Za a gyara tarbiyar tubabbun ’yan daban Kano
Published: 11th, August 2025 GMT
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya shawarci matasan da ake ribatarsu a matsayin ’yan daban siyasa da suka tuba da su guji tashin hankali, yana tabbatar musu da shirye-shiryen gwamnatinsa na gyara tarbiyarsu tare da mayar da su cikin al’umma.
Gwamnan ya yi wannan alkawari ne a taron wuni ɗaya da aka gudanar tare da shugabannin rukunan ’yan daban da suka tuba a ƙarƙashin Shirin Safe Corridor.
Gwamnan, wanda Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Waiya, ya wakilta, ya ce: “Ba za a sake ɗaukar makami da sunan fadan siyasa ko wasu munanan dabi’u ba.
“Za mu gyara muku tarbiya, mu tabbatar kun samu ababen yi da suka dace domin samun abun dogaro da kai. Za mu karɓe ku ɗaya bayan ɗaya, mu gyara ku, mu tura ku inda kuka fi dacewa.”
Waiya ya bayyana cewa wasu daga cikin tubabbun mutanen da aka yi wa rajista a baya a cikin shirin sun riga sun rasu, inda gwamnati za ta sake gudanar da sabon aikin tantancewa domin sabunta bayanai.
Ya jaddada cewa wannan shiri ba na siyasa ba ne, yana mai cewa manufarsa ita ce kawar da matsalar ‘yan daba da sauran munanan halaye a jihar.
“Mutane da dama masu shekarunku suna yin abubuwa masu kyau. Mun fahimci cewa ba ku ci moriyar wasu shirye-shirye na tallafi ba a baya, amma yanzu mun tsaya tsayin daka domin ku,” in ji shi.
Sauran masu jawabi a yayin taron sun haɗa da Kwamandan Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) na Kano, Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar, da sauran masu ruwa da tsaki wajen yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi a Kano.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan daba Jihar Kano Siyasa
এছাড়াও পড়ুন:
UNICEF Da Gavi Sun Bada Na’urorin Samar Da Wutar Lantarki Ta Hasken Rana Ga Jihar Kano
Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) tare da haɗin gwiwar Gavi da ke taimakawa wajen samar da rigakafi, sun mika na’urorin samar da wutar lantarki ta hasken rana g Gwamnatin Jihar Kano domin amfani da su a cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko (PHCs) guda 28 da nufin ƙarfafa rigakafin yara da kuma kula da lafiyar jama’a.
A yayin bikin mika kayayyakin ga gwamnatin jihar da Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Ƙasa (NPHCDA), Kwamishinan Lafiya na Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya ce wannan shiri na nufin taimaka wa yaran da ba a musu rigakafi, da mata masu juna biyu da ba su da damar samun rigakafin yau da kullum da kuma wasu ayyukan kiwon lafiya.
“UNICEF tare da Gavi, ƙarƙashin shirin ƙarfafa tsarin kiwon lafiya na CDS3, sun tallafa wajen saka na’urorin hasken rana a cibiyoyin PHC na kananan hukumomin da ke da yawan yaran da ba a musu rigakafi a Najeriya.” In ji Dakta Labaran.
Ya ce Kano ce ta fi kowace jiha a Najeriya yawan yaran da ba a taba yi wa rigakafi ba, yana mai jaddada cewa cibiyoyin da aka saka musu wadannan na’urorin za su taka muhimmiyar rawa wajen kawar da matsalar.
Wannan aiki ya biyo bayan binciken yadda cibiyoyin lafiya a matakin farko ke aiki da wutar lantarki da UNICEF ta tallafa a shekarar 2023, wanda ya gano cibiyoyi 371 da suka cancanci a saka musu na’urorin. A wannan matakin, tare da haɗin gwiwar eHealth Systems Africa, an samar da wutar hasken rana a cibiyoyi 28 a Kano.
Tsarin zaɓen cibiyoyin ya mayar da hankali kan cibiyoyin kiwon lafiya a kananan hukumomin da ke da yawan yaran da ba a musu rigakafi, tare da cire waɗanda wasu ayyuka irin su CRIBS da IMPACT suka riga suka rufe, da kuma mayar da hankali kan cibiyoyin da ba su da ingantacciyar wutar lantarki.
Dakta Labaran ya gargadi jami’an da ke kula da cibiyoyin da kada su karkatar da su don amfani na kashin kansu.
Daraktan Ƙasa na Gavi, Jessica Crawford, ta bayyana cewa wannan karamcin wani ɓangare ne na ƙoƙarin haɗin gwiwa don ƙarfafa tsarin kiwon lafiya a Kano, inda ta ƙara da cewa Gavi za ta kashe kusan dala miliyan biyar a jihar cikin shekara biyu masu zuwa domin tallafawa manufofi da shirye-shiryen gwamnati wajen inganta lafiyar mata da yara.
Mai riƙon mukamin Shugaban Ofishin UNICEF a Kano, Michael Banda, wanda ya wakilci Shugaban Ofishin, Mista Rahama Rihood Mohammed Farah, ya bayyana shirin a matsayin mataki na gina tsarin kiwon lafiya mai ɗorewa da adalci ga kowa.
Ya bayyana cewa samun wutar lantarki mai inganci na taimakawa wajen adana rigakafi yadda ya kamata, yin aiki a kowane lokaci, da rage dogaro da man fetur.
Taron ya samu halartar Darakta Janar na Hukumar Kula da Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Kano, Farfesa Salisu Ibrahim, da wakilai daga WHO, Gidauniyar Gates, da sauran abokan haɗin gwiwa.
Daga Khadijah Aliyu