Obi ya ziyarci Bauchi, ya ba da tallafin N15m don inganta ilimi
Published: 8th, August 2025 GMT
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, ya ziyarci Jihar Bauchi tare da ba da tallafin Naira miliyan 15 don tallafa wa harkar ilimi.
Obi, ya sauka a filin jirgin sama na Abubakar Tafawa Balewa da misalin ƙarfe 9:40 na safe.
Sojoji sun yi wa ’yan ta’adda ɓarin wuta a Borno ’Yan damfara 2 sun shiga hannun ’yan sanda a YobeBayan saukarsa ya wuce Makarantar Kiwon Lafiya da Koyon Aikin Jinya da Ungozoma ta Malikiya da ke Bauchi.
A yayin ziyarar, Obi ya gana da ɗaliban makarantar, inda ya roƙe su da su dage wajen karatu domin aikin jinya da kula da lafiya yana da matuƙar muhimmanci wajen ci gaban ƙasa.
Ya ce: “A yau, nasarar kowace al’umma tana dogara ne da lafiyar mutane. Ba za a iya maganar lafiya ba tare da an ambaci masu aikin jinya da ungozoma ba.
“Ana hasashen cewa nan da shekarar 2030, za a fuskanci ƙarancin ma’aikatan jinya a duniya. Wannan ya sa aikinku ke da matuƙar muhimmanci.”
Daga nan sai ya ba da tallafin Naira miliyan 10 ga makarantar a madadin ɗaliban da ma’aikata.
Shugaban makarantar, Alhaji Aminu Mohammed Danmalikin Bauchi, ya gode masa bisa wannan tallafi da kuma irin karamcin da ya nuna.
Bayan nan, Obi ya ziyarci makarantar Islamiyya ta Intisharu Tahfizul Qur’an da ke unguwar Yelwa, inda ya gana da malamai da ɗalibai.
Shugaban makarantar, Mallam Adamu Suleiman Jibril, ya bayyana farin cikinsa da ganin Obi, inda ya bayyana hakan a matsayin ƙauna ce da damuwa wajen ci gaban ilimin addini da kuma na zamani.
Obi, ya jaddada cewa yana matuƙar muhimmanci a bai wa matasa ilimi mai nagarta da tarbiyya.
“Mun zo yau saboda muna ganin muhimmancin sauraron muryar matasa da tunaninsu game da batutuwan da suka shafi rayuwarsu da ƙasar nan,” in ji shi.
Haka kuma, Obi ya kai ziyara Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU), inda ya tattauna da ɗalibai a kan batutuwan siyasa, tattalin arziƙi da ci gaban ƙasa.
A yayin wannan ziyarar, Obi yana tare da tsohuwar Ministar Kuɗi kuma muƙaddashiyar shugabar jam’iyyar LP na ƙasa, Nenadi Usman, da kuma jagoran ƙungiyar Obi, Salisu Ibrahim.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
An rantsar da shugaban Kamaru Paul Biya karo na 8
An rantsar da Paul Biya a matsayin shugaban ƙasar Kamaru karo na takwas mai shekaru 93 a majalisar dokokin ƙasar da ke Yaoundé.
Paul Biya ya shafe shekaru 43 yana mulkin ƙasar, kuma yanzu zai fara wani wa’adi na tsawon shekara bakwai nan gaba.
Ƙungiyyar Ƙwallon yashi ta Kada BSC ta fatattaki Kebbi BSC Kwalara ta kashe mutum 10 a Ƙaramar Hukumar AdamawaBiya wanda shine shugaban ƙasa mafi tsufa a duniya, ya sami kashi 54 na ƙuri’un zaɓe, yayin da abokin takararsa, Issa Tchiroma Bakary ya samu kashi 35%, a cewar sakamakon zaɓen hukumar ƙasa.
Tchiroma Bakary dai ya yi iƙirarin cin nasara a zaɓen da aka yi yana kuma zargin cewa an yi maguɗin zabe, wanda hukumomi suka musanta.