Ghana: Ministocin tsaro da muhalli sun rasa rayukansu a hatsarin jirgi mai saukar ungulu
Published: 7th, August 2025 GMT
Ministocin tsaro da muhalli na Ghana na daga cikin mutane takwas da suka rasa rayukansu a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a ranar wannan Laraba, kamar yadda fadar shugaban kasar ta tabbatar, bayan da rundunar sojin kasar ta bayar da rahoton cewa jirgin ya fita daga tsarin tantacewa na na na’urar radar.
Lamarin dai ya jefa al’ummar kasar cikin firgici tare da sanar da makoki a dukkanin fadin kasar a hukumance.
Ministan tsaro Edward Omane Boamah ya hau kan mukaminsa ne bayan rantsar da Shugaba John Mahama a watan Janairu. Sai kuma Ministan Muhalli, Kimiyya da Fasaha Ibrahim Murtala Muhammed, wanda shi ma yana cikin wadanda suka rasa rayukansu a hadarin.
Shugaban ma’aikata Mahama Julius Debrah ya ce “Shugaban kasa da gwamnati suna mika ta’aziyyarmu da jajantawa ga iyalan ‘yan uwanmu da ma’aikatan da suka rasa rayukans a hidimar kasa,” in ji Julius Debrah, kamar yadda kuma hukumomi suka tabbatar da cewa babu wanda ya tsira a hatsarin.
Wannan lamari dai ya auku ne a daidai lokacin da ake kara nuna damuwa kan karuwar barazanar kungiyoyin ‘yan ta’ada masu ikirarin jihadi a kan iyakar Ghana da Burkina Faso da ke arewacin kasar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Jamus: Shahararrun mutane fiye da 160 da ‘yan jarida sun bukaci a daina baiwa Israila makamai August 7, 2025 Gaza: Fararen hula 22 sun yi shahada a hare-haren Isra’ila a daren jiya August 7, 2025 Pezeshkian Ya Jaddada Wajabcin Haduwar Kasashen Musulmi Wajen Hana Laifukan Yaki A Gaza August 6, 2025 Araqchi Ya Taya Larijani Murnar Zama Sakataren Majalisar Kolin Tsaron Kasar Iran August 6, 2025 Japan: An Fara Juyayin Cikar Shekaru 80 Da Harin Amurka Na Makamin Nukiliya A Hiroshima August 6, 2025 Sudan: Dakarun RSF Sun Kashe Fararen Hula 14 Tare Da Jikkata Wasu Na Daban August 6, 2025 IRGC: Bayan yakin Kwanaki 12 Yanayi Ya Sauya Zuwa Ga Amfani Ga Iran August 6, 2025 ‘Yansanda A Iran Suna Amfani Da Kayakin Tsaro Na Zamani A Lokacin 40 August 6, 2025 Iran tana Goyon Bayan Zaman Lafiya Tsakanun Kasashen Yankin August 6, 2025 Azizi: Iran Ba Za Ta Bar Wani Ya Kusanci Cibiyoyinta Na Tace Sanadarin Uranium Ba August 6, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Rahotonni Sun Bayyana Cewa; Agajin Jin kai Da Ake Wurga Ta Sama A Gaza Tamkar Digon Ruwa Ne
Jaridar Le Monde ta bayyana cewa: Tallafin kayan da jiragen sama suke saukarwa a Gaza tamkar digon ruwa ne idan aka kwatanta girman bukatun al’ummar yankin
Jaridar Le Monde ta ruwaito cewa, ko da yake hukumomin mamayar Isra’ila, a karkashin matsin lamba na kasa da kasa, sun ba da izinin saukar da kayan agajin abinci ta hanyar jiragen sama, amma adadin tallafin takaitacce ne da ba zai magance wata matsala ba.
Le Monde ta kara da cewa: Sakamakon ya bayyana takaitacce ne a daidai lokacin da dubban manyan motoci makare da kayan agaji ke makale a wajen zirin Gaza. Jaridar ta yi bayanin cewa kasashe da dama da suka hada da Jordan, Hadaddiyar Daular Larabawa, Faransa, da Birtaniya, sun fara jigilar kayan agaji zuwa zirin Gaza mako guda da ya gabata ta hanyar amfani da jiragen yaki da ke shawagi a kan yankin Falasdinu.
Faransa za ta yi taimaka da ton 40 a jigila hudu, yayin da Spain za ta sauke tan 12. Sauran ƙasashe, kamar Belgium, Italiya, da Jamus, suma sun sanar da aniyarsu ta shiga ko ba da gudummawa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Wa’adin Da Shugaban Amurka Ya Gindaya Na Kawo Karshen Yaki A Ukraine Ya Karato Ba Tare Da Alamun Karewarsa Ba August 4, 2025 Sojojin Somaliya Sun halaka Mayakan Kungiyar Al-Shabab Fiye Da Hamsin A Kudu Maso Yammacin Mogadishu August 4, 2025 Pakisatan: Iran Ce Madogara Ga Al-ummar Musulmi August 4, 2025 Wakilin Hukumar FAO A Iran Yace Sauyin Yanayi Ya shafi Dukkan Yankin August 4, 2025 Malamai A Najeriya Suna Goyon Bayan Iran A Yadda Take Fuskantar HKI August 4, 2025 Shugaban Kasar Lebanon Ya Yi Alkawalin Adalci Ga Wadanda Feshewar Beirut Ta Shafa August 4, 2025 Iran Ta Ce Ba Wani Ma’aikacin Hukumar IAEA A Kasar A Halin Yanzu August 4, 2025 Pezeshkian ya yaba da irin goyon bayan da Pakistan ta baiwa Iran a lokacin yaki August 4, 2025 Bloomberg: FBI ta cire sunan Trump daga Fayilolin badakalar Epstein August 4, 2025 Jerin gwanon nuna goyon baya ga al’ummar Gaza a Sydney Australia August 4, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci