Leadership News Hausa:
2025-08-08@10:14:31 GMT

Buƙatar Katange Iyakokin Nijeriya Don Tabbatar Da Tsaro 

Published: 8th, August 2025 GMT

Buƙatar Katange Iyakokin Nijeriya Don Tabbatar Da Tsaro 

Nijeriya ta kasance ƙasa ce, mai girman gaske, wadda kuma ‘yan ta’adda masu iƙirarin jihadi, Al-kamar irinsu; Al- Ƙaeda da ISIS da ke aikata ayyukan ta’addancinsu a yankin Sahel ke kutsowa cikin ƙasar, domin aikata ta’addanci.

Bugu da ƙari, ba tun yau ne, wasu ƙwararru a ɓangaren tsaro na ƙasar nan, suke yin gargaɗin cewa, yadda aka bar iyakokin ƙasar sakakai ne, ke ƙara ta’azzara matsalar tsaro a ƙasa, inda wasu’yan ta’adda daga wajen ƙasar, ke yin amfani da damar, wajen shigowa tare da kuma shigo da muggan makamai da yadda masu ra’ayin riƙau na addini, daga ƙasashe kamar su, Mali da Jamhuriyar Nijar da Chadi, ke shigowa ƙasar, su kuma ci Karensu ba babbaka.

Misali, ‘yan ta’addar ƙungiyar Lakurawa, masu iƙirarin jihadi, waɗanda ta hanyar ayyukan ta’addacin su, suka hana wasu yankuna musamman a Arewa Maso Yamma sakat, daga nan kuma suka ƙara faɗaɗa ta’addacinsu, zuwa wasu yankuna na Arewa Maso Gabas da kuma zuwa iyakokin Nijeriya da Jamhuriyar Nijar.

Hakazalika, wasu rahotanni sun nuna cewa, ‘yan ta’addar Lakurawan ‘yan aware nada alaka da ƙungiyar masu iƙirarin jihadi da ke gudanar da ayyukansu na ta’addanci, a yankin Sahel, waɗanda shigarwarsu wasu yankuna na Arewa Maso Yammacin ƙasar nan, suka samu damar janyo suke janyo ra’ayoyin wasu matasa cikin ƙungiyar da kuma auren wasu da yankunan na Arewa Maso Yamma.

Shi ma wani tsohon mai magana da yawun rundunar tsaron ƙasar Majo Janar Edward Buba, ya sanar da cewa, ƙungiyar ce, ta ƙara haifar da rudanin siyasa a ƙasashen Mali da Jamhuriyyar Nijar.

Kamar yadda Janar Musa ya faɗa, katange iyakon Nijeriya abu da ke da alfanu da dama ga ƙasar, musamman domin ci gaba da dorewar ƙasar da kuma kare ta, daga hare-hare daga ketare.

Tabbas batun Katange ƙasar, abu ne, da zai laƙumi ɗimbin kuɗaɗe, amma aiwatar da hakan, zai kare Nijeriya daga kutsen ‘yan ta’adda daga wajen aasar.

A wani rahoto da Asusun da ke tallawa kananan yara na majalisar dinkin duniya wato UNICEF, ya yi gargaɗin cewa, rikice-rikicen da ke aukuwa a yankin Sahel ta tsakiya, na kutsawa zuwa wasu ƙasashen da ke maƙwabtaka na yankin, wanda hakan ke kara ta’azzara tarwatsa alumomi daga yankunan su da haifar da matsin tattalin arziki da kuma haifar da  karanci kuɗaɗe.

Duba da yadda iyakokin Nijeriya suke sakakai, wannan matsalar za iya cewa, tamkar kasar, na zaune, a karkashin Bam.

Ya zama wajibi mahukunta a Nijeriya su ɗauki dabaru Nijeriya wajen daƙile shigowar ‘yan ta’adda cikin ƙasar.

Duk da cewar, katange iyakon Nijeriya ba zai hana kutsowar ‘yan ta’adda ba, amma katangewar, za ta taimaka wa hukumomin tsaron ƙasar wajen ƙaukar matakan gaggawa na mayar da martani, ta hanyar yin amfani da kayan aiki na sanya ido.

Tsawon iyakonin Nijeriya, ya kai sama da kilomita 4,000 kilomita, wanda hakan ke nuna cewa, sun fi ƙarfin jami’an hukumar kula da shige da fice, iya kula da iyakokin su kaɗai.

Hakazalika, salon shugabanci a ƙasar na rashin nuna damuwa, ya sanya iyakokin ƙasar sun kasance wajen na samun damar shigowar ɓata gari cikin ƙasar, musamman ga ‘yan ta’addar daga yankin Sahel.

Akwai wasu dabarun zamani da ya kamata a runguma a ƙasa na katange iyakokin ƙasar.

Alamisali, ƙasar Fakistan wadda ta yi iyaka da ƙasar Afghanistan, kusan ta kammala katange iyakokinta masu tsawon kilomita 2,611 wanda aikin ya kai kaso 98.

Kazalika, ƙasar Saudi Arabiya, wadda ta yi iyaka da ƙasar Iraki, ta katange iyakar da ƙasar tsawon kilomita 900 domin daƙile shigowar masu fasakwari da kuma barazanar ‘yan ta’adda.

Wadannan misalan kaɗai, sun isa hujjar da nuna cewa, katange iyakokin ƙasa tare da yin amfani da kayan fasahar zamani, za su taimaka wajen ƙara tabbatar ƙasa. 

Batun gaskiya a nan shi ne, mun yi ammanar cewar cewa, rashin tsaron da ke ci gaba da addabar Nijeriya ba daga cikin gida Nijeriya ba ne, daga ƙetare ne.

A ra’ayin wannan Jaridar, muma muna goyon bayan kiran na  Janar Musa, na buƙatar a katange iyakokin ƙasa, domin kuwa, bai kamata ace, Nijeriya ta yi wani jinkirin aiwatar da hakan ba. Wannan ne matsayar mu.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Nijeriya katange iyakokin a yankin Sahel iyakokin ƙasa a Arewa Maso yan ta adda

এছাড়াও পড়ুন:

An kama bama-baman da aka boye a cikin kayan gwangwan a Kaduna

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta kama wasu bama-bamai da ba su fashe ba da wasu tarin makamai da aka shigar da su jihar cikin kayan gwangwan daga jihar Borno.

Lamarin dai ya jefa fargaba a zukatan mutane kan yadda kayayyaki ke yawo babu bincike daga jihohin da ke fama da rikici.

Yadda kwacen babur da waya ya maye gurbin garkuwa da mutane a Birnin Gwari Bai kamata ake bai wa ɓarayi muƙamin ministoci ba — Sarki Sanusi II

Kakakin rundunar a jihar, DSP Mansir Hassan ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce an kama kayan ne ranar Asabar bayan wasu bayanan sirri da rundunar ta samu.

Ya ce an samu kayan ne a cikin wani kamfanin da ke hada-hadar kayan gwangwan da ke rukunin masana’antu na Kudandan da ke karamar hukumar Kaduna ta Kudu.

“Wasu kwararrun jami’anmu daga sashen da ke kula da abubuwa masu fashewa ne ya je wajen bayan bayanan. Bayan cikakken bincike, an tabbatar da cewa kayan bama-bamai ne da ba su kai ga fashewa ba,” in ji Mansir.

Kakakin ya ce nan take jami’an nasu suka kwashe bama-baman zuwa wajen da ya dace sannan suka lalata su ba tare da sun fashe ba.

Ya kuma ce yayin aikin, dakarun sun gano makamai, cikin har da wata karamar bindiga kirar gida wacce ke makare da albarusai, da ma wasu tarin makaman.

Kakakin ya ce nan take Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Rabiu Muhammad ya bayar da umarnin rufe kamfanin da aka sami kayan domin a samu damar fitar da dukkan makaman ba tare da an bar ragowa ba.

Kwamishinan ya kuma gargadi masu sana’ar ta gwangwan da su daina kawo irin kayayyakin daga yankunan da suke fama da rikici zuwa jihar ta Kaduna.

Ya kuma ce yanzu haka suna ci gaba da bincike domin gano tushen makaman da kuma dalilin shigo da su cikin jihar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mahaifin Ɗan Bello ya rasu
  • NAHCON ta ƙayyade N8.5m kafin alƙalami na kujerar Hajjin 2026
  • Nijeriya Da Indiya Za Su Haɗa Kai Wajen Yaƙi Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi
  • An kama bama-baman da aka boye a cikin kayan gwangwan a Kaduna
  • Masu Ƙwacen Waya Sun Kashe Ɗalibin BUK A Kano
  • Ministan tsaron Ghana da wasu sun rasu a hatsarin jirgin sama
  • Kwamishinan ‘Yan Sanda Na Jihar Kano Ya Sha Alwashin Kawar Da Badala A Harkokin Fina-finai
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce; Hadin Kai Tsakanin Cibiyoyi  Na Tabbatar Da Karfi Da Ci gaba
  • An soka wa jami’in Sibil Difens wuka har lahira a Jigawa