’Yan bindiga sun kashe gomman mutane a ƙauyukan Sakkwato
Published: 10th, August 2025 GMT
An sake shiga tashin hankali a Jihar Sakkwato bayan wani sabon mummunan hari da ’yan bindiga suka kai a wasu kauyuka, lamarin da ke ƙara tsananta matsalar tsaro a faɗin jihar.
Rahotanni sun nuna cewa duk shekara musamman a lokacin damina, ’yan bindiga sukan ƙara ƙaimi wajen kai hare-haren da ke tarwatsa jama’a a garuruwansu da hana manoma zuwa gona ko kuma ƙaƙaba musu harajin zuwa gonakin.
Aminiya ta ruwaito cewa, a bana ma, maharan sun ci gaba da addabar mazauna ƙananan hukumomi 20 daga cikin 23 na Jihar Sakkwato.
Majiyoyi sun tabbatar cewa a harin baya-bayan nan, ’yan ta’addan sun hallaka mutane da dama sannan sun yi garkuwa da wasu.
Shafin Bakatsine da ke bibiyar rahotannin da suka shafi sha’anin tsaro, a wannan Lahadin ya wallafa a manhajar X cewa, an kai hari a wani masallaci a garin Bushe da ke Karamar Hukumar Sabon Birni, inda aka sace aƙalla mutum 10 ciki har da limamin masallacin.
Rundunar ’yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa ana ci gaba da ƙoƙarin ceto waɗanda aka sace.
Haka kuma, rahotanni sun ce maharan sun sake kai wani hari a lokacin sallar Isha a ƙauyen Marnona na Karamar Hukumar Wurno, a daren Asabar, inda suka kashe masallata da dama sannan suka yi awon gaba da wasu.
Sanata Ibrahim Lamido, mai wakiltar Sakkwato ta Gabas a Majalisar Dattawa, ya yi Allah wadai da hare-haren da suka auku a Bushe da Marnona, inda ya buƙaci hukumomi su ƙara ƙaimi wajen kare rayuka da dukiyar al’umma.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Jihar Sakkwato
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan sanda sun ceto mutum 10 daga hannun ’yan bindiga a Kaduna
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta samu nasarar ceto mutum 10 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su tsawon watanni huɗu da suka gabata a Ƙaramar Hukumar Kagarko.
A cikin sanarwar da kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan, ya fitar, ya bayyana cewa daga cikin waɗanda aka ceto har da yara masu shekaru ɗaya, uku da kuma 13.
Tinubu ya yi wa Maryam Sanda afuwa Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaroDSP Mansir, ya ce ’yan bindigar sun kai farmaki ƙauyen Kushe Makaranta, inda suka sace mutanen daga gidajensu sannan suka kai su dajin da ke kusa da Rijana.
Rundunar, ta ce aikin ceto mutanen ya samu ne ta haɗin gwiwar ’yan sanda, jami’an DSS, da kuma sojoji.
Wani mazaunin yankin ya shaida cewa suna matuƙar farin ciki da wannan nasara, musamman ganin cewa mutanen sun kwashe watanni a hannun ’yan bindiga cikin tsananin wahala.
Hukumomin tsaro sun ce ana ci gaba da bincike domin kamo sauran ‘yan bindigar da suka tsere, tare da inganta matakan tsaro a yankin don kauce wa sake faruwar irin wannan lamarin.
“Za mu ci gaba da aiki tare da sauran hukumomi don tabbatar da cewa babu wata ƙungiyar ‘yan ta’adda da za ta samu mafaka a Kaduna,” in ji DSP Mansir Hassan.