Aminiya:
2025-11-08@16:58:52 GMT

Tinubu ya yi alhinin rasuwar tsohon shugaban PDP, Audu Ogbeh

Published: 9th, August 2025 GMT

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga jama’a da Gwamnatin Jihar Binuwai bisa rasuwar Cif Audu Ogbe tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Cif Audu Ogbeh.

Ya kuma yi wa iyalansa, abokansa da dukkanin ’yan uwansa ta’aziyya kan rashin da suka yi.

Kotu ta ɗaure wata mata shekara 3 a kan damfara  Tsohon Ministan Noma Audu Ogbeh ya rasu

Cif Ogbeh, ya rasu yana da shekaru 78 a duniya, ya hidimta wa Najeriya a ɓangarori daban-daban ciki har da Ministan Sadarwa a lokacin Jamhuriya ta Biyu.

Sannan daga baya ya zama Ministan Noma a Gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari.

A cewar sanarwar Bayo Onanuga, mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labaru, Ogbeh mutum ne mai basira da zurfin tunani wanda ya taimaka wajen tsara manufofin gwamnati da magance manyan matsalolin ƙasa.

Ogbeh, ya fara harkar siyasa a shekarun 1970 a matsayin ɗan majalisa, sannan daga baya ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar APC.

Shugaba Tinubu, ya bayyana shi a matsayin “Ɗan ƙasa wanda hikimarsa, jajircewarsa, da ƙoƙarinsa na ci gaba suka bar tarihi a siyasar Najeriya.

“Kullum yana da hujjoji da alkaluma don kare ra’ayinsa. Ƙasa za ta yi matuƙar kewar gogewarsa.”

Shugaban ya yi addu’ar Allah Ya jiƙansa ya kuma bai wa iyalansa haƙuri da juriya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: rasuwa ta aziyya

এছাড়াও পড়ুন:

Matsalar Tsaro: Mun sami gagarumin ci gaba a shekaru biyu – Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta samu ci gaba sosai wajen magance matsalar rashin tsaro a faɗin ƙasar cikin shekaru biyu da suka gabata.

Shugaban ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa na daƙile ayyukan ta’addanci da kuma tabbatar da zaman lafiyar ƙasa.

Ɗan shekara 2 ya rasu bayan faɗawa rijiya a Kano An gano gawar wata mai shekara 96 a cikin masai

A wata sanarwa da Tinubu ya fitar a shafinsa na sada zumunta, a ranar Juma’a, ya ce ƙalubalen tsaro a Najeriya, da suka haɗa da ta’addanci da aikata laifuka, ana magance su da sabbin tsari da sauye-sauyen dabarun dawo da zaman lafiya a faɗin ƙasar.

“Haƙiƙa muna fuskantar ta’addanci – ƙalubalen da Najeriya ta fuskanta kusan shekaru ashirin, kuma ba za mu ja da baya ba, za mu yi nasara a kan ta’addanci kuma mu yi iƙirarin samun nasara a wannan yaƙin, ba za mu taɓa yin sulhu harkar tsaro ba.

“Najeriya ƙasa ɗaya ce mai haɗin kai, mun tashi tare, mun ci gaba tare, kuma mun ƙi yanke ƙauna domin tabbatar da ƙuduri.

“Aikin da ke gabanmu yana da yawa, amma duk da haka ƙudurinmu ya fi girma, za mu ci gaba da ɗorewa tare da inganta nasarorin da muka samu na sake fasalin ƙasa da kuma samar da ci gaba a Najeriya.

“Ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba kuma ba za mu bar wani abu ba a cikin aikinmu na kawar da masu aikata laifuka a cikin al’ummarmu, muna kira ga abokan haɗin gwiwarmu da su tsaya tsayin daka tare da mu yayin da muke ƙara faɗaɗa yaƙin da muke yi da ta’addanci, mun samu gagarumin ci gaba a cikin shekaru biyu da suka gabata, kuma za mu kawar da wannan barazana.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ta’aziyyar Rasuwar Jarumin Kannywood, Malam Nata’ala
  • An Fara Binciken Batan Dan Bautar Kasa A Bayelsa
  • An Damke Mutum 11 Da Ake Zargi Da Kisan Wani Matashi A Bauchi
  • Tinubu ya gana da Sarkin Musulmi a Aso Rock
  • Matsalar Tsaro: Mun samu gagarumin ci gaba a shekaru biyu – Tinubu
  • Matsalar Tsaro: Mun sami gagarumin ci gaba a shekaru biyu – Tinubu
  • An rantsar da shugaban Kamaru Paul Biya karo na 8
  • Majalisa Ta Ɗage Tantance Ministan Tinubu Saboda Rashin Rahoton Tsaro
  • Jirgin ƙasa ya murƙushe babur mai ƙafa uku a Jos
  • Majalisar Dattawa ta dakatar da tantance sabon Ministan Tinubu