Tankokin mai sun yi bindiga a Zariya
Published: 11th, August 2025 GMT
Wasu manyan motocin dakon sun yi bindiga a yankin Ɗan Magaji da ke Ƙaramar Hukumar Zariya a Jihar Kaduna.
Ana fargabar mutuwar mutane da dama sakamakon gobarar tankokin man bayan sun yi hastari a safiyar Litinin.
Shaidu sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:30 na safe a kusa da Makarantar Rochas Foundation, kan titin Kaduna–Kano bypass daga Kwangila zuwa Dan Magaji.
Hatsarin ya haɗa da manyan motoci biyu masu ɗauke da man fetur da kuma motoci biyu ƙirar Golf ɗauke da fasinjoji.
A sakamakon haka, tankokin biyu suka yi bindiga, wanda ya tayar da wutar gobara mai ƙarfi tare da hayaƙi mai kauri ya lulluɓe hanyar.
Jami’an ceto da tsaro sun rufe hanyar, tare da gargaɗin direbobi da su guji bi ta wurin yayin da ake ci gaba da aikin ceto da dawo da gawarwaki.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan sanda sun kama masu laifi 34 a Kaduna
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta bayyana sabbin nasarorin da ta samu wajen yaƙi da laifuka a jihar, ta hanyar holen mutum 34 da ta kama da aikata laifuka daban-daban.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Rabi’u Muhammad, ya ce wannan ci gaba ya samu ne saboda sabbin dabarun aiki da kuma bayanan sirri da aka samu daga al’umma da hukumomin tsaro.
Jami’an tsaro sun ƙaddamar da shirin murƙushe ’yan bindiga a Kaduna Zulum ya ba kowanne ɗalibin Borno da ke karatu a Indiya tallafin N500,000A Anguwar Barnawa da wasu wurare a Kaduna, rundunar Operation Fushin Kada ta kama mutane 13 da ake zargi da aikata fashi da makami da satar wayoyi a otel-otel da gidaje.
An ruwaito sun taɓa kashe ɗan sanda a shekarar 2024, kuma suna samun bayanai daga dilolin miyagun ƙwayoyi a wuraren shaƙatawa. A
An ƙwato bindiga ƙirar gida, gatari da adduna 13, mota, kwamfuta huɗu, wayoyi 13 da talabijin huɗu.
Haka kuma, a Nunbu Bashayi da ke Sanga, an kama mutane bakwai da ake zargi da garkuwa da mutane tare da neman kuɗin fansa.
Dukkanimsu sun amsa laifinsu kuma ana neman ragowar waɗanda suke tsere.
A wani samame daban, ’yan sanda sun kama wasu mutane huɗu da ake zargi da aikata fashi, fyaɗe da damfara.
Sun saba kai hari gidajen mutane, ɗaukar kuɗaɗen mutane, aikata fyaɗe sannan su riƙa ɗaukar bidiyo tsoratar da mutane.
A Zariya kuwa, an kama wasu mutane tara da suka haɗa da maza da mata waɗanda ake zargi da yi wa direban Adaidaita sahu fashi ta hanyar zuba masa magani a abin sha.
Rundunar ta kuma kama wani likitan bogi mai suna Adamu Abubakar Muhammed wanda ya yi wa mutane tiyata ba tare da shaidar karatun likitanci ba.
Ya yi amfani da takardun bogi wajen yin aiki na tsawon wata guda kafin a gano shi.
Kwamishinan, ya ce duk waɗanda aka kama suna hannun rundunar, kuma za a gurfanar da su kotu bayan kammala bincike.
Ya gode wa jami’an tsaro da al’umma kan haɗin kai, inda ya yi da a ci gaba da bayar da sahihan bayanai domin inganta tsaro a jihar da ƙasa baki ɗaya.