Tsohon Ministan Noma Audu Ogbeh ya rasu
Published: 9th, August 2025 GMT
Allah Ya yi wa tsohon Ministan Aikin Gona, Cif Audu Ogbeh rasuwa.
Iyalansa sun sanar cewa a safiyar Asabar Allah Ya yi masa cikawa, yana da shekara 78 a duniya.
.উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: ya rasu
এছাড়াও পড়ুন:
Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 4, 16 sun jikkata a Yobe
Aƙalla mutum ne sun rasu, yayin da wasu 16 suka jikkata a wani hatsarin mota da ya auku a Ƙaramar Hukumar Karasuwa, a Jihar Yobe.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Yobe, SP Dungus Abdulkareem ne, ya tabbatar da faruwar hatsarin ya faru a ranar Asabar da misalin ƙarfe 2:50 na rana a ƙauyen Zangon Kanwa.
Gwamnan Gombe ya bai wa maharba kyautar motoci da babura don bunƙasa tsaro An sanya tukwicin N10m domin kama makasan limamin coci a EnuguHatsarin ya rutsa da mota ƙirar Toyota Hiace wadda ke ɗauke da fasinjoji daga Jakusko zuwa kasuwar Jajimaji da kuma mota ƙirar Volvo daga garin Azare.
Rahoto ya nuna cewa mota ƙirar bas ce ta ƙwace ta buga wani Keke Napep sannan ta ci karo da babbar motar.
Sakamakon haka, direban bas ɗin, Ibrahim Makeri, tare da fasinjoji biyu; Adamu Isiya da Alhaji Shaibu sun rasu nan take.
Daga baya kuma wani daga cikin waɗanda suka ji rauni ya rasu, wanda ya kawo adadin waɗanda suka mutu zuwa huɗu.
An kai gawarwakin da kuma waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Gashuwa da ke Ƙaramar Hukumar Bade.
Likitoci suka tabbatar da mutuwar waɗanda suka rasu, sauran kuwa suna samun kulawa.