2025-08-11@21:47:27 GMT
إجمالي نتائج البحث: 7684
«kasar Lebanon ta»:
Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya ce yaki da talauci muhimmin mataki ne na hanzarta ci gaban tattalin arziki da samar da ayyukan yi. Ya bayyana haka ne a lokacin shirin gwamnatin jihar mai taken “Gwamnati da Jama’a” wanda aka gudanar a karamar hukumar Ringim. Malam Umar Namadi ya jaddada muhimmancin horas da matasa sana’o’in hannu da samar da yanayin kasuwanci mai kyau domin cimma wadannan manufofi. Saboda haka, ya yi kira ga zababbun wakilai, masu rike da mukaman siyasa, shugabannin kasuwanci da sauran attajirai da su taimaka wa al’ummarsu domin kara bunkasa ci gaba da habaka tattalin arziki. A yayin taron, Kwamishinan jin kai da harkokin musamman na jihar, Auwal Danladi Sankara, ya raba naira miliyan 50...
Yanzu haka mutane huɗu suna karɓar magani a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Shika, Zariya, bayan sun jikkata a wani mummunan haɗarin da ya haɗa da tankoki biyu a ƙauyen Kake, yankin Dan Magaji, kan hanyar Zariya–Kaduna. Haɗarin ya jawo mummunar gobara bayan haɗuwar motocin. Kwamandan hukumar kiyaye haɗɗura ta ƙasa (FRSC) reshen Zariya, Nasir Abdullahi Falgore, ya bayyana cewa ɗaya daga cikin tankokin na ɗauke da iskar gas (LNG), yayin da ɗayar kuma babu komai a cikinsa. Ya ce sakamakon binciken farko ya nuna tayar ɗaya daga cikin tankokin ce ta fashe, lamarin da ya sa tankar da ke biye ta bugi ta gaba, wanda ya haddasa fashewar gas da tayar da gobara. Kwalejin Digiri...
Sojoji sun samu nasarar kai wani gagarumin farmaki kan maboyar ’yan ta’addan da suka addabi manoma da mazauna wasu ƙauyuka a Jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Nijeriya. Bayanai sun ce dakarun sojin na sama da ta ƙasa, waɗanda ke ƙarƙashin rundunar Operation Fasan Yamma da ke sintiri a Arewa maso Yamma domin kawar da masu tayar da ƙayar baya, sun hallaka sama da ’yan ta’adda 400 a yayin wannan samamen. Za a gyara tarbiyar tubabbun ’yan daban Kano Direba ɗaya ya tsira a hatsarin tankokin dakon iskar gas a Zariya Majiyoyi sun bayyana cewa ’yan ta’addan, waɗanda ke fakewa a dajin Makakkari tare da shugabanninsu daban-daban, sun dauki haramar kai hari kan wani ƙauye ne kafin sojojin su...
Lee ya kara da cewa, fifikon musammam da Hong Kong ke da shi karkashin manufar “kasa daya mai tsarin mulki biyu’, ya ba yankin damar jan hankalin masu zuba jari na ketare domin su lalubo damarmakin kasuwanci a yankin da ma kasuwar babban yankin kasar Sin tare da taimakwa kamfanonin babban yankin shiga kasuwannin ketare. Bugu da kari, ya ce kamfanonin waje da dama sun samu damarmakin kasuwanci a Hong Kong, kuma suna ci gaba da fadada harkokinsu. Su ma kamfanonin babban yankin kasar Sin sun aminta da karfin Hong Kong kuma suna hada gwiwa da tawagar dake Hong Kong wajen lalubo damarmakin dake akwai a kasuwanni masu tasowa na ketare. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa a gobe talata mataimakin shugaban hukumar makamashin nukliya ta duniya zai ziyarci kasar, amma ba tare da zuwa cibiyoyin nukliya na kasar ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa wannan shi ne ziyarar aiki na farko wanda wani jami’in hukumar ya kawo ziyara Tehran bayan yakin kwanaki 12 wanda HKI ta dorawa JMI. Gwamnatin JMI dai tana shakkan ma’amatar da hukumar, inda take ganin babu gaskiya a cikin mu’amalarta da ita, da farko saboda tabbacin cewa hukumar tana bawa makiyanta, musamman HKI wasu bayanai wadanda ta karba a wajenta dangane da shirinta na makamashin nukliya, inda HKI ta sami damar kashe masana fasahar nukliyar kasar da...
Gwamnatin kasar Iran ta bayyana cewa kasar Lebanon tana da hakkin kare kanta, kuma tana bukatar makaman kungiyar hizbullah don yin haka. Kumfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Ismail Bakae yana fadar haka a yau litinin ya kuma kara da cewa, gwamnatin kasar Iran ta yi imanin cewa gwamnatin kasar Lebanon tana bukatar makaman kungiyar hizbullah don kare kasar daga mamayar HKI. Sannan ya kammala da cewa batun tsaron kasar Lebanon wani abu ne na cikin gida kungiyoyin siyasa da kuma gwamnatin kasar suna iya tattaunawa a tsakaninsu don zabar hanyar da ta dace don kare kansu daga makiyansu. Musamman HKI wacce ta sha kokarin mamaye kasar amma suka kasa. Kungiyar hizbullah...
Sojojin Kasar Mali kimani 45 aka kama biyu daga cikinsu masu mukamin Janar a karshen makon da ya gabata a kokarin da suka yi na juyin mulki a kasar Shafin yanar gizo na labarai ;Afrika News: ya bayyana cewa daga cikin wadanda aka kama har da janar Abass Dembele, kuma tsohon gwamna na lardin Tsakiyar Mopti. Majiyoyi kusa da Abbas sun bayyana cewa sojoji sun kama shi ne a safiyar ranar lahadi a wajen birnin Bamako babban birnin kasar, ba tare da wani karin bayani ba. Har’ila yau labarin ya kara da cewa, Nema Sagara, mai mukaman brigadier General a sojojin sama na kasar, kuma mace wacce ba wanda ya fita mukami a sojojin kasar tana daga cikin wadanda aka...
Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran, Dr Ali Larijani ya gana da firai ministan kasar Iraki Mohammad Shia Assudani a birnin bagdaza inda bangarorin biyu suka tattauna al-amura da dama da suka shafi harkokin tsaro a tsakanin kasashen biyu da kuma matsalolin yankin wadanda suka hada da kasar falasdinu. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar iran ya bayyana cewa Dr Larijani ya gana da shugaban kasar ta Iraki Abdullataf Rashid da kuma Qasin al-araji mai bawa shugaban kasa shawara a kan al-amuran tsaron kasa. A gaban shugaban kasan ne Larijani da Araji suka rattaba hannu kan wata sabuwar yarjeniyar tsaro mai muhimmanci tsakanin kasashen biyu. Dr larijani ya yabawa kasar Iran a kokarinda take yi don tabbatar da...
Kashi 3/4 na kasashe mambobi a majalisar dinkin duniya sun amince da samar da kasar Falasdinu, mai zaman kanta tare da kasar Australia a yau Litinin ta bada sanarwan cewa zata shelanta amincewarta da kasar Falasdinu a matsayin mai zaman kanta a taron babban zauren mdd wana za;a gudanar a cikin watan Satumba mai zuwa. Shafin labarai na yanar gizo, Arab News na kasar saudiya ya bayyana cewa, yakin da kungiyar Hamas ta fara da HKI a ranar 7 ga watan octoban shekara ta 2023 ya jawowa Falasdinawa tausayi a mafi yawan kasashen duniya in banda ita HKI da kuma Amurka. Wadan nan kasashe sun yi Imani kan cewa Palasdinawa zasu sami yenci ne kawai a kan teburin tattaunawa. Sai...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya shawarci matasan da ake ribatarsu a matsayin ’yan daban siyasa da suka tuba da su guji tashin hankali, yana tabbatar musu da shirye-shiryen gwamnatinsa na gyara tarbiyarsu tare da mayar da su cikin al’umma. Gwamnan ya yi wannan alkawari ne a taron wuni ɗaya da aka gudanar tare da shugabannin rukunan ’yan daban da suka tuba a ƙarƙashin Shirin Safe Corridor. Direba ɗaya ya tsira a hatsarin tankokin dakon iskar gas a Zariya An kama mutumin da ake zargi da kashe jami’in sibil difens a Jigawa Gwamnan, wanda Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Waiya, ya wakilta, ya ce: “Ba za a sake ɗaukar makami da sunan fadan siyasa ko wasu munanan...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Fitaccen masanin tattalin arziki dan kasar Birtaniya John Ross, ya ce ma’aunin tattalin arziki na GDP na kasar Sin ya karu da kaso 5.3 bisa dari a mizanin shekara, cikin rabin farko na shekarar nan ta 2025, wanda hakan ke nuni ga ingancin tushen tattalin arzikin kasar. Ross, wanda ya bayyana hakan a baya-bayan nan, yayin zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua, ya ce Sin ta wanzar da managarcin yanayin zuba jari, tana kuma kara fadada jarin da ake shigarwa a fannin bincike da samar da ci gaba, tare da ingiza daga matsayin fasahohi, wanda hakan ya haifar da managarcin yanayi na bunkasa tattalin arzikin kasar. A cewar shaihun malamin, tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba...
Ma’aikatar kula da albarkatun kasa ta kasar Sin ta sanar a yau Litinin cewa, kasar ta kammala yin rajistar hakkin mallakar yankuna 5 na kare muhalli da halittu na kasar, a matsayin wani muhimmin mataki na daukaka aikin kare muhalli da halittu. Yankunan 5 na kasa sun hada da na Sanjiangyuan da na Giant Panda da yankin kare dabbar Tiger na arewa maso gabashin kasar wato the Northeast China Tiger da na kare Damisa da ake kira Leopard National Park da daji mai dumi da damshi na Hainan wato Hainan Tropical Rainforest da kuma yankin Wuyishan. Rajistar na bayyana ikon da matakai daban-daban na gwamnati ke da shi da bayyana hakkokin mallaka da aikin kula da yankunan da nauyin kula...
Jam’iyyar ADC ta zargi hukumar EFCC na yin son zuciya tare da yin aiki a matsayin kayan aikin siyasa ga jam’iyyar mai mulki APC. Jam’iyyar ta gargaɗin cewa irin wannan mataki yana rage ingancin yaƙin da ake da cin hanci da kuma rage amincewar jama’a. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar, ADC ta bayyana cewa ayyukan EFCC na baya-bayan nan, ciki har da buɗe tsofaffin shari’o’i da kuma maida hankali kan ƴan adawa, sun nuna halayyar kamar ta “mai aiwatar da umarnin siyasa” maimakon hukuma mai aiki da gaskiya. Ta kuma zargi hukumar da kiran wasu shugabannin adawa kan shari’o’in da suka dogara da tsoffin zarge-zarge na siyasa. UEFA...
A safiyar wannan Litinin ɗin ce aka wayi gari da wani mummunan hatsarin tankoki biyu na dakon iskar gas a Zariya, inda direba ɗaya kacal ya tsira da rai, yayin da wasu da dama suka ƙone ƙurmus. Shaidun gani da ido sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe tara na safe, a kusa da shatale-talen Jirgin Sama Mota da ke titin Kaduna zuwa Zariya, daura da sabuwar Kasuwar Ɗan Magaji. An kama mutumin da ake zargi da kashe jami’in sibil difens a Jigawa Ya ba wa alaramma kyautar motarsa saboda daɗin karatun Alkur’ani Rahotanni sun nuna cewa motocin biyu sun gogi juna ne yayin da ɗaya ke ƙoƙarin wuce ɗaya, lamarin da ya haddasa kamawar wuta nan take....
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna ta shawarci maniyyata aikin Hajjin shekarar 2026 da su fara shirin biyan kudaden ajiya. Kiran ya biyo bayan taron da Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta gudanar tare da hukumomin Alhazai na jihohi, inda aka bayar da shawarar ajiyar naira miliyan 8 da rabi ga masu niyyar zuwa aikin Hajji, kafin a sanar da hakikanin kudin aikin Hajjin shekarar 2026. A cikin wata sanarwa, mai magana da yawun hukumar, Yunusa Mohammed Abdullahi, ya shawarci wadanda ba su da fasfo da su gaggauta zuwa Hukumar Shige da Fice ta Kasa domin yin nasu, yana mai cewa shi ne ake amfani da shi wajen hada takardun tafiya. Najeriya ta sake samun kujeru...
Chen Xiaoguang ya bayyana cewa, dabarun da aka saba amfani da su na yaki da sauro suna da tasgaro. Ya ce tarko da gidan sauro na kama sauro ne marasa shan jini, yayin da tsarin kama sauro cikin mazubi da ruwa, ke kama sauro masu jan jini da yin kwai. Ya kara da cewa, abun da suka kirkiro na’ura ce dake gudanar da ayyuka biyu a lokacin da ake ciki, kuma tana da matukar inganci wajen sa ido da bibiyar sauro. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
Hukumar tsaro ta sibil difens (NSCDC) ta sanar da cafke wani mutum, Salisu Muhammad, mai shekaru 45, bisa zargin kashe jami’inta, Bashir Adamu Jibrin, a kasuwar Shuwarin da ke Karamar Hukumar Kiyawa a Jihar Jigawa. A cewar wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Muhammed Badarudeen ya fitar a Dutse, babban birnin jihar, lamarin ya faru ne a ranar kasuwa lokacin da marigayin yake gudanar da aikinsa. Ya ba wa alaramma kyautar motarsa saboda daɗin karatun Alkur’ani Tankokin mai sun yi bindiga a Zariya Rahotanni sun nuna cewa, ana zargin Salisu ya buga wa jami’in dutse a kai, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa. Hukumar ta ce ta kama wanda ake zargin ne a gidansa da ke Shuwarin...
Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) tare da haɗin gwiwar Gavi da ke taimakawa wajen samar da rigakafi, sun mika na’urorin samar da wutar lantarki ta hasken rana g Gwamnatin Jihar Kano domin amfani da su a cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko (PHCs) guda 28 da nufin ƙarfafa rigakafin yara da kuma kula da lafiyar jama’a. A yayin bikin mika kayayyakin ga gwamnatin jihar da Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Ƙasa (NPHCDA), Kwamishinan Lafiya na Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya ce wannan shiri na nufin taimaka wa yaran da ba a musu rigakafi, da mata masu juna biyu da ba su da damar samun rigakafin yau da kullum da kuma wasu ayyukan...
Kakakin NAF ya ce harin, an kai ne tare da hadin gwiwar runduna ta kasa, wanda ya yi sanadin mutuwar wasu fitattun ‘yan bindiga rundunarsu da dama. Daraktan ya kuma jadadda cewa hadin kai tsakanin sassan sama da na kasa na Operation Fasan Yamma ya sa farmakin ya zama na musamman. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta karɓi ƙarin kasafin kuɗi na shekarar 2025 daga bangaren zartarwa na jihar domin tattaunawa da amincewa. Bisa wasikar da bangaren zartarwa ya aika wa Majalisar, ana neman amincewar ta kan ƙarin kasafin kuɗi na kimanin Naira biliyan 170 domin aiwatar da muhimman ayyukan ci gaba a fadin jihar. Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Alhaji Jibril Isma’il Falgore, ya bayyana cewa bangaren zartarwa yana neman wannan ƙarin kuɗi ne domin gudanar da ingantattun ayyuka da za su amfani rayuwar al’ummar jihar. Bayan tattaunawa, ‘yan majalisar sun mika kudirin ga Kwamitin Majalisa kan Kasafin Kuɗi domin yin bincike da shirye-shiryen aiwatar da dokokin da suka dace. A wani labarin kuma, majalisar ta karɓi...
Wasu da ake zargin ‘yan ta’addar ISWAP ne sun kashe shugaban kungiyar mafarauta a kauyen Garjang da ke karamar hukumar Damboa a jihar Borno. Majiyoyi, a cewar Zagazola Makama, kwararre a fannin yaki da ‘yan tada kayar baya, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 5 na safiyar Lahadi. Kungiyoyin Kwadago Sun Tsunduma Yajin Aiki A Taraba Inganta Harkokin Gwamnati: Oyebanji Ya Sauke Kwamishinoni 19 Wanda aka kashe mai suna Habu Dala mai shekaru 53, ‘yan ta’addan ne suka dauke shi daga gidansa, inda suka bi da shi ta hanyar Mulharam zuwa kauyukan Forfot da ke karamar hukumar Damboa. An tattaro jama’ar kauye ne domin neman Dala amma daga baya suka tarar da gawarsa dauke da raunukan harbin...

Mahukuntan Iraki Sun Bayyana Cewa: Akwai Yiwuwar Masu Ziyarar Arba’een Na Imam Husaini {a.s} Zasu Zarce Miliyan 4
Birnin Karbala mai tsarki na sa ran karbar bakwancin masu ziyara sama da miliyan 4 daga kasashen ketare domin gudanar da juyayin Arbaeen Jama’a masu dimbin yawa na tururuwa zuwa birnin Karbala mai tsarki daga Najaf domin halartar yuyayin ranar Arbaeen a cikin tsauraran matakan tsaro da na hidima. Wakilin Al-Alam da ke kan titin Karbala Mo’ataz Al-Aboudi ya ruwaito cewa: Ana ci gaba da zirga-zirgar masu ziyarar Arbaeen lami lafiya duk kuwa da tsananin zafi a kan hanyoyin da ke kan hanyar zuwa Karbala. Wakilin na Al-Alam ya bayyana cewa: Birnin Karbala mai tsarki yana sa ran halartar masu ziyara sama da miliyan 4 daga wajen kasar Iraki, a cewar gwamnan Karbala Jassim Al-Khattabi. Ya yi nuni da cewa...
Sojojin mamayar Isra’ila sun harba wata mugunyar ‘karfin wuta’ da jiragen saman yaki kan yankin kudancin Gaza Bayan tsakar dare ne jiragen yakin sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kaddamar da luguden wuta a kudancin birnin Gaza. Cibiyar yada labaran Falasdinu ta nakalto majiyoyin da ta bayyana a matsayin na cikin gida na cewa: Jiragen saman sojin mamayar Isra’ila sun kaddamar da hare-haren wuce gona da iri, inda suka harba makamai masu linzami sama da 20 cikin ‘yan mintuna a kudancin mahadar Al-Musalaba da Dawla da kuma kusa da masallacin Ali, inda suka nufi kudu. Wakilin cibiyar ya ruwaito cewa, galibin hare-haren sun fi karkata ne a kan titin 8 da ke kudancin Gaza. Wadannan hare-haren dai na zuwa ne a...

Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya Ya Gudanar Da Zaman Taro Kan Aniyar ‘Yan Sahayoniyya Kan Gaza
Kasashen Turai biyar na kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya sun ki amincewa da matakin mamaye Gaza Wakilin dindindin na Slovenia ya gabatar da wata sanarwa ga kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya a madadin Burtaniya, Faransa, Denmark, da Girka, yana mai cewa: “A matsayinsu na kasashen Birtaniya, Denmark, Faransa, Girka, da Slovenia, sun kira taron gaggawa na kwamitin tsaron Majalisar kan halin da ake ciki a Gaza. Suna Allah wadai da matakin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta dauka na fadada ayyukanta na soji a Gaza. Ya kuma jaddada cewa: Hakan yana barazana tare da keta dokokin kasa da kasa, yana mai kiran gwamnatin mamayar Isra’ila da ta hanzarta janyewa daga wannan matsayi. Ya jaddada cewa: Duk wani matakin mamaye yankunan Falasdinawa...
Wani mutum ya ba da kyautar motarsa da ita kadai gare shi ga wani mai jan baki (alaramma) saboda ƙwarewarsa a haddar Al-kur’ani. Malam Yusuf Ɗan-Birni, ya kyautar da motar ce a taron wa’azin wata-wata da Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa Iƙamatis Sunna (JIBWIS) ta shirya a garin Kubwa da ke yankin Babban Birnin Tarayya. Malam Yusuf Ɗan-Birni wanda ke sana’ar gyaran waya, ya bai wa jama’a mamaki a yayin da ake tsaka da karatun da misalin ƙarfe 10 nan dare inda ya miƙa makullan motarsa ga mai gabatar da wa’azin, Sheikh Mahmud Assalafi, ya sanar da shi cewa ya kyautar da ita ga majabaƙinsa, Alaramma Usman Nasidi Gusau. Wani ganau mai suna Malam Nuhu Abu-Huzaifa ya shaida wa Aminiya...
Kungiyar Kwadago da ta ‘yan kasuwa ta Nijeriya (NLC da TUC) reshen jihar Taraba sun bayyana shirin fara yajin aiki tun daga karfe 12 na daren Litinin 11 ga watan Agusta, 2025. Wannan mataki ya biyo bayan sakamakon taron majalisar zartarwa ta jihar da kungiyoyin biyu suka yi a ranar Lahadi a Jalingo, babban birnin jihar Taraba. A cikin sanarwar da LEADERSHIP ta samu a daren Lahadi mai dauke da sa hannun sakataren kungiyar NLC, Adamu-Buba, da sakatariyar kungiyar TUC, Polina Gani, sun yi kira ga mambobinsu da su ba da hadin kai ga matakin da kungiyoyin suka dauka domin neman hakkokinsu a wurin gwamnatin jihar ta Taraba. Kungiyar kwadagon ta ce, taron ya sake duba wa’adin da aka bayar...
Wasu manyan motocin dakon sun yi bindiga a yankin Ɗan Magaji da ke Ƙaramar Hukumar Zariya a Jihar Kaduna. Ana fargabar mutuwar mutane da dama sakamakon gobarar tankokin man bayan sun yi hastari a safiyar Litinin. Shaidu sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:30 na safe a kusa da Makarantar Rochas Foundation, kan titin Kaduna–Kano bypass daga Kwangila zuwa Dan Magaji. Hatsarin ya haɗa da manyan motoci biyu masu ɗauke da man fetur da kuma motoci biyu ƙirar Golf ɗauke da fasinjoji. A sakamakon haka, tankokin biyu suka yi bindiga, wanda ya tayar da wutar gobara mai ƙarfi tare da hayaƙi mai kauri ya lulluɓe hanyar. Jami’an ceto da tsaro sun rufe hanyar, tare da gargaɗin direbobi...
Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta kashe wani fitaccen dan jarida na kafar yada labarai ta Al Jazeera Anas al-Sharif tare da abokan aikinsa hudu a wani hari da ta kai Gaza. Isra’ila ta zarge shi da kasancewa wani jagora na Hamas sannan ta ce ta hallaka shi saboda irin rahotannin da yake bayarwa masu tsanani daga arewacin Gaza. Isra’ila ta hari ‘yan jaridar biyar – Anas al-Sharif wanda shi ne fitacce tare da Mohammed Qreiqeh masu aikawa da rahotanni ne sai kuma masu daukar musu hoto Ibrahim Zaher da Mohammed Noufal da kuma Moamen Aliwa wadanda dukkanin su suna aiki ne da kafar ta Al Jazeera. A lokacin da Isra’ila ta kai musu harin ta sama suna cikin wani...
’Yan ta’adda sun kashe mutum 24 tare da sace wasu akalla 144 a cikin mako guda a sassan Jihar Zamfara. Kungiyar Al’ummar Zamfara mai suna Zamfara Zamfara Circle Community Initiative ta bayyana cewa ’yan ta’addan sun kai hare-haren da suka kai kan kauyuka 15 inda suka jikkata mutane 16 a kananan hukumomi daban-daban. Ta bayyana cewa daga ranar 4 zuwa 10 ga watan nan na Agusta, 2025 ’yan ta’adda suka kai hare haren; kauyukan da aka kai wa farmakin sun hada da Sabe, Tungar Yamma, Sauru, Lambasu, Dogon Madacci, Dankalgo, da Kwanar Kalgo a ƙaramar hukumar Bakura. A Karamar Hukumar Tsafe, hare-haren sun shafi Chediya, Kucheri, Yankuzo, da Katangar Gabas Bilbils. A Karamar hukumar Mafara, an samu rahoton hare-hare a...
A ci gaba da gudanar da bukukuwan makon shayarwa da nonon uwa na duniya, asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF ya shirya tarurruka a Kano tare da hadin gwiwar U-Reporters da sauran kungiyoyin matasa domin wayar da kan al’umma kan amfanin shayarwa. An gudanar da gangamin a lokaci guda a wurare daban-daban a fadin jihar, wadanda suka hada da Dangi Roundabout, KSIP Roundabout dake kan titin Ahmadu Bello, Central Road, Triumph Roundabout, Legas Street, Hotoro Roundabout dake Gabashin Bypass, Gidan Gwamnati dake kan titin Jiha, da Kasuwar Abubakar Rimi. Sauran wuraren sun hada da Kofar Gadon Kaya, Kofar Nasarawa, Gadar Lado dake kan titin Zaria, da Unguwar Kasuwar Yankaba dake kan titin Hadejia. ...
Gwamna Oyebanji ya godewa ‘yan majalisar zartarwar jihar da abin ya shafa tare da yi musu fatan samun nasara a ayyukansu na gaba. Sai dai, umarnin bai shafi babban Lauyan jihar da kwamishinan shari’a ba. Har ila yau, daga cikin wadanda sallamar ba ta shafa ba, akwai Kwamishinonin Lafiya da Ayyukan Jama’a, Noma da Tattalin Abinci da Ayyuka. Bugu da kari, kwamishinan ciniki, saka hannun jari, masana’antu da kungiyoyin hadin gwiwa; Mai ba da shawara na musamman kan Ilimin masu bukata ta Musamman; da mai ba da shawara na musamman kan tsare-tsaren kasa, duk suna nan kan mukamansu. Haka kuma, duk Daraktocin da ke cikin majalisar zartarwa ta Jihar, za su ci gaba da rike mukamansu....
Gwamna Mohammed Umar Bago na jihar Neja, ya kaddamar da aikin sarrafa man kade tan dubu talatin a karamar hukumar Mokwa ta jihar tare da alkawarin samar da muhallin kasuwanci don bunkasa. Wani wuri mai daraja na duniya, wanda Salid Agriculture Nigeria Ltd ya gina kuma bankin NEXIM PLC zai samar da shi zai kawo sauyi ga tattalin arzikin matan karkara, kananan manoma, da kuma tattalin arzikin jihar Neja. Gwamna Mohammed Umar Bago ya samu rakiyar Dr. Aliyu Sabi Abdullahi, Ministan Noma, Abba Bello, MD/Shugaban Bankin NEXIM, Alhaji Ali Sa’idu, MD/Shugaba na Salid Agriculture Nigeria Ltd da tsohon Gwamnan Bayelsa da kuma fitattun iyayen gidan sarauta da suka hada da mai martaba Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar da...
Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta cafke wasu mutane shida da ake zargin ‘yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane ne a karamar hukumar Doma da ke jihar. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar SP Ramhan Nansel ya bayyana haka a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a lafiya, ya ce jami’an sun kuma kama wani makiyayi dauke da makamai a karamar hukumar Keana ta jihar. Sanarwar ta ce, jami’an sashin Doma da ke aiki da sahihan bayanan sirri daga wani dan kasa mai kishin kasa, karkashin jagorancin jami’in ‘yan sandan shiyya, sun kai samame a wata maboyar ‘yan ta’adda da ke Yelwa Ediya inda aka kama wadanda ake zargin. ...
Kungiyar Muslim Media Watch Group ta Najeriya ta yi Allah-wadai da wata sanarwa da ake zargin Bishop David Oyedepo kan amfani da hijabi da daliban Musulman Jami’ar Landmark ta Omu-Aran ta Jihar Kwara suka yi. A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun wakilinta na kasa Sheikh Abu Sheriff, kungiyar ta yi Allah wadai da Bishop David Oyedepo da take hakkin dalibai musulmi da ma’aikatan cibiyar da ke da hakkin dan Adam kamar yadda sashe na 38 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya tabbatar. A cewarsa a cikin wani faifan bidiyo da aka yada sosai, Oyedepo ya yi kira ga iyaye da masu kula da Musulmai da su janye ‘ya’yansu mata idan suka dage ba za ayi amfani...
Mahalarta taron masu ruwa da tsaki na yini daya don tabbatar da sakamakon bincike kan al’amuran zamantakewa da suka shafi ilimin ‘ya’ya mata a jihar Zamfara, sun bukaci iyaye, shugabannin al’umma, da gwamnati a dukkan matakai da su magance matsalolin da ke hana yara mata zuwa kammala karatun sakandare. Kungiyar AGILE da ke Jihar Zamfara tare da hadin gwiwar Media and Publicity Consult ta shirya taron masu ruwa da tsaki na rana daya domin tabbatar da sakamakon binciken da aka yi kan ka’idojin zamantakewa da ke kawo cikas ga ’yan mata matasa da ke hana shiga makarantun gaba da sakandare a jihar Zamfara. Da yake jawabi a wajen taron, Farfesa Abubakar Aliyu Liman na Jami’ar Ahmadu Bello da...
Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta ce ta karfafa matakan tsaro a yankin Babanla biyo bayan harin da wasu da ake zargin mahara ne suka kai musu, inda suka kashe mutane 5 ciki har da dan sanda Adejumo Wasiu. A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, SP Adetoun Ejinre-Adeyemi ya fitar, ya ce ‘yan fashi da makami da yawansu ya kai daruruwa, a kan babura, sun mamaye al’ummar Babanla a karamar hukumar Ifelodun. A cewarsa wadanda ake zargin sun kai hari ne a hedikwatar ‘yan sanda inda suka kai farmaki cikin kasuwar. Ya bayyana cewa maharan sun yi ta harbe-harbe kai-tsaye, inda suka kashe mutane 5 ciki har da dan sanda...
Gwamnatin Tarayya ta yi hasashen ruwan sama mai karfi da zai iya haifar da ambaliya a jihohi 15 na Arewacin Najeriya da wasu wurare 68, a cikin kwanaki biyar masu zuwa. Wannan gargadi ya fito ne daga Cibiyar Lura da Gargadin Ambaliya ta Kasa, karkashin Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya, inda aka bukaci hukumomi da al’umma su dauki matakan gaggawa don kare rayuka da dukiyoyi. Cibiyar ta bayyana jerin jihohi da wuraren da ambaliyar za ta iya shafa sun hada da: Adamawa: Jimeta, Mubi, Mayo-Belwa, Wuro-Bokki, Yola, Farkumo Bauchi: Jama’a Nasarawa: Keffi Kaduna: Jaji, Kafanchan, Zaria, Birnin-Gwari Katsina: Katsina, Bindawa, Kaita Kebbi: Kamba, Kangiwa, Kalgo, Ribah, Sakaba, Saminaka, Gwandu, Jega, Bunza, Birnin Kebbi, Bagudo, Argungu Kano: Bebeji, Gwarzo, Karaye, Sumaila, Tundun-wada...
Sanarwar ta zayyana wasu fitattun garuruwa da al’ummomin da ka iya fuskantar mummunar ambaliyar ruwa da suka hada da Jimeta, Mubi, Keffi, Kafanchan, Birnin Kebbi, Minna, Gusau da Sakkwato. A cikin jihohin da aka lissafa, Kebbi ce ta fi kowacce yawan garuruwa da aka fi tsammanin ambaliyar za ta yi kamari, ga su guda 10 kamar yadda ta bayyana: Kamba, Kangiwa, Kalgo, Ribah, Sakaba, Saminaka, Gwandu, Jega, da Birnin Kebbi. Bokani ya bukaci mazauna yankin da hukumomin jihar da su dauki matakan kare rayuka da dukiyoyi cikin gaggawa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin...
Kakakin ofishin jakadancin kasar Sin a kasar Birtaniya, ya soki kalaman da kasashen kungiyar G7 suka yi, dangane da ganin baiken ‘yan sandan yankin HK, bayan da a ranar 25 ga watan Yuli da ya shude, ‘yan sandan suka fitar da takardar sammacen cafke wasu mutane 19, masu yunkurin haifar da tashin-tashina a kasar Sin da suka tsere zuwa kasashen ketare. A ranar Asabar ne ofishin jakadancin na kasar Sin a Birtaniya, ya yi tir da kalamai marasa ma’ana da kasashe membobin kungiyar G7, ciki har da Birtaniya suka furta kan batun, yana mai cewa, wasu kasashe tsiraru ciki har da Birtaniya, sun tsoma baki a batun dokar tabbatar da tsaro, wadda ‘yan sandan yankin musamman na HK ke aiwatarwa,...

Sin Ta Gudanar Da Gwajin Farko Na Gagarumin Bikin Murnar Cika Shekaru 80 Da Cimma Nasarar Yakin Kin Jinin Harin Dakarun Japan
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Cikin shekaru 20 da suka gabata kawo yanzu, kasar Sin ta himmatu wajen gina tsarin tattalin arziki mai kiyaye muhallin halittu, da ingiza sabon karfi da fifikon bunkasa kai, karkashin tsarin kare muhalli bisa matsayin koli. Wani rahoton hadin gwiwa na cibiyar kwararru ta Xinhua dake karkashin kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua, da cibiyar bincike game da tunanin shugaba Xi Jinping dangane da wayewar kai ta fuskar kare muhallin halittu ne ya bayyana hakan. Rahoton da aka fitar a yau Lahadi, mai taken “Kyakkyawan ruwa, da tsaunuka masu ban sha’awa, da Sin da duniya masu kayatarwa: Yanayin wayewar kan Sin ta fuskar kare muhallin halittu, da ayyukan da kasar ke gudanarwa a fannin, da yadda take zaburar da...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Damina lokaci ne da ɗan Adam yake matuƙar bukata. Da za ta yi jinkiri, sai a ga hankalin kowa ya tashi. A lokaci guda kuma, yadda damina kan hana wasu harkoki gudana kan jefa wasu mutane cikin wani irin yanayi. NAJERIYA A YAU: Shekara nawa shugabanni ke bukata don cika alkawuran zabe? DAGA LARABA: Me Ke Sa Matasa Zama Karnukan Farautar ‘Yan Siyasa A Kafafen Sadarwa Na Zamani? Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan yadda damina kan shafi rayuwar ƙananan ’yan kasuwa da masu ƙananan sana’oi. Domin sauke shirin, latsa nan
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce dole ne dukkan kasashen duniya su yi kokarin kawo karshen laifukan da Isra’ila ke aikatawa a zirin Gaza da kuma kawo karshen killacewa da take yi wa yankin. Pezeshkian ya bayyana hakan ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin da yake karbar takardar shaidar sabbin jakadun kasashen Habasha, Estonia, Djibouti, Laos, Cambodia, Burundi, Latvia, Myanmar, da Nepal. Ya ce gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana ci gaba da kara zafafa laifukan da take aikatawa a kan al’ummar Palastinu marasa kariya da ake zalunta a zirin Gaza. Shugaban na Iran ya jaddada cewa: Dole ne dukkan kasashen duniya musamman kasashen musulmi su kara himma da hadin gwiwa wajen dakile wadannan laifuka a Gaza, da...
‘Yan jarida 4 Anas al-Sharif da Mohammad Qraiqea, da masu daukar hoto Mohammad Nawfal da Ibrahim Daher sun shahada a wani harin da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kai kan wani tantin ‘yan jarida a arewacin zirin Gaza. Anas al-Sharif, shahharen dan jarida wanda ya sha bayar da rahotonnai da suke fallasa ayyukan kisan kare dangi da Isra’ila take aikatawa kan fararen hula a Gaza, lamarin da ya Sanya sojojin Isra’ila farautar rayuwarsa. A baya Isra’ila ta bayyana cewa Anas mamba ne na kungiyar Hamas kuma kwararre a bangaren makaman kungiyar, a kan yana daga cikin wdanda take dako. Kwamitin Kare ‘Yan Jaridu (CPJ) ya fitar da wata sanarwa a ranar 24 ga Yuli, 2025, inda ya ce al-Sharif na fuskantar...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa “babu wani abu da aka yanke ya yanzu game da tattaunawa da Amurka,” ya kara da cewa “babu wani tabbci kan zabar wata kasa da za ta karbi bakuncin tattaunawar.” A jawabin da ya yi a gefen taron majalisar ministocin a jiya Lahadi, Araqchi ya yi jawabi kan ziyarar mataimakin babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA wanda ke shirin isa birnin Tehran a yau litinin. Araqchi ya bayyana cewa “babu wani shiri na ziyartar wata tashar nukiliya kafin a cimma wata matsaya kan hakan,” ya kara da cewa wannan tsarin “zai dogara ne kan dokar majalisar dokokin kasar Iran kawa,” kuma “ba za a fara wasu...
Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da zaman gaggawa a hedikwatar MDD da ke birnin New York a jiya Lahadi, bayan matakin da majalisar ministocin Isra’ila ta dauka na fadada ayyukan soji da kuma mamaye yankin zirin Gaza. Mataimakiyar Sakatare-Janar mai kula da harkokin Turai, Tsakiyar Asiya da Amurka, Miroslav Jenča, ta jaddada a yayin zaman cewa, “ba za a iya dakatar da dimbin wahalhalun jin kai da ake fama da su a Gaza ba, sai ta hanyar tsagaita bude wuta nan take kuma mai dorewa,” tana mai kira da a gaggauta sakin dukkan fursunoni ba tare da wani sharadi ba. Jenča ta yi kira ga Isra’ila da ta bi abin da ya rataya a wuyanta a karkashin...
Jami’an tsaron kasar Iraki sun sanar da gano wata kungiyar ‘yan ta’adda da ta yi niyyar kai wa masu ziyarar Arbaeen hare-hare, wanda aka shirya gudanarwa a kwanaki masu zuwa. Ma’aikatar tsaron ta bayyana cewa, “tsarin da ‘yan ta’addan ke da shi sun hada da dasa ababen fashewa a kan hanyoyin da masu tattaki ke bi a yankin kudancin kasar da kuma saka guba a cikin kayan abinci da ake ba wa masu tattaki. Har ila yau, bincike ya nuna cewa kungiyar ta’addanci ta ISIS ta yi amfani da hanyoyi daban-daban wajen daukar wadannan mambobi nata da aka wanke wa kwakwalwa domin aiwatar da wadannan ayyuka. Ma’aikatar ta bayyana cewa, kungiyar na yin hakan ne ta hanyar yin amfani littafai...
“Na taɓa zama abar kwatance, musamman a ɓangaren da shafi kuɗi, suna, girmamawa, amma kuskuren da na yi ya zama dalilin da yasa masana’antar ta juya min baya, sakamakon babu abin da na iya ko na sani face; harkar ta fim. Halin da ake ciki yanzu, babu wani tallafi, babu aikin yi, akwai lokacin da ina da ɗimbin masoya da suke son aurena da kuma nuna min soyayya, amma sai na kasa zaɓen wanda zan ci gaba da rayuwata da shi a wancan lokaci. Babban dalilin da ya jawo min koma-baya a harkar fim shi ne, hatsarin da na samu na mota, wanda Allah ya jarrabce ni da shi, na yi hatsarin mota da har sai da na samu karaya...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rahotanni daga sojojin da ke mulki a Mali, sun ce sun kama wasu sojoji kusan 30 da ake zargin suna shirin kifar da gwamnati ƙasar. Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa cikin waɗanda aka kama akwai Janar Abass Dembele, tsohon gwamnan yankin Mopti da ke tsakiyar ƙasar. Ma’aikatan shari’a 97 sun samu ƙarin girma a Borno EFCC ta kama ’yan damfara a ɗakin karatun Obasanjo Har yanzu gwamnatin ƙasar ba ta fitar da sanarwa a hukumance ba game da lamarin. Ita ma gwamnatin da ke mulki yanzu ta karɓi mulki ne ta hanyar juyin mulki a shekarar 2021. Wannan zargi ya ƙara nuna cewa akwai rashin kwanciyar hankali a tsakanin gwamnatin sojin. Yanzu haka dai gwamnatin na fuskantar matsalar hare-haren masu...
“Duk da cewa jama’a suna da ‘yancin nuna sha’awarsu kan siyasa, shirye-shiryen amincewa, yunƙurin tattarawa, da tallace-tallace irin na kamfen da nufin tallata ‘yan takara kafin lokacin yaƙin neman zaɓe na hukumance ba a amince da su ba. “INEC tunin ta nusar da wannan batun a lokacin ganawarta da jam’iyyun siyasa, ta kuma gargaɗin dukkanin ‘yan siyasa da su bi dokoki da ƙa’idojin zaɓe,” sanarwar ta shaida. Ya buƙaci ‘yan siyasa da magoya bayansu da su mutunta matakan zaɓe tare da jiran jadawalin yadda zaɓen zai gudana a hukumance kafin su fara harkokin yaƙin neman zaɓe. Wannan gargaɗin dai na zuwa ne yayin da ake ƙara samun yadda jama’a suke ayyana goyon bayan tazarcen Shugaban ƙasa Bola Tinubu da kuma...
Wata kotu a kasar Chadi ta daure tsohun firai ministan kasar Succes Masra shekaru 20 a gidan kaso da taran caifa biliyon guda a jiya Asabar. Shafin yanar gizo na Labarai Afrika Newas ya kara da cewa kotun ta tabbatar da laifin kan dan siyasar, kuma dan adawa da gwamnatinn Debi, da laifin watsa wasu kalaman batanci da raba kan mutane, har ila yau da hannu cikin rigimar Mandakao ina ya kai ga rasa rayuka masu yawa. A cikin watan Mayun da ya gabata. Lawyan dan siysan ya bayyana rashin amincewa da hukuncin, ya kuma bayyana cewa an yi amfani da sharia don warware matsalar siyasa ne kawai. Akai wasu mutane 74 wadanda suka gurfana a gaban kotun dangane da...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abba Aragchi ya bayyana cewa kara karfin da dangantaka tsakanin Iran da Saudia yake yi, yana taimakawa zaman lafiya a yankin. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar iran ya kara da cewa Aragchi ya bayyana haka ne a lokacinda ya gana da jakadan kasar Iran a Saudiya Ali Reza Enayati a jiya Asabar a nan Tehran. Jakadan ya gabatarwa ministan rahoto kan inda dangantaka tsakanin Iran da saudiya yake. A na shi bangaren ministan ya bayyana kara karfin da dangantaka tsakanin kasashen musulmi biyu yana taimakawa da zaman lafiya mai dorewa a yankin. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name*...
Babban mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae shawara, wato Ali Akbar Wilayati ya bayyana cewa Iran zata hana America samar da hanya a yankin Caucasus, ko da kasar rasha ta taimaka ko bata taimaka ba. A wata hira na musamman da kamfanin dillancin labaran Tasnim, Ali Akbara wailayati ya yi watsi da wani shiri wai shi zangezur wanda an tsara zai hana kasar Armenia da Nakhchivan. Da aka tambaye shi da maganar cewa Armenia zata bawa Amurka yankin haya na tsawon shekaru 99 masu zuwa, Wilayati ya bayyana cewa warin zai zama makabartan sojojin Donal trump, wannan ba hanya ce wanda Amurka ta mallaka ba. Ya ce gwamnatin kasar Iran ta sha bayyana cewa bata...
Sojojin HKI sun shiga yankuna da dama a lardin Qunaitara na kasar Siriya a Jiya Asabar. Inda ta kafa shingaye a kan tituna a wasu garuruwa a lardin suka yi ta binciken ababen hawa, kafin su janye daga baya. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, HKI tana shirin mamayar wadan nan yankunan na kasar Siriya shi ya sa bata son ganin an sami zaman lafiya a kasar ta Syriya gaba daya, har zuwa lokacinda zata mamaye yankin. Gwamnatin kasar Siriya mai ci ta tabbatar da cewa samuwar sojojin HKI a duk lokacinda suka ga dama a wadannan yankuna alamace ta rashin zaman lafiya a kasar. Kowa ya san cewa HKI ba zata taba barin kasar Siriya...
Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta bada sanarwan cewa alkalan wasan kwallon kafa ta mata kuma ta Salon guda biyu ne ta zama a kasar Iran don alkalanci a gasar FIFA ta kwallon Saloon ta masa na wannan shekara ta 2025, wanda za’a gudanar a kasar Philipine. Zaben Zari Fathi da kuma Gelareh Nazemi a matsayin alkalai a wannan gasar mai muhimmanci ya nuna irin matsayinda Iran take da shi a hukumar ta FIFA. A ranar 21 ga watan Nuwamba mai zuwa ne, zuwa 2 ga watan Decemban shekara ta 2025 ne za’a gudanar da gasar kwallon salon ta mata da kuma duniya a biranen Manila da Negros,na kasar Philipine. Inda kungiyoyin kwallon kafa ta mata 16 daga kasashen...
Amma saboda yanzu yanayin rayuwa ya canza, ba ni da mota ko ɗaya; ya sa idan na yi waccan maganar sai wasu su riƙa nuna rashin amincewarsu, wannan kuma rashin sani ne kawai, domin kuwa da a ce sun san wane ne Mai Dawayya a shekarun da suka gabata, da ba su yi wannan magana ba, koda kuwa da wasa, in ji shi. Mai Dawayya ya buƙaci matasan mawaƙa masu tasowa a masana’antar ta Kannywood, da su tabbatar sun yi amfani da wannan lokaci da suke kan ganiyarsu, duniya kuma take yi da su; wajen gina gobensu, ba wai su dinga hawan motoci da sauran sharholiyar rayuwa ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
Ƴan bindiga sun kashe mutane biyar, ciki har da wani Ɗansanda, a sabon harin da suka kai garin Babanla a ƙaramar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara. Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, kwanaki ƙalilan bayan kisan wasu matafiya uku da garkuwa da wasu biyu a yankin. Mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar, Toun Ejire-Adeyemi, ta ce maharan sun kai ɗaruruwa akan babura ne suka farmaki garin, kuma suka kai hari ofishin Ƴansanda na yankin, sannan suka yi ɓarna a kasuwar garin. An kashe Kofural Adejumo Wasiu tare da wasu fararen hula huɗu. NDLEA Ta Kama Fasto Bisa Laifin Safarar Miyagun Kwayoyi A Legas Jirgin Shugaban Ƙasa Ya Laƙume Naira Biliyan 26.38 Cikin Wata 18 Ƙarƙashin Tinubu Ta bayyana...
Hukumar Shari’a ta Jihar Borno ta ƙara wa ma’aikatanta 97 girma bayan wani taro na kwanaki huɗu da ta gudanar a Maiduguri. Muƙaddashin sakataren hukumar, Saleh Khala Jidda ne, ya bayyana hakan a wata sanarwa cewa ma’aikatan sun samu ƙarin girma ne saboda ƙwazonsu. EFCC ta kama ’yan damfara a ɗakin karatun Obasanjo ’Yan bindiga sun kashe gomman mutane a ƙauyukan Sakkwato Waɗanda abin ya shafa sun hada da Majistare 10 daga matakin Majistare mataki na ɗaya zuwa Babban Majistare mataki na biyu. Sai Majistare daga matakin farko zuwa Babban Majistare na biyu. Sauran sun haɗa manyan Magatakarda daga mataki na ɗaya zuwa na biyu. Sai dai a gefe guda, hukumar ta ɗauki mataki kan wani alƙalin Babban Kotun Majistare...
Wakilan LEADERSHIP sun lura cewa yanzu ana amfani da wasu daga cikin waɗannan ofisoshin hulɗa da jama’a na Jihar Legas a matsayin matsugunin ‘yan kasuwa na da masu safarar barasa. Binciken da aka yi ya kuma nuna cewa jami’an tsaro da masu kula da waɗannan gidaje suna hayar wasu sassan gine-ginen da daddare don yin haramtattun ayyuka, inda suka mayar da su gidajen karuwai. Lamarin dai ya haifar da fargaba a tsakanin mazauna yankin da kuma ‘yan kasuwa a yankunan da ke maƙwabtaka da su, inda suka ce ayyukan na da matuƙar haɗari ga tsaro, suna jawo masu aikata laifuka, da kuma zubar da mutuncin wakilan Jihar a Legas. Lamarin dai ya haifar da fargaba a tsakanin mazauna yankin da...
Jami’an tsaron kasar Iran sun murkushe ‘yan ta’adda da suka kai hari a ofishin ‘yan sanda a kudu maso gabashin kasar Wasu ‘yan ta’adda da ake kira “Rundunar Shari’a” sun yi yunkurin kai farmaki ofishin ‘yan sanda na Saravan da ke lardin Sistan da Baluchestan na kasar Iran a wani tsararren harin wuce gona da iri kan jami’an tsaron Iran, amma jami’an tsaron da aka tura domin kalubalantansu sun yi nasarar mayar da martani mai gauni kan ‘yan ta’addan. A cewar majiyoyin Iran, an kashe ‘yan ta’adda uku tare da kame biyu a wadannan gumurzun. Wani dan sanda mai suna Khodadad Baqiri Saravan ya yi shahada a wani artabu da gungun ‘yan ta’adda a birnin Saravan. Share 0 0 votes...
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da matakin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta dauka na mamaye zirin Gaza Ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da matakin baya-bayan nan da majalisar ministocin gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta dauka na mamaye yankin zirin Gaza da korar al’ummarta, tare da la’akari da hakan a matsayin wani mataki na kammala shirin kisan gillar ga Falasdinawa da suke yi da kawar da asalin wanzuwar Falastinu. A cikin bayanin da ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fitar dangane da abubuwan da suke faruwa a zirin Gaza da yankunan Falastinu da aka mamaye, ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana matukar damuwarta da takaicin yadda ake ci gaba da...
Jami’in ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa; Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cimma babban matsayi a yakin kwanaki 12 Ali Baqiri Kani mamba a majalisar tsare-tsaren a ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cimma babban matsayi a yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa da yahudawan sahayoniyya. Baqiri ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi ta gidan talabijin a yammacin jiya Asabar cewa: Tabbas Iran ta cimma matsayi sosai a yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa, yana mai jaddada muhimmancin diflomasiyya wajen tunkarar hare-haren da ake kai wa kasar, yana mai jaddada cewa: “Dole ne Iran ta mayar da martanin wuce gona da iri...
A kokarin ta na ci gaba da kula da harkokin ilimi a yankin, Karamar Hukumar Birnin Kudu dake Jihar Jigawa ta kaddamar da aikin tantance malaman makaranta na B teach da kuma ma’aikatan lafiya na wato B health. A jawabin sa wajen fara tantance malaman da ma’aikatan lafiyar, Shugaban karamar hukumar, Dr Muhammad Uba Builder, yace aikin tantancewar ya zama wajibi domin tabbatar da ma’aikata na gaskiya da kuma gano na bogi. Yana mai cewar akwai rahotannin daya nuna wasu suna aiki 2 wasu kuma suna amfani da takardun bogi. A don haka, yace duk wanda aka samu da hakan zai rasa aikin sa gami da kama shi don fuskantar hukunci. Builder Muhammad Uba, yace an...
Jami’an Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), sun kai samame a Ɗakin Karatun Olusegun Obasanjo da ke Abeokuta, a Jihar Ogun, inda suka kama wasu matasa da ake zargin ’yan damfara ne. Samamen ya faru ne da safiyar ranar Lahadi a sashen otal na ɗakin karatun. ’Yan bindiga sun kashe gomman mutane a ƙauyukan Sakkwato An ɗaure tsohon Firaminista Succes Masra shekaru 20 a Chadi Gidan Obasanjo na musamman yana cikin harabar ɗakin karatun. Wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, ya nuna yadda wasu matasa ke gudu domin ka da EFCC ta kama su. Rahotanni sun ce jami’an EFCC sun ƙwace sama da motoci 20 tare da wasu kayayyaki masu daraja. Wani jami’in...
An sake shiga tashin hankali a Jihar Sakkwato bayan wani sabon mummunan hari da ’yan bindiga suka kai a wasu kauyuka, lamarin da ke ƙara tsananta matsalar tsaro a faɗin jihar. Rahotanni sun nuna cewa duk shekara musamman a lokacin damina, ’yan bindiga sukan ƙara ƙaimi wajen kai hare-haren da ke tarwatsa jama’a a garuruwansu da hana manoma zuwa gona ko kuma ƙaƙaba musu harajin zuwa gonakin. An ɗaure tsohon Firaminista Succes Masra shekaru 20 a Chadi Dan wasan Barcelona Inigo Martinez ya koma Al-Nassr Aminiya ta ruwaito cewa, a bana ma, maharan sun ci gaba da addabar mazauna ƙananan hukumomi 20 daga cikin 23 na Jihar Sakkwato. Majiyoyi sun tabbatar cewa a harin baya-bayan nan, ’yan ta’addan sun hallaka...
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta kama wanda ya kafa kuma yake kula da cocin ‘The Turn of Mercy’, Adefolusho Olasele, wanda aka fi sani da Abbas Ajakaiye, bisa zarginsa da hannu wajen safarar miyagun kwayoyi da dama daga Ghana zuwa Nijeriya. Fasto Olasele, wanda ya shafe watanni ba a san inda yake ba, an kama shi ne a ranar Lahadi, 3 ga watan Agusta, 2025, a cocinsa da ke Okun Ajah, yankin Lekki, a Legas. NDLEA Ta Cafke Masu Baburan Da Ke Kai Saƙon Muggan Ƙwayoyi A Abuja Dole Ne Afrika Ta Mayar Da Hankali Wajen Amfana Da Damarmakin Da Ke Tekunanta – Ɗantsoho Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Femi...
dimokuradiyya ta hanyar ba da umarni ga manyan wadanda ya nada na arewa su halarci taron. “Wannan aiki daya na sadaukarwar da shugaban kasa ya yi don tattaunawa da mutane Yana ishara da cewa, ba wai isa ce kadai a kan iya siyasa ba har ma da isa matuka wajen mutunta ka’idojin dimokuradiyya. Mahalarta taron sun hada da; Sakataren Gwamnati na Tarayya, Sanata George Akume, Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro Malam Nuhu Ribadu, Babban Hafsan Hafsoshin Tsaro Janar Christopher Musa, Hafsan Hafsan Sojin Sama Hassan Bala, Kwamanda Janar na NSCDC Dr. Ahmed Abubakar Audi, Shugaban Gwamnonin Arewa, Mai Girma Gwamna Inuwa Yahaya, Mai Girma Gwamnan Jihar Kwara Da Shugaban Kungiyar Gwamnonin Nijeriya Hon. Abdulrazak...
Wata kotu a N’Djamena, babban birnin Chadi, ta yanke wa tsohon firaminista kuma madugun adawa, Succes Masra, hukuncin ɗaurin shekaru 20 a gidan yari. Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP ya ruwaito kotun ta samu tsohon firaministan da laifin kalaman ƙiyayya, nuna wariyar ƙabilanci da kuma tayar da tarzomar da ta rikiɗe zuwa kisan kiyashi. Dan wasan Barcelona Inigo Martinez ya koma Al-Nassr MDD za ta yi zaman gaggawa kan yunƙurin ƙwace Gaza Kotun a ranar Asabar ta ce ta sami Mista Masra da laifi kan rawar da ya taka wajen tayar da rikicin ƙabilanci wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 42 a ranar 14 ga Mayu — waɗanda galibi mata da yara ne a yankin Mandakao da ke kudu maso...
A ranar Asabar kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta sanar da cewa dan wasan bayanta, Inigo Martinez zai bar kungiyar, kuma jaridun Sifaniya sun ruwaito cewa zai koma kungiyar Al-Nassr da ke gasar Saudi Pro League. Tafiyar Martinez za ta taimaka wajen rage nauyin biyan albashin ’yan wasa a Barcelona, kungiyar da a bayan nan ke fama matsalar rashin kudi. MDD za ta yi zaman gaggawa kan yunƙurin ƙwace Gaza Dubban mutane sun yi zanga-zangar goyon bayan Falasɗinu a Isra’ila da Pakistan Martinez mai shekara 34 ya buga wasa a wasanni 71 a dukkan gasanni tun bayan komawarsa kungiyar daga Athletic Bilbao a shekarar 2023, inda ya taimaka wa Barcelona ta lashe kofin La Liga a kakar bara. Kafin haka,...
Gwamnan ya kuma umurci jami’an tsaro da su rufe gidan rediyon tare da nemo bayanan mai gidan rediyon, inda ya zarge ta da haddasa tashin hankali. Sai dai a kara mai lamba FHC/L/CS/1587/2025 da aka shigar a ranar Juma’ar da ta gabata a babban kotun tarayya da ke Legas da SERAP da kuma NGE suna neman sani “ko a sashe na 22 na kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) da sashe na 2(1) (t) na dokar NBC, NBC na da hakkin kare ‘yancin Badeggi FM da gwamnan Neja ya rufe.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga...
Jami’in ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa; Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cimma babban matsayi a yakin kwanaki 12 Ali Baqiri Kani mamba a majalisar tsare-tsaren a ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cimma babban matsayi a yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa da yahudawan sahayoniyya. Baqiri ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi ta gidan talabijin a yammacin jiya Asabar cewa: Tabbas Iran ta cimma matsayi sosai a yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa, yana mai jaddada muhimmancin diflomasiyya wajen tunkarar hare-haren da ake kai wa kasar, yana mai jaddada cewa: “Dole ne Iran ta mayar da martanin wuce gona da iri...
Ɗan wasan Liverpool Mohamed Salah ya soki hukumar kwallon kafa ta Turai, UEFA, kan wallafa sakon alhinin mutuwar ɗan wasan Falasɗinawa da ya rasu ba tare da ba da cikakken bayani kan abin da ya yi sanadin rasuwarsa ba. A ranar Alhamis aka kashe Suleiman al-Obeid, wanda aka fi sani da Pelen Falasɗinawa – a hare-haren Isra’ila lokacin da yake jiran karɓan kayan tallafi a kudancin Gaza. “Ko za ku faɗa mana ta yaya ya mutu sannan a ina,” kamar yadda Salah ya wallafa a shafinsa na X ranar Asabar. Obeid wanda ɗan wasan gaba ne, ya zura kwallaye sama da 100 a tsawon rayuwarsa ta tamaula.
Adadin wadanda suka yi shahada sakamakon saukar agajin da aka kai a zirin Gaza ya kai Falasdinawa 23 tare da jikkata wasu 124 Adadin Falasdinawa da suka yi shahada sakamakon saukar da agaji ta hanyar jiragen sama tun bayan fara yakin kisan kare dangi da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kaddamar kan zirin Gaza ya karu zuwa 23, yayin da wasu 124 suka samu raunuka, kamar yadda ofishin yada labarai na gwamnati a zirin Gaza ya sanar. Ofishin ya tabbatar da cewa, a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya, Asabar, cewa: Akasarin wadannan kayan agajin da jiragen saman ke watsowa ta sama suna fadowa ne a yankunan da ‘yan mamaya suka mamaye, ko kuma a cikin unguwannin da...
“Baya ga alaƙa da Ruwa, ƙasashen da ke Afirka ta Gabas da kuma waɗanda ke a Afrika ta Tsakiya, da suke yi musharaka da irin ƙalubalensu da kuma sauran damarmakinsu, dole ne mu zage mu amfana da tattalin arzikin da ake da shin a Tekuna, musamman ta hanyar haɗa kanmu da kuma yin haɗaka, wanda idan ba a yi hakan ba, tamkar muna kawai yaudarar kawunan mu ne,” Ɗantso ya ce. A cewar Shugaban na Hukumar NPA, alƙaluman da ake da su, sune za su bamu damar, ci gaba da ɗaukar matakan da suka kamata, na wajen ci gaba da bai wa Tashoshin Jiragen Ruwa na Afrika, kulawar da ta dace. Kazalika, Shugaban ya kuma jinkinawa shugaban ƙasa Bola Tinubu,...
Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kira taron gaggawa a wannan Lahadin domin tattauna ƙudirin Isra’ila na ƙwace iko da Zirin Gaza. Wannan shirin, wanda Majalisar Tsaron Isra’ila ta amince da shi a ranar Juma’a, ya jawo suka daga ƙasashen duniya. Al-Hilal ta ɗauki Nunez daga Liverpool Sojoji sun kashe Kwamandan Boko Haram a Borno Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres ya kwatanta shirin da abin da zai ƙara dagula lamura a fadan da aka kwashe watanni 22 ana yi. Kasashen Turai da ke cikin Kwamitin Sulhun da suka hada da Denmark da Faransa da Girka da Burtaniya da Slovenia ne suka kira wannan zaman gaggawan a birnin New York na Amurka. DW ya ruwaito cewa, dukkan...

Gwamna Yusuf Ya Amince Da Korar Wasu Mataimaka Biyu Bisa Hannu Akan Belin Wani Dilan Miyagun Kwayoyi
Gwamnatin jihar Kano ta amince da korar wasu manyan mataimaka na musamman (SSAs) ba tare da bata lokaci ba, sakamakon zarge-zargen da wasu kwamitocin bincike suka yi na gudanar da bincike kan wasu laifuka. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Alhaji Umar Farouk Ibrahim ya fitar. A wani gagarumin mataki da gwamnan ya dauka, ya amince da korar Abubakar Umar Sharada, babban mataimaki na musamman kan harkokin siyasa, bayan da kwamitin bincike na musamman ya tuhume shi a matsayin wanda ya shirya belin wani mai hatsarin gaske kuma dilan kwyaan maye, Sulaiman Aminu Danwawu, wanda ya tabbatar da laifin Abubakar Sharada a cikin takaddamar belin ta hanyar kwamitin da ya gabatar a gaban...
Don haka, kwamishinan ya gode wa ƙungiyar bisa wannan ziyara tare da bayyana shirin Ma’aikatar na yin haɗin gwiwa da haɗin gwiwa ta fuskar horarwa, wayar da kan jama’a, da wayar da kan jama’a game da SGBƁ. Tun da farko, Misis Achimugu ta bayyana cewa ziyarar bayar da shawarwarin ita ce kashi na biyu na ci gaba da wayar da kan jama’a, da bayar da shawarwari, koyan fasaha, da kuma shirin tallafa wa jama’a, wanda wani ɓangare ne na dabarun yaƙi da cin zarafin mata (SGBƁ) a Jihar Kogi. Ta bayyana muhimmancin haɗa hannu da masu ruwa da tsaki, ma’aikatu, sassa, hukumomi (MDAs), ƙungiyoyi masu zaman kansu, da cibiyoyin gargajiya da na addini domin yaƙar matsalar SGBƁ, musamman a tsakanin...
Gwamnatin jihar Kwara ta gargadi manoma da mazauna yankunan da ke fama da ambaliyar ruwa da su dauki matakan kariya cikin gaggawa domin ceto jarin da suke zubawa. A wata sanarwa da kakakin ma’aikatar noma da raya karkara, Ashaolu Omotola ya fitar, ya ce. Hukumar Kula da Ruwa ta Najeriya NIHSA, ta yi hasashen yiwuwar ambaliyar ruwa a wasu sassan jihar Kwara tsakanin ranakun 7 zuwa 21 ga watan Agustan bana. A cewar hukumar ta gano al’ummomi da dama a jihar daga cikin wurare 832 a fadin kasar da ke fuskantar hadarin ambaliya a wannan lokaci. Ta ce ambaliyar ruwan da ake sa ran za ta iya tarwatsa hanyoyin sufuri tare da yin barazana ga filayen noma,...
Ya ƙara da cewa an kama aƙalla mutane uku da ake zargin suna da alaƙa da kayan a wani samame da aka kai musu. Babafemi ya ce, “Kashi na farko na kayan, wanda ya kunshi kwayoyin Tramadol 57,420 na tramadol 225mg da 57 na hodar ibilis mai nauyin kilogiram 1.60, an kama su ne a cikin wani kaya da zai je kasar Gabon a Air Cote d’Iɓoire a ranar Asabar, 19 ga watan Yuli, 2025. Wani shahararren dan kasuwan nan mai suna Benkwee Ihesi Osina, shi ne wakilin cargo, wanda aka kama. Shipment, an kama shi nan take, wani bincike ya kai ga kama wani wanda ake zargi, Uzochukwu Godspower Chukwurah, a ranar Lahadi, 20 ga watan Yuli. “An gano...
Dubban mutane ne suka fito kan tituna a birnin Tel Aviv na Isra’ila ranar Asabar, domin yin kira da a kawo ƙarshen yaƙin Gaza, kwana guda bayan da gwamnatin Isra’ila ta lashi takobin faɗaɗa rikicin tare da ƙwace birnin Gaza. Masu zanga-zangar da ke riƙe da hotunan waɗanda har yanzu ake garkuwa da su a yankin Falasdinawa sun yi kira ga gwamnati da ta tabbatar da sakin su ’yan uwansu. Al-Hilal ta ɗauki Nunez daga Liverpool ASUU na shirin sake tsunduma yajin aiki ’Yan jaridar AFP a wajen gangamin sun ƙiyasta adadin waɗanda suka halarci taron a matsayin dubbai, yayin da wata ƙungiya da ke wakiltar iyalan wadanda aka yi garkuwa da su ta ce mutane kusan 100,000 ne suka...
Garima wanda har ila yau shi ne, and Jakadan Gwandu ya yi nuni da cewa, cibiyoyin na CNG da gwamnatin taraya ta samar a jihohin Kano da Kaduna, za su taimaka wajen samar da Iskar Gas ɗin a Arewa ta tsakiya da kuma Arewa ta Gabas. Kazalika ya ce, samar da cibiyar a jihar Sokoto wadda take kusa da Jamhuriyyar Nijar, hakan zai ƙara bunƙasa tattalin arzikin jihar Garima ya sanar da cewa, Iskar Gas ɗin ta CNG tsafatattaciya ce kuma bata da wani tsada, inda kuma ta rage gurɓatar muhalli. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin...
Wani lokacin, yanayin shekaru da Jinsin Jini ne ke fayyace irin girma ko ƙantantar Ƙwan da Kajin za su yi. 2- Wajen Kwana: Kajin na buƙatar a tabbatar da ana samar musu da wadataccen ruwan sha a ɗakunan kwanansu da kuma ba su kariya daga kamuwa da cutuka da rage musu wahala da cunkoso da kuma zafi, wanda hakan na iya shafar Ƙwan da za su yi kai tsaye. 3- Abinci Mai Gina Jiki: Ciyar da su abinci mai gina jiki, wanda ke ɗauke da sinadaran ‘protein, amino acids’, waɗanda za su sanya su yi nauyi tare kuma da buƙatar a riƙa yi musu allurar ƙara musu lafiya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
Jaridar Tehran Times, ta nakalto cewa, Iran da Amurka a shirye suke su fara wata sabuwar tattaunawa. Majiyoyin sun ce tattaunawar za ta kasance ba kai tsaye ba, sanann kuma ana sa ran cewa kasar Norway ce za ta kasance mai shiga tsakanin bangarorin biyu. Jaridar ta kasar Iran ta yi nuni da cewa “Tehran ta dage kan cewa batun biyan diyya a kan barnar da aka yi mata a yakin baya-bayan nan ya zama wani muhimmin bangare na duk wata tattaunawa a nan gaba.” A ranar Alhamis kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya musanta duk wata Magana kan wani takamaiman lokaci ko wurin da za a yi shawarwari da Washington, yana mai jaddada cewa “dukkan jita-jita game da hakan...
Dubban mazauna birnin Tel Aviv ne suka taru a tsakiyar birnin a daren jiya Asabar, domin neman kawo karshen yakin Gaza, kwana guda bayan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta sanar da shirin kara kai hare-hare da kuma mamaye birnin Gaza. Masu zanga-zangar dai na dauke da allula da kuma hotunan wadanda ake tsare da su a Gaza, suna masu kira ga hukumomi da su ba da fifikon sakin su kan fadada ayyukan soji. An kuma bayyana cewa hatta a cikin manyan jami’an soji na Isra’ila, babban hafsan hafsan hafsoshin sojin Isra’ila Eyal Zamir ya yi yunkurin shawo kan majalisar ministoci kan cewa mamaye Gaza ba shi ne zabin da ya dace ba, da kuma tattauna babbar illar da hakan...
Ali Akbar Velayati mashawarcin jagoran juyin juya halin Musulunci da Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan harkokin kasa da kasa ya tabbatar da cewa “Jamhuriyar Musulunci tana adawa da shirin kwance damara na kungiyar Hizbullah” yana mai jaddada cewa Iran a ko da yaushe tana goyon bayan al’ummar kasar Labanon da kuma gwagwarmayarsu. Da yake magana da kamfanin dillancin labarai na Tasnim na Iran a ranar Asabar, Velayati ya ce bijiro da batun kwance damarar Hizbullah ba sabon abu ba ne a Lebanon. “Kamar yadda wannan yunƙurin ya gaza a baya, wannan karon ma ba za iyi nasara ba, kuma ‘yan gwagwarmaya zasu ci gaba da yin tsayin daka a kan manufofinsu da kuma dakile wannan makirci,” in ji shi. Ya...
‘Yan sandan Birtaniya a birnin Landan sun sanar da kame mutane 365 a wata zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinu, wadda kungiyar Palestine Action da gwamnatin Birtaniya ta haramta a watan jiya ta shirya. A cikin jerin rubuce-rubucen da aka yi a Shafin X, ‘yan sanda sun ce “sun dauki tsauraran matakai a kan wannan laari, tare da yin barazanar kame duk wanda ya nuna goyon baya ga Action Palestine. Masu zanga-zangar dai na dauke da alamomin da aka rubuta “Ku kawo karshen kisan kare dangi, ku goyi bayan matakin Falasdinu,” tare da rera taken “Ku kun ji kunya”. Kungiyar kare hakkibil adama ta “Lift the Ban”, ta bayar da rahoton cewa ‘yan sandan Biritaniya sun gaba da kame mutane kan...
Hukumomin tsaro a kasar Venezuela sun kama wasu tarin bama-bamai a gabashin birnin Maturin na jihar Monagas, a wani abin da jami’ai suka bayyana a matsayin yunkurin da wasu bangarori masu tsatsauran ra’ayi suka yi na kai hare-haren ta’addanci da nufin kawo cikas ga gwamnatin shugaba Nicolas Maduro. Ministan harkokin cikin gida, Diosdado Cabello, ya sanar a jiya Asabar cewa, jami’an tsaro, bayan gudanar da ayyukan leken asiri, sun gano wasu kayyayakin fashewa da abubuwan harhada bama-bamai da aka boye a wasu shaguna biyu.Kayan sun dai sun hada da akwatuna 1,137 da ke dauke da wasu nauyin bama-bamai da ba a taba ganin irinsu a kasar ba, da rokoki 35, da igiyoyin tayar ta bama-bamai da ababen fashewa, na’urorin kashe...
Kyari ya ce, a yanzu ana noma Waken Soya da ya kai kimanin tan miliyan 1.35, wanda kuma buƙatar da ake da shi a ƙasar ya wuce tan miliyan 2.7. Ya sanar da cewa, wanan tsari zai kuma amfani tattalin arziƙin ƙasar da ƙara samar da ayyuakn yi da kuma ƙara haɓaka samar da wadataccen abinci a ƙasar. Shi kuwa a nasa jawabin a wajen ƙaddamarwar, Gwamnan Jihar Biniwai, Hyacinth Iormem Alia, ya jaddada muhimmancin da za a amfana da shi a tsarin. “Dabarun faɗaɗa noman Waken Soya na ƙasa, mataki ne da ya dace wajen yin haɗaka, domin samar da kuɗaɗen shiga ga ƙasar a duk shekara da suka kai kimanin Naira tiriliyan 3.9 da ƙara ƙirƙiro da ayyukan...
Yayin ziyararsa a kasar Indiya kwanan nan, shugaban kasar Philippines ya bayyana cewa, idan Sin da Amurka suka yi taho-mu-gama kan batun yankin Taiwan, Philippines ba za ta iya killace kanta daga ciki ba. Irin wannan furucin nasa yana da ban mamaki, wanda ya saba da alkawarin da Philippines ta yi na tsayawa ga manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, kana, zai kara illata dangantakarta da kasar Sin, da zaman lafiya da tsaro a wannan shiyya. Rura wutar rikici kan yankin Taiwan, yunkuri ne da Philippines ta yi na dogaro kan Amurka tare da ba ta hadin-kai, don hana ci gaban kasar Sin. Amma batun da ya shafi yankin Taiwan, batu ne na cikin gidan kasar Sin, kuma...
Mambobin haɗakar jam’iyar sun ƙunshi tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi da tsohon gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal da tsohon shugaban jam’iyyar APC, John Oyegun, da sauran manyan mutane da dama. A cikin wannan tsarin, haɗakar jam’iyyar ta naɗa tsohon shugaban majalisar dattawa, Daɓid Mark da tsohon ministan cikin gida, Rauf Aregbesola, a matsayin shugaban da sakatare na riƙon ƙwarya. Tun daga wannan lokaci, jam’iyyar tana ta karɓar masu sauya sheƙa daga sauran jam’iyyun adawa da kuma gudanar da tarurruka domin ƙara masun mambobi a faɗin ƙasar nan kafin zaɓen 2027. El-Rufai, wanda ya kasance ɗaya daga cikin asalin mambobin APC, ya...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta raba katin duba sakamakon jarabawa ga ɗalibai sama da dubu shida da ɗari biyar da suka kammala makarantun sakandaren Larabci da suka yi nasarar rubuta jarabawar NBAIS ta shekarar 2025 a jihar. Shugaban Hukumar Ilimin Addinin Musulunci ta Jihar, Dakta Mubarak Abdulwahab Hassan ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Dutse, babban birnin jihar. A cewarsa, dukkan ɗaliban aji na ƙarshe na makarantun sakandaren Larabci na gwamnati da suka amfana da wannan tallafi sun kammala rubuta jarabawar NBAIS makon da ya gabata, kuma suna jiran sakamakon. Ya ce wannan tallafi na daga cikin ɗawainiyar da gwamnatin Gwamna Umar Namadi ke yi wajen taimaka wa ɗaliban aji na ƙarshe na sakandaren Larabci domin...

Jakadan Kasar Sin A Najeriya Ya Gana Da Ministar Kula Da Masana’antu Da Cinikayya Da Zuba Jari Ta Kasar
Jakadan kasar Sin da ke Najeriya, Yu Dunhai, ya gana a kwanan nan da ministar kula da harkokin masana’antu, da cinikayya, da zuba jari ta tarayyar Najeriya, madam Jumoke Oduwole. Jakada Yu ya bayyana cewa, tun bayan da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci kasar Sin tare da halartar taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC a watan Satumban bara, zuwa yanzu, Sin da Najeriya na kara samun fahimtar juna ta fuskar siyasa, tare da fadada hadin-gwiwa a bangarorin da suka shafi masana’antu, cinikayya da zuba jari, har ma kwalliya ta biya kudin sabulu. Ya ce kasar Sin tana fatan ita da Najeriya za su rattaba hannu kan yarjejeniyar raya dangantakar abokantaka a...
Dakarun Sojin Najeriya sun kashe wani babban Kwamandan Boko Haram, mai suna Abu Nasr, wanda ya jagoranci kai hari garin Rann, da ke Ƙaramar Hukumar Kala Balge, a Jihar Borno. A makon da ya gabata, dakarun rundunar Operation Hadin Kai, sun daƙile harin da Boko Haram suka kai garin Rann. Jarumar Kannywood Rahama Sadau ta yi aure Za a biya ma’aikata 445 garatutin sama da biliyan ɗaya a Kebbi Sun kashe ’yan ta’adda da dama, duk da cewa sojoji biyu sun rasa rayukansu sakamakon harba roka da ‘yan ta’addan suka yi. Rann na da iyaka da ƙasar Kamaru, kuma daga Maiduguri yana da nisa kusan kilomita 196. Bayanan jami’an tsaro sun tabbatar cewa Abu Nasr, wanda ya jagoranci tawagarsa zuwa...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya yabawa yan jarida musamman a khidimar da suka gabatar a yakin kwanaki 12. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a yau Asabar a lokacinda ya kai ziyarar ganin ido a cibiyar hukumar gidajen radiyo da talabijin na JMI a nan birnin Tehran. Labarin ya kara da cewa shugaban yay aba da ayyukan da yan jarida a kasar suka yi a lokacin yakin kwanaki 12, na samar da hadin kai tsakanin iraniyawa duk tare da banbanci-bambance da ke tsakaninsu da kuma fadin labaran gaskiyan abinda yake faruwa ga mutanen kasar da kuma duniya gaba daya dangane da yakin. Shugaban yay aba da yadda suka nuna zanga-zangar hadin kai...
Yansanda a kasar Burtaniya ta kama mutane fiye da 200 wadanda suka fito zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a birnin London. Tashar talabijinn ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kafafen yada labarai a birnin London na cewa mutane kimani 600-700 ne suka fito suka kuma tsaya a wani wuri kusa da majalisar dokokin kasar wanda ake kira ‘ in Westminster’s Parliament Square ‘ inda suke dauke da kwalaye da rubuton ina son mutuncin ma’aikatar sharia, bana son zalunci. Kafin haka dai gwamnatinn kasar ta haramta zanga-zangar da aka saba gudanarwa a birnin na Lodun a dukkan karshen mako, wato ranar asabar na goyon bayan Falasdinawa da kuma yin allawadai da kasashen yamma musamman gwamnatin kasar Burtaniya wacce daga daga cikin...