Sai An Magance Matsalar Asusun Haɗin Gwiwa, Za A Tabbatar Da Cin Gashin Kan Ƙananan Hukumomi
Published: 9th, August 2025 GMT
“Kuma za a yi hakan ne saboda a matsayinmu na al’umma, muna ci gaba da ƙoƙarin canza abubuwan da ‘yan siyasa ba sa son canzawa,” in ji shi.
Ya kuma bayyana cewa ba yau aka fara aikin gyaran kundin tsarin mulkin ƙasar kan batun cin gashin kan ƙananan hukumomi ba.
Ejah ya ƙara da cewa ana sa ran kashi biyu cikin uku na ‘yan majalisar wakilai za su kaɗa ƙuri’ar amincewa ko kuma ƙin amincewa da gyaran.
Ya ƙara da cewa gwamnatin Bola Tinubu ta bayar da umarnin ne kawai, biyo bayan hukuncin da kotun ƙoli ta yanke, cewa a biya kason kuɗaɗen da majalisun za su samu kai tsaye a asusunsu.
A cewarsa, wannan ba gyara ba ne, domin kuwa sai an zagaya jihohi 36 yadda al’umma za su mara masa baya kafin ya zama doka.
“Abin da muka yi shi ne yunƙurin zartarwa na ganin ƙananan hukumomi sun samu kuɗaɗensu kai tsaye amma hakan ba zai yi tasiri ba saboda tanade-tanaden hukuncin kotun ƙoli bai wuce tsarin mulki ba,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Kamfanoni Masu Jarin Waje Na Samun Kwarin Gwiwa Daga CIIE
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025 November 7, 2025
Daga Birnin Sin Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku November 7, 2025
Daga Birnin Sin An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka November 7, 2025