Sai Ummu salma ta juya ta tafi ta kama hanyar Madina, sannan ta rubutawa Amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a) wasika inda ta fada masa abinda Aisha take shirin aiwatarwa.
Wasu malaman tarihi sun bayyana cewa Ummu Salma (a) ta aiki danta Umar dan Abu salama danta daga mijinta na farko wato Abusalma, ta aike shi wajen Imam (a) tare da wasikar sannan ta fadawa Imam (a) kan cewa: Ga dana Umar wanda shi yake kula da ni, ya kasance cikin mataimakanka kan miyanka.
Wannan ya faru ne bayan da ta gabatar da nasihohi kamar yadda ka ji. Amma Aisha ta yi gabanta, tana son yakar Amirul muminina (a).
Dana nan sai Aisha ta bada umurni a yi shela a cikin Makka kan cewa da ita da \zubai da Talha zasu fita daga Makka zuwa Basra, duk wanda yake son binta kuma bai da abin hawa da kuma guzuri za’a bashi.
Daga nan sai ta hau rakuminta, wanda ake kira Askar, banu Umayya da sauran masu kwadayin duniya, suna bayanta. Haka ma tsofin gwamnonin Khalifa Uthman suna tare da ira suka kama hanyar Basra daga Makka.
Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu nay au sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu. Wassalamu alaikum.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: a wajen manzon All masu sauraro bayyana cewa kamar yadda
এছাড়াও পড়ুন:
Amurka Ta Dakatar Da Bai Wa ‘Yan Kasar Nijar Bisa Shiga Cikin Kasarta
Kasar Amurka ta sanar da dakatar da bai wa mutanen Nijar bisa ta shiga cikin kasarta har illa masha Allahu.
Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka ne ya tabbatar da cewa an dakatar da bayar da bisa din ga ‘yan kasar Nijar da suke son shiga cikin kasar, saboda abinda ya kira matsala da ake da ita da gwamnatin Nijar, ba tare da yin Karin bayani ba.
Sai dai kuma sanarwar ta yi togiya akan jami’an diflomasiyya da sauran jami’an gwamanti,kamar yadda wani sako na diplomasiyya ya nuna a ranar 25 ga watan Yuli.
Wannan matakin na Amurka ya biyo byan rashin jituwar da ake da shi a tsakanin gwamatin Amurka da gwamnatin Jamhuriyar Nijar. A watan Satumba da ya shude ne dai Amurka ta kammala dauke sojojinta daga kasar Nijar bayan da gwamnatin sojan kasar ta umarce su, su fice daga kasar.
Da akwai sojojin Amurka da sun kai 1000 a cikin jamhuriyar Nijar, da janye su yake a matsayin kwankwasar kan Amurka da rage tasirinta a yammacin Afirka.
Gabanin juyin mulkin da aka yi a kasar dai Amurka tana amfani da wannan cibiyar a abinda take kira fada da ta’addaci a yammacin Afirka. Sai dai kuma hakan bai hana ci gaba da yaduwar ayyukan ta’addanci a cikin kasashen na yammacin Afirka ba.