Fashewar gurneti ya kashe yara uku a Borno
Published: 9th, August 2025 GMT
Fashewar gurneti ya salwantar da rayukan yara mata uku a garin Pulka da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza a Jihar Borno.
A wani rahoto da ma’aikacin Sibiliyan JTF Buba Yaga ya fitar, ya ce ɗaya daga cikin ƙananna yaran suna wasa da gurnetin da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne, suka yi watsi da su a lokacin da gurnetin ya tashi da misalin ƙarfe 2:20 na ranar Alhamis.
An garzaya da yaran zuwa Babban Asibitin Gwoza, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsu.
Daga nan ne aka miqa gawarsu ga iyalansu domin yi musu jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Yadda ma’aikatan gwamnati ke gina gidaje da kuɗin sata a Abuja Yadda ma’aikatan gwamnati ke gina gidaje da kuɗin sata a AbujaHaɗaɗɗiyar tawagar ’yan sandan da suke tantance bama-bamai (EOD-CBRN), da dakarun Operation Hadin Kai, CJTF, da mafarautan yankin sun ziyarci wurin, inda suka gudanar da aikin share wasu na’urori.
Ba a samu ƙarin ko ɗaya ba, kuma an ayyana yankin a matsayin keɓantaccen wurin da za a kauce wa bi zuwa wani lokaci.
Hukumomin tsaron sun bukaci mazauna yankin da su gaggauta kai rahoton abubuwan da suke zargi ga jami’an tsaro domin hana afkuwar irin wannan bala’i.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Boko Haram yara
এছাড়াও পড়ুন:
Mahara sun kashe ɗan sanda, sun ɗauke bindigarsa a Taraba
An kashe wani ɗan sanda mai muƙamin Sajan a wani hari da ’yan bindiga suka kai wani shingen bincike, inda suka ɗauke bindigarsa bayan sun halaka shi a Jihar Taraba.
Wata majiyar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10 na dare a garin Tella, cikin Ƙaramar Hukumar Gassol, lokacin da ’yan bindigar suka yi wa shingen binciken ƙwanton ɓauna.
An ce maharan sun harbi ɗan sandan ne a kansa, wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa nan take, lamarin da ya sa sauran abokan aikinsa da ke wurin suka tsere.
Bayan sun yi kisan, ’yan bindigar sun ɗauke bindigar marigayin sannan suka tsere daga wurin.
Kakakin rundunar ’yan sandan Taraba, ASP Leshen James, bai ɗaga wayar kiran da aka yi masa ba kuma bai amsa saƙon da aka tura masa dangane da lamarin ba.