Australia ta gargadi Isra’ila game yunkurin mamaye birnin Gaza
Published: 8th, August 2025 GMT
A wannan Juma’a ne Australia ta bukaci Isra’ila da ta janye shirinta na mamaye yankin Zirin Gaza, inda ta yi gargadin cewa hakan zai kai ga barkewar matsaloli na jin kai a yankin.
Ministar harkokin wajen Australiya Penny Wang a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce: Australia ta yi kira ga Isra’ila da kada ta bi wannan zabi, wanda zai kara ta’azzara matsaloli a zirin Gaza, tana mai jaddada cewa, tilasta tsugunnar da Falastinawa a wajen yankunansu ya sabawa dukanin dokoki na kasa da kasa.
Wang ta sake nanata kiranta na “tsagaita bude wuta, da shigar da kayan agaji ba tare da wani cikas ko tarnaki ba, da kuma sakin fursunonin da Hamas ke tsare da su tun watan Oktoban 2023.”
Ta yi nuni da cewa, batun kafa kasashe biyu ita ce hanya daya tilo ta hanyar samun zaman lafiya mai dorewa, ta hanyar kafa kasar Falasdinu tare da kasar Isra’ila, da zaman lafiya da tsaro a cikin iyakokin da kasashen duniya suka amince da su.”
Duk da ci gaba da sukar da take yi wa Isra’ila, har yanzu Australia ba ta bi sahun kawayenta na yammacin duniya kamar Canada da Faransa ba wajen bayyana aniyarsu ta amincewa da kasar Falasdinu mai ci cin gashin aknta ba. Duk da haka, ta jaddada cewa “za ta yanke shawara a lokacin da ya dace.”
Kalaman na Wang sun zo ne a matsayin mayar da martani ga wata hira da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi da gidan talabijin na Fox News, inda ya bayyana aniyar Isra’ila na kakaba takunkumin soji a daukacin zirin Gaza. Ya ce, “Tel Aviv na son mika wa dakarun Larabawa yankin gabar tekun don tafiyar da shi,” ba tare da fayyace tsari ko kuma kasashen da za su shiga cikin shirin ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Axios: Majalisar ministocin Isra’ila ta amince da sabon shiri na mamaye birnin Gaza August 8, 2025 Iran Ta Kira taron Gaggawa Na Kungiyar Kasashen Musulmi August 8, 2025 Iraniyawa Miliyon 1.2 Ne Suka Shiga Iraki Ta Kofar Shiga Na Mehran August 8, 2025 Ansarullah Ta Yi Gargadi Ga Amurka Da HKI Kan Kara Tada Hankali A Yakin August 8, 2025 Hizbullah Da Amal Sun Yi Tir da Shirin Kwance Damarar Hizbullah August 8, 2025 Jirgin Daukar Marasa Lafiya Ya fadi A kasar kenya Ya Kuma Kashe Akalla mutane 6 August 8, 2025 Araqchi: Hari Kan Cibiyoyin Makamashin Nukiliyar Kasar Iran Ba Zai Taba Canza Matsayinta Ba August 7, 2025 Manjo Janar Mousawi: Martanin Iran Nan Gaba Zai Kasance Mafi Muni Kan Makiya August 7, 2025 Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran Sun Jaddada Shirinsu Na Tunkarar Duk Wata Barazana August 7, 2025 Hare-Haren Sojojin Mamayar Isra’ila Kan Gaza Sun Janyo Shahadan Falasdinawa Masu Yawa August 7, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Dembele Ya Lashe Kyautar Ballon d’Or Ta Shekara Ta 2025.
An bayyana dan wasan a matsayin wanda ya lashe kyautar ne a bikin da aka gudanar ranar Litinin 22 ga watan Satumban 2025 a dakin taro na Theatre du Chatelet da ke birnin Paris a kasar Faransa.
Ballon d’Or kyauta ce da akan bai wa dan wasan da ya nuna gwaninta a kowace shekara, inda akan yi la’akari da gudunmawar da dan wasan ya bayar ga kungiya da kuma kasarsa.
Tun farko an fitar da jerin ‘ƴan wasa 30 cikin wadanda ake sa ran za su lashe kyautar.
Dembele ya taka rawar gani wajen taimakon kungiyar PSG ta lashe gasar Ligue 1 da da kuma samun nasarar lashe gasar Champions Leage na farko a tarihinta, sannan ta kai wasan karshe a gasar kofin duniya ta ƙungiyoyi.
Ya zura ƙwallo 21 a wasa 29 da ya buga a gasar Ligue 1, inda ya karkare gasar a matayin wanda ya fi zura kwallo, sannan ya lashe kyautar gwarzon dan’wasan gasar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hindi: Amurka Da Kasashen Yamma Ba Sa Son A Dakatar Da Bude Wuta A Gaza. September 23, 2025 Tattalin Arzikin Najeriya Ya HaBaka A Rubu’i Na Biyu Na 2025 September 23, 2025 Kashi 80 Cikin Dari Na MDD Sun Amince Da Falasdinu A Matsayin Kasa. September 23, 2025 Iran Da Rasha Zasu Rattaba Hannun Kan Batun Gina Wasu Tashoshin Nukiliya. September 23, 2025 Hamas ta bukaci kasashen duniya da MDD su mayar da Isra’ila saniyar ware September 22, 2025 Iran : Dakatar da kisan kiyashi a Gaza, ‘’zakaran gwajin dafi ‘’ne ga MDD” September 22, 2025 Italiya: An yi gagarimar zanga-zangar tir da kisan kiyashi da ake yi a Gaza September 22, 2025 Iran ta la’anci harin da aka kai kan wani masallaci a Sudan September 22, 2025 Ana Ci Gaba Da Kidayar Kuri’aun Zaben Shugaban Kasa A Guinea September 22, 2025 Kwamandan Sojan Iran: Ba Za Mu Taba Wasa Da Manufofinmu Na Kasa Ba September 22, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci