Cacar Baki Ta Ɓarke Tsakanin el-Rufai Da APC Kan Tazarcen Tinubu A 2027
Published: 10th, August 2025 GMT
Mambobin haɗakar jam’iyar sun ƙunshi tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi da tsohon gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal da tsohon shugaban jam’iyyar APC, John Oyegun, da sauran manyan mutane da dama.
A cikin wannan tsarin, haɗakar jam’iyyar ta naɗa tsohon shugaban majalisar dattawa, Daɓid Mark da tsohon ministan cikin gida, Rauf Aregbesola, a matsayin shugaban da sakatare na riƙon ƙwarya.
Tun daga wannan lokaci, jam’iyyar tana ta karɓar masu sauya sheƙa daga sauran jam’iyyun adawa da kuma gudanar da tarurruka domin ƙara masun mambobi a faɗin ƙasar nan kafin zaɓen 2027.
El-Rufai, wanda ya kasance ɗaya daga cikin asalin mambobin APC, ya fice zuwa jam’iyyar SDP a rubi’in farko na wannan shekarar. Haka kuma ya kasance cikin jam’iyyar haɗaka ta ADC.
Ya bayyana cikakken goyon bayansa ga ADC kuma ya yi alƙawarin taimakawa wajen jan hankali ‘yan Nijeriya domin tabbatar da cewa APC ta sha kaye a 2027 a lokacin taron Sakkwato.
Tsohon gwamnan Kaduna ya jaddada cewa idan Tinubu ya samu wa’adi na biyu zai zama barazana mai tsanani ga makomar ƙasar nan.
“Na yi imanin cewa in muka yarda wannan jam’iyya da gwamnatinta ta ci gaba da mulki a zango na biyu, za ta wawuri dukkan abin da ya rage na tattalin arzikin Nijeriya, kuma ba za mu sami ɓarɓushin ƙasarmu ba ko kaɗan. Don haka, wannan yaƙi ne don rayukanmu,” in ji shi.
El-Rufai ya ce dawowarsa cikin harkokin siyasa ba ta ƙashin kansa ba, said ai akwai buƙatar dawowarsa don yaƙar gazawar wannan gwamnati.
Da yake mayar wa El-Rufai martani, sakataren jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Ajibola Basiru, ya buƙaci El-Rufai ya dakatar da yaƙin neman zaɓe 2027 har sai lokaci ya yi, kuma ya jira ya gani yadda jam’iyya mai mulki za ta ƙara yin nasara.
Sakataren APC ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai ta wayar tarho a ƙarshen mako.
Yayin da yake martanin, sakatare APC ya yi kira ga tsohon Gwamnan Jihar Kaduna da ya nemi aiki yi da zai sa ya zama mara zaman banza kafin zaɓen 2027.
Ya nuna cewa za a bayyana jadawalin zaɓen 2027 ne a watan Fabrairun 2026, ya yi mamakin yadda tsohon gwamnan Jihar Kaduna ya fara yaƙin neman zaɓen da ya rage saura shekara biyu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Yelwatza
এছাড়াও পড়ুন:
Ɗan Majalisar Wakilai, Jibrin Ƙofa Ya Sauya Sheƙa Daga NNPP Zuwa APC
Da yake sanar da sauya sheƙarsa a ranar Litinin ta hanyar shafukansa na sada zumunta da aka tabbatar, Jibrin ya ce magoya bayansa sun yanke shawarar barin jam’iyyar NNPP da kuma kungiyar Kwankwasiyya don shiga APC da kuma yin aiki tuƙuru don marawa Shugaba Tinubu baya a zaɓen 2027.
“A yau, a cikin nuna goyon baya, dubban ‘yan mazaɓarmu a garinmu na Ƙofa, Bebeji, Kano sun yi min maraba sosai. Taron ya tabbatar barinmu jam’iyyar NNPP/Kwankwasiyya, zuwa APC, da kuma goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu a karo na biyu a kan mulki,” in ji Jibrin.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA