Dubban mutane sun yi zanga-zangar goyon bayan Falasɗinu a Isra’ila da Pakistan
Published: 10th, August 2025 GMT
Dubban mutane ne suka fito kan tituna a birnin Tel Aviv na Isra’ila ranar Asabar, domin yin kira da a kawo ƙarshen yaƙin Gaza, kwana guda bayan da gwamnatin Isra’ila ta lashi takobin faɗaɗa rikicin tare da ƙwace birnin Gaza.
Masu zanga-zangar da ke riƙe da hotunan waɗanda har yanzu ake garkuwa da su a yankin Falasdinawa sun yi kira ga gwamnati da ta tabbatar da sakin su ’yan uwansu.
’Yan jaridar AFP a wajen gangamin sun ƙiyasta adadin waɗanda suka halarci taron a matsayin dubbai, yayin da wata ƙungiya da ke wakiltar iyalan wadanda aka yi garkuwa da su ta ce mutane kusan 100,000 ne suka yi dafifi.
Hukumomin ƙasar ba su bada wasu alƙaluma mutane da suka shiga zanga-zangar ba, amma sun hakikance lalai ya, zarta duk wasu gangamin da aka yi a baya na adawa da yakin.
Masu zanga-zangar sun ƙarkare da aike wa Firaminista Benjamin Netanyahu saƙo da kakkausar murya.
Shahar Mor Zahiro, ɗaya daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da ɗan uwansa, ya shaida wa AFP cewar: “Idan ka mamaye sauran sassan Gaza kuma aka kashe sauran ’yan uwanmu da ake garkuwa da su, za mu bi ka har cikin harabar dandalin Square, ko a lokacin yakin neman zaɓe ko a kowane lokaci ko waje.”
A ranar Juma’ar da ta gabata, majalisar ministocin tsaron Netanyahu ta amince da gagarumin farmaki na kwace birnin Gaza, lamarin da ya janyo cece-kuce da tofin Allah tsine daga cikin gida da ƙasashen duniya.
Wasu ƙasashen ketare, ciki har da wasu kawayen Isra’ila, sun yi ta matsa kaimi don ganin an tsagaita wuta domin tabbatar da dawowar wadanda aka yi garkuwa da su da kuma taimakawa wajen rage matsalar jin kai a yankin.
Zanga-Zangar Goyon Bayan Falasɗinu a IstanbulDubban masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinu sun taru a Dandalin Beyazit na Istanbul a ranar Asabar bayan sallar Magariba, domin nuna adawarsu ga kisan kiyashi da ƙaƙaba yunwa da Isra’ila ke yi a Gaza.
Gangamin, wanda ya haɗa da ƙungiyoyin ba da gwamnati da kuma jama’a da dama, ya ci gaba da tafiya zuwa Masallaci mai tarihi na Ayasofya.
Mahalarta sun yi ƙoƙarin jan hankalin duniya game da matsalar jin kai da ke faruwa a Gaza, tare da nuna goyon baya gare su, yayin da tashin hankali da ƙarancin abinci da magunguna ke ƙara ta’azzara.
Masu shirya zanga-zangar sun yi kira ga al’ummar duniya da su ɗauki matakan gaggawa don kawo ƙarshen wahalhalun.
Isra’ila Na Fuskantar Matsin Lamba Daga DuniyaIsra’ila na fuskantar ƙarin fushin duniya saboda kisan kiyashi da take yi a Gaza, inda ta kashe fiye da mutane 61,000 tun watan Oktoba 2023.
Haren-haren da soja ke kaiwa sun lalata yankin sosai kuma sun haifar da mutuwa ta hanyar yunwa da ƙunci.
A watan Nuwamba da ya gabata, Kotun Hukunta Laifukan Yaƙi ta Duniya ta bayar da sammacin kama Firayiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da tsohon Ministan Tsaronsa Yoav Gallant saboda laifukan yaƙi da laifukan cin zarafin ɗan adam a Gaza.
Haka kuma, Isra’ila tana fuskantar shari’ar kisan kiyashi a Kotun Duniya saboda yaƙin da take yi a yankin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Isra ila garkuwa da su zanga zangar
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaba Xi Jinping Ya Gabatar Da Shawarwari Hudu A Taron Kolin Mata Na Duniya
Na farko, hada kai don samar da yanayi mai kyau ga ci gaban mata. Na biyu, a karfafa abubuwan da za su habaka ingancin ayyukan mata cikin hadin kai. Kana na uku, a gina tsarin kare hakkin mata tare. Sai na hudu, a bude sabon babin hadin gwiwa tsakanin mata a duniya.
Za a gudanar da taron kolin mata na duniya a yau da gobe Talata a birnin Beijing. Kuma tuni shugaban kasar Sin Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan, suka yi musafaha da shugabannin tawagogin kasashe, da kungiyoyin duniya da suka halarci taron, tare da daukar hotuna tare da su. (Amina Xu)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA