Tattalin Arzikin Kasar Sin Na Da Makoma Mai Haske In Ji Wani Kwararre
Published: 11th, August 2025 GMT
Fitaccen masanin tattalin arziki dan kasar Birtaniya John Ross, ya ce ma’aunin tattalin arziki na GDP na kasar Sin ya karu da kaso 5.3 bisa dari a mizanin shekara, cikin rabin farko na shekarar nan ta 2025, wanda hakan ke nuni ga ingancin tushen tattalin arzikin kasar.
Ross, wanda ya bayyana hakan a baya-bayan nan, yayin zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua, ya ce Sin ta wanzar da managarcin yanayin zuba jari, tana kuma kara fadada jarin da ake shigarwa a fannin bincike da samar da ci gaba, tare da ingiza daga matsayin fasahohi, wanda hakan ya haifar da managarcin yanayi na bunkasa tattalin arzikin kasar.
Bugu da kari, masanin ya ce, a matsayinta na kasa dake kan gaba wajen cinikayyar hajoji, Sin na ci gaba da ingiza manufar bude kofa mai inganci ga sassan kasa da kasa, tana kuma kara bude kofofin kasuwanninta ga duniya, da tsayawa tsayin daka wajen bunkasa dunkule tattalin arzikin duniya baki daya. Ya ce, ko shakka babu kasar Sin ta zamo babban ginshiki na ingiza dunkulewar duniya waje guda. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: tattalin arzikin kasar
এছাড়াও পড়ুন:
Ba Gudu Ba Ja-da-baya Kan Ci Gaba Da Kwaskwarima Ga Tsarin Haƙar Ma’adanai – Minista
“Shekaru goma da suka wuce, gudummawar da ma’adanai ke bayarwa ga GDP na kasarmu bai wuce 0.5% ba, amma a yau ya karu zuwa 1.8% – alkalumman NBS suka nuna a cikin rabi na biyu na 2025 wanda ba a taba ganin irinsa ba”.
Da yake tsokaci kan ci gaban fannin, Ministan ya bayyana cewa, makon hako ma’adanai na Nijeriya ya yi nuni da yadda masana’antar ke sauya tunani zuwa tsari mai kyau, da sabbin abubuwa, da ke lalubo masu zuba jari na kasa da kasa.
Ya bayyana cewa, sauye-sauyen sun tattara ne a kan gaskiya, rage haɗari, da inganta masana’antar.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA