Isra’ila Ta Kashe ‘Yan jaridar Al Jazeera Biyar A Gaza
Published: 11th, August 2025 GMT
Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta kashe wani fitaccen dan jarida na kafar yada labarai ta Al Jazeera Anas al-Sharif tare da abokan aikinsa hudu a wani hari da ta kai Gaza.
Isra’ila ta zarge shi da kasancewa wani jagora na Hamas sannan ta ce ta hallaka shi saboda irin rahotannin da yake bayarwa masu tsanani daga arewacin Gaza.
Isra’ila ta hari ‘yan jaridar biyar – Anas al-Sharif wanda shi ne fitacce tare da Mohammed Qreiqeh masu aikawa da rahotanni ne sai kuma masu daukar musu hoto Ibrahim Zaher da Mohammed Noufal da kuma Moamen Aliwa wadanda dukkanin su suna aiki ne da kafar ta Al Jazeera.
A lokacin da Isra’ila ta kai musu harin ta sama suna cikin wani tanti ne na ‘yan jarida da ke wajen asibitin al-Shifa a birnin na Gaza.
Isra’ilar ta ce kisan hukunci ne na irin rahotannin da Anas din ya ke aika wa Al Jazeera da ke arewacin Gaza.
Baya haka Isra’ila ta kuma ce dan jaridar wani jigo ne na wani reshe na kungiyar Hamas da ke shirya hare-haren makaman roka da Hamas ke kai mata – zargin da Al Jazeera ta musanta.
A sanarwar da ta fitar rundunar sojin Isra’ilar ta zargi al-Sharif da fakewa a matsayin dan jarida- tana zarginsa da hannu wajen kai mata hare-hare da makaman roka kann fararen hula da sojojinta.
Ta ce a baya ta fitar da wasu bayanan sirri da ke tabbatar da alakarsa da ayyunakn soji na Hamas, ciki har da jerin horon ta’addanci da ya halarta.
Sanarwar ta kara da cewa kafin harin sojin na Isra’ila sun dauki matakai na kauce wa illata farar hulha.
Mako biyu da ya wuce Al Jazeera ta soki rundunar sojojin ta Isra’ila kan abin da ta kira kokarin tunzura masu aika mata da rahotanni a Gaza ciki har da al-Sharif.
Kungiyoyin kare hakkin dan’adam sun ce Isra’ila ta kashe ‚yan jarida sama da dari biyu (200) a Gaza tun daga watan Oktoba na 2023, kan abin da suka ce yunkuri ne na hana bayar da rahotannin zargin cin zarafin da Isra’ila ke yi a Gaza.
Isra’ila dai ta hana ‘yan jarida na waje aikawa da rahotanni a fili daga yankin.
Jim kadan bayan harin ne Isra’ila ta fitar da wata sanarwa da a ciki take tabbatar da kai harin da ta ce ta hallaka Anas al.-Sharif, tana mai cewa wani jagora ne a Hamas.
Rundunar sojin ta Isra’ila ba ta ambaci sauran ‘yan jaridar da ta kashe su tare ba.
Al-Sharif, mai shekara 28, yana rubuta sakonni ne ta shafin X, jim kadan kafin mutuwarsa – inda a ciki yake gargadi kan ruwan bama-bamai da Isra’ila ke yi a birnin na Gaza.
BBC ta ga wasu hotunan bidiyo masu tayar da hankali wadanda kuma ta tabbatar da sahihancinsu, na bayan harin da ya hallaka ‘yan jaridar, inda a ciki ake iya ganin mutane na dauke gawawwakin.
BBC/Hausa
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: yan jaridar Isra ila ta
এছাড়াও পড়ুন:
Tabarbarewar Tsaro na Barazana ga Siyasar Ƙasar Nan Gabanin Zaɓen 2027-Ado Doguwa
Daga Salihu Tsibiri
Tsohon shugaban masu rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya bayyana tabarbarewar tsaro da ake fuskanta, wato ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma hare-haren ’yan bindiga, a matsayin barazana ga siyasar ƙasar nan gabanin zaɓen 2027.
Ya yi wannan tsokacin ne a jawabinsa yayin bude zaman taron musamman na yini biyu da Majalisar Wakilai ta shirya kan halin tsaro da ƙasar ke ciki.
Alhassan Ado Doguwa, wanda ya yaba da ayyukan da hukumomin tsaro ke ci gaba da gudanarwa, ya ce halin da Arewa ke ciki abin takaici ne ƙwarai, la’akari da yawan mutanen da ke hannun masu garkuwa da kuma waɗanda ke rayuwa cikin tsananin rashin tabbas.
Tsohon shugaban ya jaddada cewa duk da cewa su ma gwamnoni suna da alhakin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a tare da gwamnatin tarayya, lokaci ya yi da za a duba batun tsaro a matsayin barazana da ba ta da alaƙa da jam’iyya, addini ko ƙabila.
Ya kara da cewa idan matsalar tsaro ta ci gaba da ta’azzara, akwai bukatar a rufe majalisa gaba ɗaya tare da ayyana dokar ta-baci, har sai an ɗauki matakin gaggawa don kare ƙasar daga halin da take ciki.
A nasa bangaren, shugaban kwamitin majalisar kan harkokin ’yan sanda, Makki Abubakar Yalleman, ya bayyana tsaro a matsayin alhakin kowa, inda ya yaba wa umarnin shugaban ƙasa na janye ’yan sanda daga wasu manyan mutane domin ƙara ƙarfi a yaki da laifuka a fadin ƙasar.
Sai dai Makki Yalleman ya yi kira da a samar da isasshen kuɗi da na’urorin zamani domin inganta ƙwarin gwiwa da ƙwarewar rundunar ’yan sandan Najeriya a yakin da take yi da ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma ’yan bindiga.
A nasa bangaren, shugaban marasa rinjaye na majalisar, Kingsley Chinda, ya danganta matsalolin tsaro da ake fuskanta ga gazawar bangarorin gwamnati uku wajen tabbatar da bin tanade-tanaden kundin tsarin mulki, musamman kan ta’addanci, garkuwa da mutane, ’yan bindiga da kuma masu yi wa gwamnati tawaye.