Kwamitin Sulhu na MDD na Shirin gudanar da zaman gaggawa kan batun Gaza
Published: 9th, August 2025 GMT
A gobe Lahadi ne kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai gudanar da wani zaman gaggawa kan halin da ake ciki a zirin Gaza, kamar yadda wakilin Al-Mayadeen a birnin New York ya bayyana.
Wannan shawarar ta zo ne bayan amincewar majalisar ministocin Isra’ila da shirin firaministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu, wanda ya hada da shirye-shiryen sojojin Isra’ila na mallake birnin Gaza.
Shirin ya tanadi wasu ka’idoji guda biyar na kawo karshen yakin, wanda ya fara da “kwace makaman Hamas,” sannan a dawo da dukkan fursunonin wadanda ke raye ko a mace.
Hakan zai biyo bayan kwance damarar zirin Gaza gaba daya, da kafa wata sabuwar gwamnatin da ba ta karkashin ikon kungiyar Hamas ko kuma hukumar Falasdinawa.
Za a gudanar da zaman gaggawa na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a daidai lokacin da mamayar Isra’ila ke ci gaba a a cikin yankunan Gaza, gami da kai munanan hare-hare babu kakakutawa tsawon kusan shekaru biyu a jere, lamarin da ya jefa fararen hula sama miliyan biyu a cikin mawuyacin hali da kunci, baya ga matakan baya-bayan nan nah ana shigar da abinci da kayayakin buatar rayuwa zuwa yankin wanda Isra’ila take aiwatarwa, wanda shi ma ya haifar da matsananciyar yunwa a a yankin zirin Gaza baki daya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran da Masar sun jaddada wajabcin daukar matakan kawo karshen kisan kiyashi a Gaza August 9, 2025 Jamus ta dakatar da ba wa Isra’ila kayayyakin aikin soji saboda shirinta na mamaye Gaza August 9, 2025 Hizbullah: Amurka na hakoron taimaka wa ajandar Isra’ila ne a kan Lebanon August 9, 2025 Ramaphosa da Putin sun tattauna rikicin Ukraine da batutuwan da suka shafi kasashensu August 8, 2025 Australia ta gargadi Isra’ila game da yunkurin mamaye Gaza August 8, 2025 Axios: Majalisar ministocin Isra’ila ta amince da sabon shiri na mamaye birnin Gaza August 8, 2025 Iran Ta Kira taron Gaggawa Na Kungiyar Kasashen Musulmi August 8, 2025 Iraniyawa Miliyon 1.2 Ne Suka Shiga Iraki Ta Kofar Shiga Na Mehran August 8, 2025 Ansarullah Ta Yi Gargadi Ga Amurka Da HKI Kan Kara Tada Hankali A Yakin August 8, 2025 Hizbullah Da Amal Sun Yi Tir da Shirin Kwance Damarar Hizbullah August 8, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Hizbullah: Amurka na hakoron taimaka wa ajandar Isra’ila ne a kan Lebanon
Kungiyar Hizbullah ta yi gargadin cewa Lebanon da yankin gabas ta tsakiya na fuskantar daya daga cikin yanayi mafi hadari a tarihin baya-bayan nan, inda al’ummar yankin ke fuskantar barazanar wanzuwa da kuma ‘yancinsu.
A cikin wata sanarwa da ta fitar bayan taronta na yau da kullun, kungiyar ta yi Allah wadai da yadda Isra’ila ke ci gaba da ruruta wutar rikici a yankin gabas ta tsakiya tare da goyon bayan Amurka da wasu kasashen yammacin duniya da na larabawa, a wani bangare na yunkurin sake fasalin yankin da kasar Lebanon.
Babban abin da kungiyar tafi nuna takaicinta akansa shi ne amincewar da gwamnatin Lebanon ta yi a baya-bayan nan da shawarar da manzon Amurka Tom Barrack ya gabatar.
Kungiyar ta bayyana matakin a matsayin wani sabon salo na saba alkawuran ministocin gwamnati da kuma karya rantsuwar da shugaban kasa ya yi. Ta nanata cewa takardar ta sabawa ka’idojin yarjejeniyar Taif, wadda ta tabbatar da ‘yancin kare kai da kuma kiyaye ‘yancin kasar Lebanon.
Kungiyar ta bayyana amincewar da gwamnatin kasar ta yi wa takardar Amurka a matsayin rashin gaskiya,” tana mai gargadin cewa irin wannan matsayi a file yake kan cewa ya keta yarjejeniyar kasa” tare da yin barazanar kwace wa kasar Lebanon daya daga cikin manyan hanyoyin karfinta, wato gwagwarmayar sa kai domin kare kasa.
Kungiyar ta kuma tabbatar da cewa, karfinta na soji wani babban jigo ne kuma ginshiki a fagen tsaron kasar Lbanon, musamman ma ganin yadda ake samun karuwar barazana da kuma rashin wani tabbataccen lamuni na kasa da kasa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Ramaphosa da Putin sun tattauna rikicin Ukraine da batutuwan da suka shafi kasashensu August 8, 2025 Australia ta gargadi Isra’ila game da yunkurin mamaye Gaza August 8, 2025 Axios: Majalisar ministocin Isra’ila ta amince da sabon shiri na mamaye birnin Gaza August 8, 2025 Iran Ta Kira taron Gaggawa Na Kungiyar Kasashen Musulmi August 8, 2025 Iraniyawa Miliyon 1.2 Ne Suka Shiga Iraki Ta Kofar Shiga Na Mehran August 8, 2025 Ansarullah Ta Yi Gargadi Ga Amurka Da HKI Kan Kara Tada Hankali A Yakin August 8, 2025 Hizbullah Da Amal Sun Yi Tir da Shirin Kwance Damarar Hizbullah August 8, 2025 Jirgin Daukar Marasa Lafiya Ya fadi A kasar kenya Ya Kuma Kashe Akalla mutane 6 August 8, 2025 Araqchi: Hari Kan Cibiyoyin Nukiliyar Iran Ba Zai Taba Canza Matsayinta Ba August 7, 2025 Manjo Janar Mousawi: Martanin Iran Nan Gaba Zai Kasance Mafi Muni Kan Makiya August 7, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci