Majalisar Jigawa Ta Yi Karatu Na Biyu Kan Dokar Fansho Ga Tsofaffin Shugabanni
Published: 8th, August 2025 GMT
Kudirin gyaran dokar fansho da sauran fa’idodi na tsaffin jami’an gwamnati ya wuce karatu na biyu a zauren Majalisar Dokokin Jihar Jigawa.
Wakilin mazabar Malam Madori, Alhaji Hamza Adamu Ibrahim wanda shi ne shugaban Kwamatin kasafin kudi na majalisar, shi ne ya gabatar da wannan kudurin, ya kuma samu goyon bayan wakilin mazabar Guri Alhaji Usman Abdullahi Tura Musari.
Alhaji Hamza Adamu Ibrahim ya yi bayanin cewar, daga cikin shugabanin da suka rike mukaman siyasa da ya kamata su amfana da irin wannan fansho sun hada da Gwamna da Mataimakan Gwamna da Shugaban Majalisar Dokoki da Kuma alfarmar da ya kamata su ci gaba da samu bayan sun bar mulki.
Bayan Akawun majalisar, Barrister Musa Aliyu Abubakar, ya gudanar da karatu na 2 akan kudurin sai Shugaban Majalisar Dokokin jihar Jigawa, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin ya kafa Kwamati na musamman mai Wakilai 7 da za su zagaya wasu daga cikin jihohin kasar nan domin gano yadda dokar ta ke aiki a wadancan jihohi.
Shugaban Masu Rinjaye na majalisar Kuma wakilin mazabar Roni, Alhaji Lawan Muhammad Dansure shi ne shugaban Kwamatin, yayin da wakilin mazabar Malam Madori Alhaji Hamza Adamu Ibrahim da na mazabar Guri Alhaji Usman Abdullahi Tura Musari da mazabar Fagam Alhaji Yahaya Zakari Kwarko da na mazabar Taura, Alhaji Dayyabu Shehu da na mazabar Kaugama Alhaji Sani Sale Zaburan da na mazabar Bulangu Alhaji Yusuf Ahmad Soja su ka kasance wakilan kwamatin.
An bai wa Kwamatin mako 4 domin ya gudanar da wannan aiki sannan ya mika rahoton sa ga zauren majalisar dokokin jihar jigawan.
Usman Mohammed Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa da na mazabar
এছাড়াও পড়ুন:
Sarkin Ruman Katsina ya rasu
A yau Litinin Allah Ya yi wa Sarkin Ruman Katsina kuma Hakimin Batsari, Alhaji Tukur Ma’azu, rasuwa.
Marigayin, wanda ya shafe shekaru 74 a duniya, ya daɗe yana fama da jinya gabanin rasuwarsa.
Hisbah ta kama masu safarar mata zuwa Saudiyya a Kano Jariri ya mutu a bayan uwarsa yayin tsere wa ’yan bindiga a NejaAlhaji Tukur wanda ya shafe shekaru 43 yana riƙe da sarautar Hakimin Batsari, ya rasu ya bar mata biyu, ’ya’ya da kuma jikoki.
Za a gudanar da jana’izarsa da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin yau a gidansa da ke cikin garin Batsari, kamar yadda sanarwa daga iyalansa ta tabbatar.