Aminiya:
2025-09-24@19:51:31 GMT

Al-Hilal ta ɗauki Nunez daga Liverpool

Published: 10th, August 2025 GMT

Kungiyar Al Hilal ta Saudiyya ta dauki dan wasan gaban Liverpool, Darwin Nunez, kamar yadda kungiyoyin biyu suka tabbatar ranar Asabar.

Masu ruwa da tsaki a harkar tamaula na ganin wannan matakin za bai wa zakarun Premier League damar sake mika tayin neman dan wasan gaban Newcastle, Alexander Isak.

ASUU na shirin sake tsunduma yajin aiki Sojoji sun kashe Kwamandan Boko Haram a Borno

Shekaru uku da suka gabata ne Nunez ya koma Liverpool daga Benfica kan farashin Yuro miliyan 75 ($87m, £65m), sai dai bai iya cika tsammanin da aka yi wa darajar da aka saye shi ba.

Nunez wanda dan kasar Uruguay ne ya zura kwallaye 40 a wasanni 143 da ya haska a Liverpool, amma daga baya ya daina samun damar buga wasanni sosai a karkashin jagorancin Jurgen Klopp da Arne Slot.

Kafafen yada labarai na Birtaniya sun ruwaito cewa a karon farko Al-Hilal za ta biya Yuro miliyan 53 na farashin dan wasan mai shekara 26.

Bayanai sun ce ko da ba a cefanar da dan wasan ba, ba zai samu damar buga wasanni a wannan kakar ba, la’akari da cewa Liverpool ta dauki Hugo Ekitike da Florian Wirtz wanda ta kashe Yuro miliyan 300 ciki har da ’yan baya da ta saya da suka hada da Milos Kerkez da Jeremie Frimpong.

Sayar da Nunez ya kara yawan kudaden da Liverpool ta samu wajen cefanar da ’yan wasa a wannan kakar zuwa kusan Yuro ,iliyan 200 bayan tafiyar Luis Diaz, Jarell Quansah, Caoimhin Kelleher, Trent Alexander-Arnold da Tyler Morton.

Nunez shi ne sabon tauraron da ya koma Al-Hilal — kungiyar da ta bai wa Manchester City mamakin doke ta wasan kwata-final na gasar Club World Cup da aka gudanar a watan jiya.

Al-Hilal, karkashin jagorancin tsohon kocin Inter Milan Simone Inzaghi, na da ’yan wasan Portugal Ruben Neves da Joao Cancelo, kyaftin din Senegal Kalidou Koulibaly, da kuma tsohon dan wasan gaba na Fulham Aleksandar Mitrovic.

AFP

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

NAJERIYA A YAU: Yadda Wata Bakuwar Cuta Take Cin Naman Jikin Mutanen Malabu

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

Wata cuta mai cin naman jikin dan’Adam ta yi sandin mutuwar mutum takwas yayin da wasu fiye da 60 suke kwance a asibiti a garin Malabu dake Karamar Hukumar Fufure ta Jihar Adamawa.

 

Wannan lamari dai ya jefa fargaba a zukatan mazauna yankin.

NAJERIYA A YAU: Ayyukan Da Fasahar AI Za Ta Raba Mutane Da Su Nan Ba Da Jimawa Ba DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi bincike a kan yadda wannan cuta take yaduwa da matakan da ya kamata a dauka don kauce wa kamuwa da ita.

Domin sauke shirin, latsa nan

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An sake raba Naira biliyan 5 haƙƙoƙin ’yan fansho a Kano
  • An Kama Tsohon Ɗan Wasan Super Eagles, Victor Ezeji, Kan Zargin Aikata Zambar ₦39.8m
  • An yi wa sojoji ɗaurin rai da rai kan sayar wa ’yan ta’adda makamai a Borno
  • ‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Filato
  • Burkina Faso, Mali da Nijar sun fice daga Kotun ICC
  • Katsina Za Ta Ɗauki Nauyin Karatun Mahaddata Alƙur’ani – Gwamna Radda
  • Jadawalin ‘Yan Wasa 30 Na Farko A Kyautar Ballon D’or Ta Bana
  • NAJERIYA A YAU: Yadda Wata Bakuwar Cuta Take Cin Naman Jikin Mutanen Malabu
  • APC Da PDP Na Zargin Juna Kan Amfani Da Addini Wajen Neman Nasara A 2027
  • Mahara sun kashe ’yan sanda a shingen bincike a Kogi