ADA/ADC, APC Da PDP: Jam ’iyyun Siyasa Da Ke Shan Jinin ’Yan Nijeriya
Published: 9th, August 2025 GMT
Waɗan nan sune suka keɓe makomar Nijeriya, kuma suka yi garkuwa da ita. Har ila yau, a cewar majalisar dattawa ta 9 da ta yi bincike na sayar da ƙaddarorin gwamnati, wanan ɓarnar dukiyar ƙasa ne a rana tsaka, kuma kamar yadda ɗaya daga cikinsu ya bayyana kafin ya koma cikinsu, ya ce: “PRIƁATIZATION” ba komai ba ce face “PIRATIZATION” — wato sata da rabon ganima ce a fili.
Waɗannan su ne masu kuɗi na yaki haram -yaki halas ,da suka ƙwace jam’iyyu, suka wawure zaɓuka, suka yi watsi da kowa sai nasu, suka kashe baitul-mali, kuma yanzu suna neman dawowa bisa kan Karagar Mulki da sunan dimokuraɗiyya. Wannan cutar dimokuraɗiyyar Nijeriya ce da ke ƙara bazuwa, kuma yaudara ne gadan-gadan da rana tsaka!
Ko wanne cikinsu yana da tabon keta doka. Waɗannan ‘yan wasan kwaikwayo ba ‘yan adawa ba ne ga juna, amma abokai ne wajen wawure dukiyar ƙasa da kuma durƙusar da ƙasa marasa kishin Nijeriya ko ‘yan Nijeriya, wanda suke kama da Judasu da ke neman a dawo da shi cikin sahun Manzanni.
“Izaa Zulzilatil Ardu Zilzaalahaa”
“Idan ƙasa ta girgiza da girgizarta ta ƙarshe…” (Suratul Zilzalah, Aya ta 1)
Amma tambaya biyu?:
Lokacin da waɗannan bayi, ‘yan cartel, masu siyar da Nijeriya , suke rike da gwamnati daga 1999 zuwa 2025:
Me suka yi alkawari ga ‘yan Nijeriya?
Me aka tono game da su bisa kundin tsarin mulkin 1999 da dokar sayar da kamfanonin gwamnati (Priɓatization Act), da rahotannin kwamitin majalisa, da ƙasidan el-rufai da bayanan jaridun gaskiya kamar Premium Times, Guardian, Daily Trust, ThisDay, Ɓanguard, Punch, Sahara Reporters da sauransu?
Alƙawura: (Sakamakon ƙarancin wuri, za a kawo kaɗan daga ciki)
Rashin inganci na kamfanonin gwamnati yasa za a sayar da su
Tsauri da wahalar tafiyar da su
Yawan ma’aikata
Rashin riƙon amana
Cin hanci da rashawa
Nauyi ga gwamnati
Rage kashe kuɗi
Samar da ayyukan yi
Shigo da jarin da ƙasashen waje
Gyaran tattalin arziki
Ci gaban ilimi da lafiya
Bunƙasa noma
Yaki da fatara
Samar da tsaro da walwala da dai sauransu…
Amma Abin Da Suka Aikata: Suna da hannu a:
Sayar da Niger Dock, sun kori ma’aikata 3,600
Sayar da Eleme Petrochemicals -Kafanin da ta saye ta tamayar da kuɗin ta har da riban jarin a cikin watani 14 kacal.
ALSCON – An gina ta akan kuɗi dalar amurka $3.2bn, aka sayar da ita akan dalar amurka $130m.
Sayar da Daily Times, NICON Insurance, Transcorp Hilton, da Ughelli Power
NEPA, NITEL, Nigeria Airways, Delta Steel, da sauran su
Cire tallafin man fetur.
Rashin biyan fansho da hakkokin ma’aikata.
Ka da mu manta da labarin akwatuna 53 a fili tashin jirgin saman a legas ( wato the 53 Suitcases Saga).
Da labarin dalar amurka $40m da aka fitar zuwa Amurka.
Takardun makaranta jamiá da shaidar ƙaryar ta Chicago State Uniɓersity.
Raba kan ‘yan Nijeriya da salon tsarin musulim – musulim ticket.
Zargin cin hanci na Grass-cutting a san sanin ‘yan gudun hijira.
Biyan fensho har ƙarshen rayuwa ga manyan sakatarorin gwamnatin taraya (PERM.SECs) da shugaban ma’aikata(Heads of Serɓice) daga asusun IPPIS ba tare da sun bada gudunmawa ba , da dai sauran su.
Rusa tattalin arziki ta karyar da darajan naira.
Ƙarancin abinci da ilimi
Durkusar da noma da kiwo da kuma tsarin noma da ya tsaya cik
Mayar da asibitocin wajen hanyar samun kuɗin shiga da taɓarɓarewan kiwon lafiya.
Rashin tsaro da garkuwa da jama’a da dai sauransu…
Kada mu manta da wanna ayoyin
“Faman ya’mal mithƙaala tharratin khayran yarah”- (Suratul Zilzalah, Aya ta 7)
“Wa man ya’mal mithƙaala tharratin sharran yarah “-(Suratul Zilzalah, Aya ta 8)
“Zaɓin da ke Gaban ‘Yan Nijeriya”
To ga su kamar haka, ‘yan Nijeriya na cewa:
PDP – Power to the People? To ku dawo da duk ƙadarorin da aka siyar ba bisa ƙa’ida ba kuma a siyar da ƙadarorin Dubai domin a kafa cibiyoyin masana’antu na matasa.
APC – Renewed Hope? Ku dawo da tallafin da aka cire, kuma a mayar da gidan Naira biliyan 21 zuwa Asibitin Ƙasa mai daraja ta ɗaya.
ADA – Justice for All? To ku dawo da duk kuɗaɗen da aka wawure daga sayar da ƙadarori da sauran madaƙala da ya faru a ƙarƙashin zamanin ku.
ADC – Arise & Shine? To ku jabaya kuba Nijeriya da ‘yan Nijeriya damar tashi, da haskakawa da cin nasara.
Tsakanin dukkan su dake cikin PDP, APC, ADA da ADC sun more rayuwa, sunyi komai mai yuwuwa a ƙarƙashin sama ta ɗaya, halartatce da haramtatce, ko ƙarya ne?
To kada mu manta da wanna aya -“Fabi ayyi aala’i Rabbikumaa tukazzibaan?”- (Surah Ar-Rahman: Ayoyi 13 da sauran ayoyi 30)
“A Ƙarshe”
Bari mu rufe sharhin da waɗannan kalmomi masu ratsa zuciyar bil adama masu tsoron Ubangiji :
“Inna Allaha ‘ala kulli shai’in shaheed” – Lalle Allah shaida ne a kan komai. (Surah Al-Mujadilah: 6)
“Wallahu khabeerun bima ta’maloon” – Allah yana sane da duk abin da kuke yi. (Surah Al-Hujurat: 18)
“Wa makaroo wa makarallah, wallahu khayrul makireen” – (Surah Al-Imran: 54)
(Su sami malamai su yi masu cikanken bayanin wannan aya)
“Yawma’izinyasdurun naasu ashtaatan liyuraw a’maalahum” – A ranar nan, mutane za su rabu sassa daban-daban domin a nuna musu ayyukansu (munana da kyawawa). (Surah Al-Zalzalah: 6)
Hon. (Alh) Adamu Rabiu (Bakondare)
Ƙwararre a fannin Kula da Ayyuka da Tantance su (M&E) kan Manufofi, Kuɗi, Siyasa da Gudanar da Gwam
nati Mai Kyau, kuma mai fafutukar Ci Gaba Mai Ɗorewa. Ya rubuto daga Kaduna
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: yan Nijeriya
এছাড়াও পড়ুন:
Buƙatar Katange Iyakokin Nijeriya Don Tabbatar Da Tsaro
Nijeriya ta kasance ƙasa ce, mai girman gaske, wadda kuma ‘yan ta’adda masu iƙirarin jihadi, Al-kamar irinsu; Al- Ƙaeda da ISIS da ke aikata ayyukan ta’addancinsu a yankin Sahel ke kutsowa cikin ƙasar, domin aikata ta’addanci.
Bugu da ƙari, ba tun yau ne, wasu ƙwararru a ɓangaren tsaro na ƙasar nan, suke yin gargaɗin cewa, yadda aka bar iyakokin ƙasar sakakai ne, ke ƙara ta’azzara matsalar tsaro a ƙasa, inda wasu’yan ta’adda daga wajen ƙasar, ke yin amfani da damar, wajen shigowa tare da kuma shigo da muggan makamai da yadda masu ra’ayin riƙau na addini, daga ƙasashe kamar su, Mali da Jamhuriyar Nijar da Chadi, ke shigowa ƙasar, su kuma ci Karensu ba babbaka.
Misali, ‘yan ta’addar ƙungiyar Lakurawa, masu iƙirarin jihadi, waɗanda ta hanyar ayyukan ta’addacin su, suka hana wasu yankuna musamman a Arewa Maso Yamma sakat, daga nan kuma suka ƙara faɗaɗa ta’addacinsu, zuwa wasu yankuna na Arewa Maso Gabas da kuma zuwa iyakokin Nijeriya da Jamhuriyar Nijar.
Hakazalika, wasu rahotanni sun nuna cewa, ‘yan ta’addar Lakurawan ‘yan aware nada alaka da ƙungiyar masu iƙirarin jihadi da ke gudanar da ayyukansu na ta’addanci, a yankin Sahel, waɗanda shigarwarsu wasu yankuna na Arewa Maso Yammacin ƙasar nan, suka samu damar janyo suke janyo ra’ayoyin wasu matasa cikin ƙungiyar da kuma auren wasu da yankunan na Arewa Maso Yamma.
Shi ma wani tsohon mai magana da yawun rundunar tsaron ƙasar Majo Janar Edward Buba, ya sanar da cewa, ƙungiyar ce, ta ƙara haifar da rudanin siyasa a ƙasashen Mali da Jamhuriyyar Nijar.
Kamar yadda Janar Musa ya faɗa, katange iyakon Nijeriya abu da ke da alfanu da dama ga ƙasar, musamman domin ci gaba da dorewar ƙasar da kuma kare ta, daga hare-hare daga ketare.
Tabbas batun Katange ƙasar, abu ne, da zai laƙumi ɗimbin kuɗaɗe, amma aiwatar da hakan, zai kare Nijeriya daga kutsen ‘yan ta’adda daga wajen aasar.
A wani rahoto da Asusun da ke tallawa kananan yara na majalisar dinkin duniya wato UNICEF, ya yi gargaɗin cewa, rikice-rikicen da ke aukuwa a yankin Sahel ta tsakiya, na kutsawa zuwa wasu ƙasashen da ke maƙwabtaka na yankin, wanda hakan ke kara ta’azzara tarwatsa alumomi daga yankunan su da haifar da matsin tattalin arziki da kuma haifar da karanci kuɗaɗe.
Duba da yadda iyakokin Nijeriya suke sakakai, wannan matsalar za iya cewa, tamkar kasar, na zaune, a karkashin Bam.
Ya zama wajibi mahukunta a Nijeriya su ɗauki dabaru Nijeriya wajen daƙile shigowar ‘yan ta’adda cikin ƙasar.
Duk da cewar, katange iyakon Nijeriya ba zai hana kutsowar ‘yan ta’adda ba, amma katangewar, za ta taimaka wa hukumomin tsaron ƙasar wajen ƙaukar matakan gaggawa na mayar da martani, ta hanyar yin amfani da kayan aiki na sanya ido.
Tsawon iyakonin Nijeriya, ya kai sama da kilomita 4,000 kilomita, wanda hakan ke nuna cewa, sun fi ƙarfin jami’an hukumar kula da shige da fice, iya kula da iyakokin su kaɗai.
Hakazalika, salon shugabanci a ƙasar na rashin nuna damuwa, ya sanya iyakokin ƙasar sun kasance wajen na samun damar shigowar ɓata gari cikin ƙasar, musamman ga ‘yan ta’addar daga yankin Sahel.
Akwai wasu dabarun zamani da ya kamata a runguma a ƙasa na katange iyakokin ƙasar.
Alamisali, ƙasar Fakistan wadda ta yi iyaka da ƙasar Afghanistan, kusan ta kammala katange iyakokinta masu tsawon kilomita 2,611 wanda aikin ya kai kaso 98.
Kazalika, ƙasar Saudi Arabiya, wadda ta yi iyaka da ƙasar Iraki, ta katange iyakar da ƙasar tsawon kilomita 900 domin daƙile shigowar masu fasakwari da kuma barazanar ‘yan ta’adda.
Wadannan misalan kaɗai, sun isa hujjar da nuna cewa, katange iyakokin ƙasa tare da yin amfani da kayan fasahar zamani, za su taimaka wajen ƙara tabbatar ƙasa.
Batun gaskiya a nan shi ne, mun yi ammanar cewar cewa, rashin tsaron da ke ci gaba da addabar Nijeriya ba daga cikin gida Nijeriya ba ne, daga ƙetare ne.
A ra’ayin wannan Jaridar, muma muna goyon bayan kiran na Janar Musa, na buƙatar a katange iyakokin ƙasa, domin kuwa, bai kamata ace, Nijeriya ta yi wani jinkirin aiwatar da hakan ba. Wannan ne matsayar mu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp