Cinikayyar Kayayyaki a Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.5 Cikin 100 Cikin Watanni 7 Na Farkon Shekarar Nan
Published: 8th, August 2025 GMT
Alkaluman kididdiga na hukumar kwastam ta kasar Sin sun nuna yadda cikin watanni 7 na farkon shekarar nan ta 2025, jimillar darajar cinikayyar kayayyaki ta kasar Sin ta kai kudin kasar yuan tiriliyan 25.7, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 3.5, wanda hakan ya nuna karuwar kashi 3.5 cikin 100 idan aka kwatanta da makamancin lokaci na shekarar bara.
A watan Yuli, jimillar darajar cinikayyar kayayyaki ta Sin ta kai yuan tiriliyan 3.91 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 544, adadin da ya karu da kashi 6.7 cikin 100. Daga wannan adadi, mizanin fitar da kayayyaki ya kai yuan tiriliyan 2.31, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 321, inda ya karu da kashi 8 cikin 100. Sai kuma mizanin shigo da kayayyaki da ya kai darajar yuan tiriliyan 1.6, kwatankwacin dala biliyan 222, wanda shi ma ya karu da kashi 4.8 cikin 100, wanda hakan ke nuna ci gaba da karuwarsa a tsawon watanni biyu. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: kwatankwacin dalar Amurka kai yuan tiriliyan ya karu da kashi da kayayyaki
এছাড়াও পড়ুন:
Jihar Kogi Na Cikin Fargaba Yayin Da Kogin Neja Da Benuwe Suka Tumfatsa
Hassan Jibril wanda ke zaune a yankin Pata da ke fama da ambaliyar ruwa a duk shekara, ya ce a yanzu haka suna cikin fargaba, duk da cewa a ko wace shekara sun saba yin gudun hijira tun bayan afkuwar ambaliyar ruwa ta 2012 da ta mamaye wasu al’ummomi a wasu kananan hukumomin jihar.
Ƙananan hukumomin dake cikin fargaba sun haɗa da Kogi, Ajaokuta, Ofu, Ibaji, Adavi, Bassa da Omala.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp