Soja ya soka wa ɗan sanda wuƙa har Lahira a Taraba
Published: 9th, August 2025 GMT
Wani kurtun soja ya soka wani ɗan sanda mai mukamin Constable, Aaron John da wuƙa har lahira a garin Jalingo, hedikwatar Jihar Taraba.
Kakakin ’yan sanda na jihar, James Lashen, ya ce wannan mummunan al’amari ya faru ne da misalin karfe 9 na dare a ranar Litinin, a unguwar Mayo-Goyi, da ke gefen birnin Jalingo.
Lashen ya bayyana cewa marigayi John ya samu kiran gaggawa daga wasu mazauna yankin dangane da sabani da suka samu da sojan.
A yayin da yake kokarin warware rikicin, sai sojan mai suna Dauda Dedan, ya soka masa wuƙa.
Ya ce, “Mun samu rahoton lamarin daga hedikwatar Brigade ta 6 ta Rundunar Sojin Najeriya, da tabbacin cewa za a kamo sojan da ya tsere domin fuskantar hukunci,” in ji Lashen.
Ya ƙara da cewa rundunar soji ta fara bincike kan lamarin, tare da tabbatar wa ’yan sanda cewa za su haɗa kai wajen kamo wanda ake zargi.
“Sojoji da ’yan sanda na aiki tare. Mun kai ziyara har gidan sojan, kuma za mu tabbatar an kama shi domin ya fuskanci hukunci daidai da abin da ya aikata,” in ji Lashen.
Ya jaddada cewa dangantaka tsakanin sojoji da ’yan sanda a jihar Taraba tana da kyau kuma babu wata matsala a tsakaninsu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ɗan Sanda har lahira
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Abin Da Doka Ya Ce Kan Kisan Jami’an ‘Yan Sanda
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Kisan jami’an tsaro na cigaba da zama ruwan dare a Najeriya, lamarin da ya daɗe yana tayar da hankali, amma a ‘yan kwanakin nan abin ya ƙara muni.
Misali, kwanan nan a an kashe wasu jami’an ‘yan sanda a kananan hukumomin Katsina-Ala da Ukum a jihar Benue, inda ‘yan bindiga suka kai hari tare da kashe ‘yan sanda uku inda suka kuma sace wasu bakwai.
NAJERIYA A YAU: Yadda Wata Bakuwar Cuta Take Cin Naman Jikin Mutanen Malabu DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin NajeriyaShirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan abin da dokokin kasa suka ce kan kisan jami’an ‘yan sanda.
Domin sauke shirin, latsa nan