Aminiya:
2025-08-07@23:07:01 GMT

Mahaifin Ɗan Bello ya rasu

Published: 8th, August 2025 GMT

Fitaccen matashin nan mai barkwanci, Bello Habib Galadanci, wanda aka fi sani da Ɗan Bello, ya yi rashin mahaifinsa a yammacin wannan Alhamis din.

Matashin lauyan nan ɗan gwagwarmaya, Abba Hikima, ne ya bayyana hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Abba ya yi alhinin hadiminsa da ’yan daba suka kashe a Kano NAHCON ta ƙayyade N8.

5m kafin alƙalami na kujerar Hajjin 2026

“Innalillahi wa inna IlaiHi rajiun. Allah Ya yi wa Mahaifin Dokta Bello Galadanchi (Dan Bello) rasuwa yanzun nan. Allah Ya gafarta masa. Ameen,” a cewar saƙon da Abba Hikima ya wallafa.

Kawo yanzu dai ba a bayyana dalilin rasuwar mahaifin Ɗan Bellon ba, amma wasu kafofin watsa labarai sun ruwaito cewa marigayi ya rasu bayan fama da jinya.

Ɗan Bello ya kasance dan gwagwarmaya marar tsoro da ake ganin na daga cikin matasa da za su iya kawo sauyi a ƙasar nan.

Matashin ya sha ƙalubalantar gwamnatocin jihohi har ma da tarayya kan sakaci da walwalar al’ummar da suke jagoranta musamman a bangaren ilimi da kuma harkokin lafiya domin zaburar da su kan abin da ya kamata.

Aminiya ta ruwaito cewa, a bayan nan ne Hukumar Tsaron Farin Kaya DSS ta riƙe matashin na dan lokaci taƙaitacce yayin saukarsa a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano bayan shigowarsa ƙasar daga China.

Ɗan Bello dai ya yi ƙaurin suna wajen yin bidiyon barkwanci kan matsalolin shugabanci da cin hanci a Nijeriya.

A kwanan baya wasu saƙonni da ya wallafa kan matsalar fanshon ’yan sanda da ta matsalar albashin malaman jami’a sun ɗauki hankali matuƙa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ɗan Bello

এছাড়াও পড়ুন:

Kwamishina ya yi murabus kan ƙarbar belin dillalin ƙwayoyi a Kano

Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Ibrahim Ali Namadi, ya yi murabus daga muƙaminsa saboda ce-ce-ku-ce da ya biyo bayan karɓar belin wani wanda ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi da ya yi.

Namadi ya yi murabus ne sa’o’i kaɗan bayan da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi rahoton kwamitin bincike da ya kafa kan lamarin.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Namadi ya ce ya yanke shawarar yin murabus ne don “amfanin jama’a gaba daya” da kuma kare gwamnatin a “yaƙin da take yi da sayarwa da shan miyagun kwayoyi.”

Sai dai ya dage kan cewa ba shi da laifi, amma ya yarda cewa ra’ayin jama’a na da muhimmanci, kuma yana da kyau ya kare kimar gwamnatin.

Tuni Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi murabus ɗin tare da yi wa tsohon kwamishinan fatan alheri.

Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya ce Gwamnatin Jihar Kano na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da adalci da yaƙi da laifukan da suka shafi miyagun ƙwayoyi.

Gwamna Abba ya kuma jaddada muhimmancin dukkan jami’an gwamnati su riƙa yin taka-tsantsan da neman izini daga manyan hukumomi kan batutuwa masu mahimmanci na jama’a.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Abba ya yi alhinin hadiminsa da ’yan daba suka kashe a Kano
  • Gwamna ya yi wa iyalan ’yan wasan Kano da suka rasu a hatsari goma ta arziki
  • Ministocin Ghana biyu sun rasu a hatsarin jirgin sama
  • Ministan tsaron Ghana da wasu sun rasu a hatsarin jirgin sama
  • Malaman Jami’o’in Isra’ila Sun Nemi Jamus Ta Tilasta Dakatar Da Yakin Gaza
  • Bello Turji Bai Yi Sulhu Da Kowa Ba – Guyawa Isa
  • Matar Marigayi MKO Abiola, Ta Rasu Tana Da Shekaru 82
  • Kwamishina ya yi murabus kan ƙarbar belin dillalin ƙwayoyi a Kano
  • Shugaban ‘Yan Bindiga A Zamfara, Bello Turji, Ya Ajiye Makamai, Ya Saki Mutane 32