Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban Hukumar Kula Da Wutar Lantarki Ta Kasa
Published: 7th, August 2025 GMT
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Injiniya Abdullahi Garba Ramat a matsayin sabon Shugaba kuma Babban Jami’in Gudanarwa (CEO) na Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC). Haka kuma, ya naɗa Abubakar Yusuf a matsayin Kwamishinan Harkokin Abokan Hulɗa, da Dr. Fouad Olayinka Animashun a matsayin Kwamishinan Kudi da Harkokin Gudanarwa.
A cikin wata sanarwa da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara ta Musamman kan Harkokin Watsa Labarai da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya sanya wa hannu, shugaban ƙasar ya bukaci waɗanda aka naɗa su yi amfani da ƙwarewarsu wajen tabbatar da burin gwamnatinsa a fannin wutar lantarki.
Onanuga ya bayyana cewa waɗannan nade-naden suna jiran tantancewar Majalisar Dattawa. Sai dai, domin kauce wa gibin shugabanci a hukumar, Shugaba Tinubu ya umarci Injiniya Ramat da ya fara aiki a matsayin mukaddashin shugaba kafin tantancewarsa, bisa tanadin doka.
Injiniya Ramat, mai shekaru 39, kwararre ne a fannin injiniyan lantarki, yana kuma da ƙwarewa a harkokin gudanarwa, yana da digirin digirgir (PhD) a fannin Gudanarwa ta Dabaru (Strategic Management).
Daga Bello Wakili
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Neja Ta Raba Motoci Ga Ma’aikata Da Hukumomi
Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya bada motocin aiki ga shugabannin hukumomi, jami’an tsaro da wasu manyan jami’an gwamnati a jihar.
An gudanar da bikin mika motocin ne a Fadar Gwamnati da ke Minna.
Gwamna Bago ya bayyana cewa wannan mataki na bayar da motocin aiki na da nufin tallafa wa harkokin sufuri da kara inganta gudanar da ayyuka yadda ya kamata.
Ya yabawa kwazon wadanda suka amfana da motocin a aikin gwamnati tare da bukatar su yi amfani da su bisa gaskiya da amanar da aka dora musu domin cimma nasarorin da ake bukata.
Cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin akwai Shugabannin Hukumar Kula da Ma’aikatan Kananan Hukumomi, Hukumar Majalisar Dokoki, Hukumar Ma’aikata da Hukumar Kula da Binciken Kudade.
Sauran sun hada da Darakta Janar na Gyaran Makarantu, Babban Mai Binciken Asusun Kananan Hukumomi da Ma’aikacin Kudi na Fadar Gwamnati.
Gwamnan ya kuma mika karin motocin Hilux guda 20 ga hukumomin tsaro daban-daban domin karfafa ayyukansu a fadin jihar.
Aliyu Lawal.