Leadership News Hausa:
2025-08-08@11:53:24 GMT

Ziyarar Manzon Allah (SAW) A Madinah (1)

Published: 8th, August 2025 GMT

Ziyarar Manzon Allah (SAW) A Madinah (1)

Idan aka dubi wannan, bai kamata a riƙa ɓata karatu ana cewa Masallaci ne za a ziyarta amma ba Annabi (SAW) ba. Ya kamata a gyara karatu, a gyara wannan fahimtar. Saboda irin wannan fahimtar ce ta haifar da a zamanin nan an samu rashin girmama Manzon Allah (SAW) har aka dasa bom kusa da shi. Ko ɗaga murya Allah ya hana a yi a gaban Annabi (SAW), to ina ga tada bom?

A huɗubar sallar Idil Fiɗir da Limamin Makka ya yi a Harami, ya ce Yahudawa ne suka tada bom ɗin, amma sai ga shi da Saudiyya ta nuna wanda ya yi abin, da sunanshi da kamanninsa har da dogon gemu, ɗan ƙasar ne mai iƙirarin bin Salafiyya Sunnah.

Duk ire-iren karatuttukan nan ne na rashin ganin girman Annabi (SAW) suke jawo waɗannan bala’o’in. Ya kamata a ji tsoron Allah a gyara.

Malamai Malikawa sun yi hukuncin cewa zuwa ziyara a Madina wajibi ne ga wanda yake da hali. Ma’ana idan mutum ya yi Aikin Hajji, wajibi ne ya ziyarci Manzon Allah (SAW) idan yana da halin zuwa.

Masu cewa idan mutum ya yi Hajji shikenan ba sai ya tafi ziyarar ba, suna nuna alama ce ta ƙin Manzon Allah (SAW).

Hadisai masu yawa sun yi bayani a kan falalar ziyarar Manzon Allah (SAW).

Yana daga ciki, Abdullahi bin Umar (RA) ya ruwaito cewa, Manzon Allah (SAW) ya ce, “Duk wanda ya yi Hajji, sai ya ziyarci ƙabarina bayan mutuwata, ya zama kamar wanda ya ziyarce ni ne lokacin da nake da rai.” Ma’ana duk ɗaya suke.

Asƙalani, mai sharhin Bukhari ya ce zuwa Madina iri biyu ne, ana zuwa a lokacin da Manzon Allah (SAW) yake raye a kan ƙasa domin a karɓi shiriya, bayan wafatinsa kuma a je a ziyarci ƙabarinsa (SAW).

Dukkanin malamai na Allah Ahlus Sunnah tun daga kan Sahabbai a kan wannan fahimtar suke.

Haka nan, Hadisi ya tabbata daga Abdullahi bin Umar (RA) cewa, Manzon Allah (SAW) ya ce, “Duk wanda ya ziyarci ƙabarina, cetona ya cancanta a gare shi”. Abu Haraira (RA) ya ruwaito Hadisi daga Manzon Allah (SAW) ya ce, “Babu wani mutum da zai yi sallama a gare ni, face Allah ya dawo mun da raina har na amsa sallamar.”

Idan mutum zai je ziyarar, walau Alhaji ko wanda ba Alhaji ba, zai yi niyyar cewa zai je ya ziyarci Manzon Allah (SAW), sannan ya yi sallah a Masallacinsa, ya ziyarci sauran Sahabbai da wuraren Musulunci. Amma dai Annabi (SAW) ne a kan gaba.

Ana so idan mai ziyara ya tasam ma Madinar Annabi (SAW), ya yawaita salati ga Manzon Allah (SAW) domin ya ƙara samun haske da soyayyarsa (SAW).

Haka nan, ana so mutum ya yi wanka, ya sa turare, ya sa tufafinsa mafi kyau, kuma ya jaddada tubansa, sannan ya halarto da girman Annabi (SAW) a cikin zuciyarsa, da girman Sahabbansa, da ganin girman garin baki ɗaya (a matsayin wurin da Annabi (SAW) da Iyalansa da Sahabbansa suka rayu, da faruwar abubuwan tarihi na Musulunci. Lallai idan mutum ya yi haka, zai ji wani ƙarin imani har ya sa shi kuka.

Idan mai ziyara ya zo shiga Masallacin Annabi (SAW), ana so ya shiga da ƙafar dama ya ce “A’uzubillahil azim wa bi wajhihil karim wa sulɗanihil ƙadim minas shaiɗanir rajim, bismillah, allahumma salli ala Muhammadin wa alihi wa sallim, allahummagfirli zunubi waftahali abwaba rahmatika.”

Idan da hali ya yi ƙoƙari ya shiga Raula (wurin da Annabi ya ce Dausayin Aljanna ne) ya yi sallah nafila raka’a biyu a matsayin gaisuwar Masallaci. Idan kuma Raula ta cika, sai a yi sallar a duk wurin da aka samu a Masallacin.

Ana so idan mai ziyara ya tasam ma Madinar Annabi (SAW), ya yawaita salati ga Manzon Allah (SAW) domin ya ƙara samun haske da soyayyarsa (SAW).

Haka nan, ana so mutum ya yi wanka, ya sa turare, ya sa tufafinsa mafi kyau, kuma ya jaddada tubansa, sannan ya halarto da girman Annabi (SAW) a cikin zuciyarsa, da girman Sahabbansa, da ganin girman garin baki ɗaya (a matsayin wurin da Annabi (SAW) da Iyalansa da Sahabbansa suka rayu, da faruwar abubuwan tarihi na Musulunci. Lallai idan mutum ya yi haka, zai ji wani ƙarin imani har ya sa shi kuka.

Idan mai ziyara ya zo shiga Masallacin Annabi (SAW), ana so ya shiga da ƙafar dama ya ce “A’uzubillahil azim wa bi wajhihil karim wa sulɗanihil ƙadim minas shaiɗanir rajim, bismillah, allahumma salli ala Muhammadin wa alihi wa sallim, allahummagfirli zunubi waftahali abwaba rahmatika.”

Idan da hali ya yi ƙoƙari ya shiga Raula (wurin da Annabi ya ce Dausayin Aljanna ne) ya yi sallah nafila raka’a biyu a matsayin gaisuwar Masallaci. Idan kuma Raula ta cika, sai a yi sallar a duk wurin da aka samu a Masallacin.

Daga nan, idan lokacin ya kasance lokacin sallar farilla ne sai ya tsaya a kammala sallar, idan kuma ba lokacinta ne ba, yana idar da nafilar sai ya nufi ziyarar Annabi (SAW).

Idan ya zo wurin ƙabarin mai girma, sai ya baiwa alƙibla baya; ya fuskanci bangon ƙabarin kusa da inda hukuma ta amince a tsaya. Ya halarto da girman Annabi (SAW) tare da tunanin cewa ga fuskar Annabi (SAW) tana kallonsa. Sai ya yi sallama cikin ladabi na sarari da ɓoye, sannan ya yi salati ga Manzon Allah (SAW). Ma’ana ya ce”Assalamu alaika ya Rasulullah, assalamu alaika ya Nabiyyallah, assalamu alaika ya Khaira khalƙillah, assallamu alaika ya Habiballah, assalamu alaika ya Sayyidal Murasalin, assalamu alaika ya rasula Rabbul alamin, assalamu alaika ya ƙa’ida gurril muhajjalin. Ash’hadu an la’ilaha illallah wa ash’hadu annaka abduhu wa rasuluhu wa aminuhu wa khiratuhu Wa ash’hadu annaka ƙad ballagtar risalata wa addaital amanata wa nasahtal ummata wa jahada fillahi haƙƙa jihadihi.”

Sai mutum ya karanta ayar nan ta neman gafarar Allah a wurinsa (SAW) ta cikin Suratun Nisa’i. Idan ya samu hali sai ya ɗan ja baya kaɗan ya yi salati guda 70 ga Annabi (SAW).

Daga nan ya matsa daidai kamu ɗaya a dama, ya yi sallama ga Sayyidina Abubakar (RA), kuma ya ƙara matsawa irin haka duk dai a dama, ya yi sallama ga Sayyidina Umar (RA). Daga nan sai ya fice ya kammala ziyara.

Dangane da juya wa aklbla baya a kalli fuskar Annabi (SAW) lokacin da mutum zai yi addu’a, an ruwaito cewa Abu Ja’afarul Mansur Al-Abbas (Sarkin Musulmi) ya tambayi Imam Malik (RA) da ya zo ziyara cewa, “Shin Annabi (SAW) zan fuskanta in yi addu’a ko alƙibla?” Sai ya amsa ma sa da cewa “Don me za ka kawar da fuskarka ga Manzon Allah (SAW) alhali shi ne tsaninka kuma tsanin Babanka Adamu (AS) zuwa ga Allah?”. Saboda haka mai ziyara ya fuskanci Annabi (SAW) ya yi addu’a.

Amma da yake hukumar can ta yanzu ba su yarda a kalli Annabi (SAW) a yi addu’a ba, to sai mutum ya kalli Alƙibla sai ya halarto da shi (SAW) a zuciya. Kuma koda ma alƙiblar aka kalla dole sai an bi ta wurin Annabi saboda mutum zai yi salatinsa (SAW) a cikin addu’ar.

Akwai wasu da suke nuna wa Alhazai cewa ba koyaushe ne suka shiga Masallaci sai sun ziyarci Annabi (SAW) ba, suna kafa hujja da Hadisin da Annabi (SAW) ya ce “… kar ku sanya ƙabarina ya zamo wurin idi…”. A tasu fahimtar yin ziyararsa (SAW) koyaushe ya zama kamar Idi. To ba haka malamai suka fassara wannan Hadisin ba.

Ma’anar Hadisin in ji Malamai ita ce “kar a sanya ziyarar ƙabarin ta zama Idi wadda ba za a riƙa yi ba sai shekara-shekara.” Saboda dama Idi ba kullum ake yi ba, don haka Hadisin yana nufin kar a ƙi yin ziyarar har ya zama daga shekara sai shekara. Duk lokacin da aka samu iko a yi kawai.

Haka Malaman da ke da soyayyar Manzon Allah (SAW) a zuciyarsu suka fahimci Hadisin.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Idan mai ziyara ya assalamu alaika ya idan mai ziyara ya idan mutum ya yi ya halarto da

এছাড়াও পড়ুন:

Yawancin ‘Yan Siyasar Nijeriya Ba Su Da Tarbiyya – Sarki Sanusi II

“Su dai kawai abin da suke alfahari da shi, shi ne dukiya, yawan gidaje da jirage. Ba su san cewa mutane na kallonsu a matsayin ɓarayi ba.”

Sanusi II, ya ƙara da cewa ba shugaban ƙasa ko gwamna kaɗai ke da laifi ba, hatta shugabannin addini da sarakuna ma sun ɓaci a yanzu.

“Yawancin shugabanninmu sun shiga ruɗani, babu wanda ya tsira,” in ji shi.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu zai kashe tiriliyan 1.5 wajen gina layin dogo na zamani a birnin Kano
  • An kashe mutum huɗu da tayar da ƙauyuka 17 a Sakkwato
  • An kashe matafiya biyu da yin garkuwa da uku a Kwara
  • ‘Hayakin janareta’ ya kashe mutum 4 ’yan gida daya a Borno
  • Yawancin ‘Yan Siyasar Nijeriya Ba Su Da Tarbiyya – Sarki Sanusi II
  • Kasar Sin Ta Bayyana Adawa Da Ziyarar Boris Johnson A Taiwan
  • “Ku Yi Murabus Idan Baza Ku Iya Rike Amanar Jama’a ba” – Gargadin Gwamna Abba Ga Kwamishinoninsa
  • Sheikh Qassem: Tsaron Isra’ila zai ruguje cikin sa’a 1 idan ta shelanta yaki a kan Lebanon  
  • Ruftawar gini ta kashe uwa da ’ya’yanta 5 a Katsina