Ƴan Bindiga Sun Sace Fasinjoji 9 A Kogi
Published: 9th, August 2025 GMT
A ranar Juma’a da yamma, wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun tare motar haya a mararrabar Ogbabo, kan titin Itobe-Anyigba a jihar Kogi, inda suka yi awon gaba da fasinjoji 9. Direban motar da wasu fasinjoji 6 kuwa sun tsere ba tare da an sace su ba.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:20 na yamma a yankin ƙaramar hukumar Ofu, lokacin da ƴan bindigar suka fito daga daji suka tare titin.
Nisan wurin da aka sace fasinjojin ya yi kusan mita 300 kacal daga shingen Sojoji na irin Ogbabo-Ochadamu. Jami’an tsaro sun isa wurin cikin gaggawa, inda suka tarar da motar haya mai lambar ENZ-55 XS da wata Toyota Carina ‘E’ a ajiye. An fara aikin ceto tare da haɗin gwuiwar ƴansanda, da Sojoji, da ƴan sa-kai da mafarauta domin gano masu laifin da kuma kuɓutar da waɗanda aka sace.
Kakakin rundunar ƴansanda jihar, SP Williams Ovye Aya, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa ana aiki kafaɗa da kafaɗa da sauran jami’an tsaro don ceto mutanen da aka sace tare da kama waɗanda suka aikata laifin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Bayan Sulhu Da Ƴan Bindiga, An Saki Mutane 70 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina
Mutune 70 da aka yi garkuwa da su sun samu ƴanci a Jihar Katsina, bayan yarjejeniyar sulhu da aka ƙulla da fitaccen shugaban ƴan bindiga, Isiya Kwashen Garwa. A wani faifan bidiyo da ya bayyana, Garwa ya saki mutane 40 a ƙaramar hukumar Faskari, kwanaki biyu bayan ya fara sakin wasu 30, wanda hakan ya kai adadin zuwa 70 gaba ɗaya.
Rahotanni daga mazauna yankin sun ce sakin na baya-bayan nan ya biyo bayan tattaunawa tsakanin shugabannin al’umma da sansanin Garwa, a wani mataki da ake ganin zai rage tashin hankali da hare-hare a yankin. Duk da haka, Garwa ya nuna rashin jin daɗi kan abin da ya kira sumamen Sojoji a unguwar Ruwan Godiya a lokacin Sallar Juma’a, inda ya yi zargin cewa wasu Hausawa da Fulani sun samu raunuka. Ya gargaɗi cewa irin waɗannan hare-hare na iya rusa sulhun da aka ƙulla.
Abubuwan Da Ba A Faɗa Ba Game Sulhu Da Ƴan Bindiga A Katsina An Cafke Wani Magidanci Da Lafin Sojan Gona A KatsinaHukumomin jihar ba su fitar da wata sanarwa ba kan sumamen da ake zargin ba, sai dai majiyoyin tsaro sun ce an kai hare-haren ne kan maboyar ƴan ta’adda tare da nufin kare rayukan jama’a. Mutanen da aka sako, galibinsu manoma ne da aka sace daga ƙauyukan karkara a Faskari, suna cikin kulawar likitoci da kuma binciken tsaro kafin a mayar da su wurin iyalansu.
Gwamnatin jihar ta ce tattaunawa tana daga cikin dabarun tsaro da ake amfani da su, amma ta jaddada cewa dole ne ƴan bindiga su miƙa makamansu gaba ɗaya tare da fuskantar hukunci kan laifuffukan da suka aikata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp